ABIN DA KE B'OYE page 27-28

2.3K 175 0
                                    

💧💧 *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      💧

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_

        *_NA_*
  *_FEEDOHM💞_*
&
*_K.A.S Precious HAJJA CE*👈

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
*Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyar mu*

        Page *27-28*

   *M*ikewa k'arama tayi tabar musu d'akin ganin sai faman uban kuka suke yi, gurin mai unguwa ta koma ta tarar baya rumfar shi sannan ta koma gindin bishiyar kuka ta zauna sai dariya take tana faman surutu, duk wanda ya ganta sai ya tabbatar da cewar ta samu ta6in hankali ta yadda take kwasar dariya ba kakautawa....,

"Ard'o wallahi k'arama ba mutum bace dan mun tabbatar da hakan yau d'innan." Cewar laminde da taga shigowar Ard'o yayi saurin kallonta da mamaki yana kokarin ajiye sandar korar awakin shi yace.

"Laminde ban shaida zancen kiba, hito kiyi min hila-hila." Cewar Ard'o yana kallon rumfar su Umma hafsatu, laminde tace, "kur'anin Allah bari jummai tazo kaji karin bayani."

K'arama ce ta biyo Tanimu yana rarrafe yana dariya har ya karasa kusa da Ard'o cikin 6acin rai ya kalli k'arama tare da gallara mata harara yace, "dan kaniyar ki ban ce kar in kuma ganin ki da yarana ba? Ja'ira kawai fitinanniya marar tushe."

K'arama ta tura mai baki tana mai kunkuni har jummai ta fito daga makewayi (toilet) duk ruwa jikinta daga gani tana nufin wanka tayi amma duk wani gurin bema san an hallici ruwa ba ta karasa inda suke dama tun a ciki take jiyosu gulma na cinta ta fito tana cewa "Ard'o babu shakka yau mun tabbatar da cewar k'arama mayya ce dan munyi mata hayak'i karshe ma caraffke mukaga tanayi a ciki.."

Zaro idanu yayi cikin tsananin mamaki da tsoro yace "ta6 d'i jam *!* abinda ba zai yiwu ba kenan shine take son ta fara takan yaro na kenan...?"

"Ke Hafsatuwalle... *!* zo nan." Ard'o ya fad'a cikin d'aga murya, Umma ta fito bayan ta goge hawanta. "Ke kam wallahi hafsatu kin janyo mana bala'i, ko waye uban k'arama ya had'a jinsi da mayyu dan haka Mu bazamu yadda ba mun baki nan da sati biyu idan baki binciko mana uban k'arama ba wallahin Allah zaki gane kuran ki."

Kuka ta sanyi a gurin zuciyar ta na zafi k'iris ya rage ta kone kurmus a yadda take yi mata zafi da rad'ad'i. "Umma tashi Mu koma d'aki dan Allah.." Cewar lauratu da itama take sharar hawaye tamkar ba amarya ba haka suka koma cikin rumfar su.

Kusan awar su biyu sannan suka share hawayen su Umma ta kalli kud'in hannun lauratu tace "Laure wannan kuma daga ina?" Ta fad'a tana tsinkar zogalen da zata dafa tabawa lauratu a matsayinta na amarya me jiran tarewa anjima a d'akin ta.

"Umma wata fillo ce ta bani, ban santa ba kuma har tambayar ta nayi amma ta wuce bata ce min komai ba." Kar6ar kullin Umma tayi tana bud'ewa taga kud'i masu yawa wajan 22k duk an cure su guri guda. "Lauratu kud'ine... *!*" Umma ta fad'a hannuta na rawa idanunta a waje tana kallon lauratu, "ke nan kyauta ta bani? Amma ban santa ba hasalima ban ta6a ganin gilminta a yankin Mu ba."

K'arama ta shigo tana rik'e da d'ankwalinta a hannu ta kallesu duk sunyi zugum abin tausayi, karasawa tayi ta zauna ta kalli Umma tare da wangale bakin ta tace "Umma fillo ce ta bayar a siyawa ya laulatu (lauratu) kwanika shabida (sabida) su jummai kalltuyi (karsuyi) mata gori..."

"Naji k'arama amma waya gaya miki...?" Umma ta tambayeta k'arama tace "fillo ce Umma." Nan da nan suka yi murna tamkar su zuba ruwa su sha. Nan da nan kuwa Umma ta mik'e ba wanda ya sani rabar gidan harta je ta dawo babu wanda ya lura.

"Inno a fito da amarya Sallau ya gama komai." Cewar matan gidan wad'anda suka fito kwansu da kwarkwatar su suna jiran a fito da lauratu aga kwa-kwaf.

Inno dake cikin rumfarta tana ji tayi shiru dan ita kanta kunya take ji, ya zata fita guri ace anyiwa jikarta aure ba ko cukali, gara tayi zaman ta dan baxata fita ba suje can suyi tayi babu abin da ya shalleta. Mutanan gidan kuwa sai munafirci suke suna kus-kus, cikin d'aki kuwa Umma ce ke yiwa lauratu nasiha sannan kwanikan da ta kar6o gidan jauro guda biyar ta ajiye su guri guda sai guru daya siyar mata 5k shima duk yaci duniyar shi sabida kayan matar shine da ta rasu kuma dama ba a kauyan take ba irin filanin nan ne masu tafiye-tafiye shi yasa shi kuma yake siyar da kayan d'akin nata.

"Ahayyeeee ayyrrrrrrrri.... *!*" matan gidan suka d'auki shewa gaba d'ayan su harda mazajen su ganin Umma ta fito da lauratu cikin lullu6inta, a haka ita da k'arama suka shiga d'akin da yake a matsayin na lauratu Umma ta zaunar da ita a wajan da taga an ajiye tabarma sannan ta koma rumfarta ta d'akko garun da langunan ta kuma komawa inda lauratu take, ganin ta shigar da kaya yasa mutanen gidan bin ta suna mamaki har ta shimfid'a mata garun tare da ajiye mata sauran kwanukan ta ra6a mutanan ta wuce tana sharar hawaye.

"Ahayye nanayeee Tambai ku ganemin a ina suka samu wanga kaya..?" Jummai ta fad'a tana rik'e da ha6a cikin tsananin mamaki, maganganun sune yasa inno fitowa itama ta leka nan taga lauratu zauna gefe kuma langunan tane inno tayi d'akin Umma da sauri cikin tashin hankali.

Karo na farko kenan da inno ta ta6a shiga cikin d'akin Umma, karasawa tayi tana tambayar ta "Hafsatuwalle ince dai na sahun 6arawo kuka fara ba..? Ina kunka samu wanan kaya haka nayan baku ajeba bare ku bayar da ajiya." Umma ta kalli inno tana mamakin yadda mahaifiyar ta tak'i ta cikin sanyin jiki tace "inno daga Allah ne, Allah ne ya bamu."

"Karya kike Hafsatu ai komai akwai sila ki sanar min kamin ranki ya kuma 6aci." Ta fad'a cikin d'aga murya, shigowar k'arama ne yasa inno juyawa tana kallonta k'arama tace "Inno gashiya (gaskiya) Umma na ta gaya miki domin fillo ce ta bawa ya laulatu tashi Umma na ta shiyo mata kayan..."

Tunda k'arama tayi magana inno taji ta kasa musawa gashi ranta na son furta abu amma bakinta ya gaza fad'a a haka tabar d'akin tana mamakin alamarin. "Ard'o da laminde sune suka 6oye tukunyan baba shallau.." Suka jiyo muryar k'arama na fad'a a tsakar gida, da gudu laminde ta bita tana zagi wai tayi mata sharri kumma haka ne sun 6oye dan azo ana cigiya ace Umma ce ta d'auke.

Ba jimawa bayan kowa ya gama gulmar shi sallau ya shiga ciki murna tamkar an bashi sarautar garin, koda ya shiga d'akin dashare baki yayi yana murna, shi duk be damu da komai ba illah kawai ya yanshi da lauratu dan ba karamin sonta yake yi ba daga nan kuma......

*{{ }}      {{ }}*

     *"M*ai-tafasa wallahi idan baki rabu dani ba zan bar  miki gidan, haba mata sai jarabar tsiya shi yasa bana son zuwa gidan nan sabida masifarki." Cewar mai unguwa cikin 6acin rai, ga bak'in cikin zubewar  kud'in shi gashi ita kuma ta sashi a gaba tana sakar mai magana.

"Yoo ni ina ruwana cewa nayi ka dinga fita da kud'i ko ina? Sabida baka yadda da kowa ba toh kur'anin Allah sai ka biyani kud'ina ahe..." Mai-tafasa ta fad'a tana kokarin shiga d'akin da lado yake ciki a kwance gwanin ban tausayi duk yayi kashi d'akin sai d'oyi yake yi tamkar bayin da ba'a wankewa.

Ko takan kashin bata yi ba nan ta ajiye mai farau-farau d'in data yi tasa kai ta fita, tana fita k'arama ta shiga ta d'ayar kofar ita ce ta gyara mai jikin shi sannan ta bashi farau-farau din tare da bashi labarin auran lauratu har hawaye yayi yana ta faman jin-jina kanshi abin tausayi.

Ta dad'e a gurin shi sannan tafi gida lokacin lauratu na d'akinta har lokacin bata fito ba sabida tsananin kunya da take ki, sallau ne keyin komai hakan ya Kara tabbatarwa da mutanan gidan komai ya wakana....







*FEEDOHM*💞
&
*HAJJA CE*👈

ABINDA KE B'OYEWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu