DUNIYA JUYIN MASA

1.5K 94 2
                                    



Labari da Rubutawa
             Basira Sabo Nadabo


SHORT STORY

Page 6 to 10


Abba ya ci gaba da cewa.

"Zan ka fa miki dokoki in har kika yi biyayya ba tare kin tsallake ko ɗaya ba to za ki zauna a gidana, botsare wa dokata daidai ya ke da barinki gidan nan na farko kenan, sannan na biyu kar ki ƙara taɓa komai na gidan nan ko da kofin gidana ban yarda ki dauka ba, na uku duk wani abin da kika san mallakina ne ki tattaro ki kawo min kama daga ATM card, car keys da credisiah da kika san da kuɗina kika same su  duk ki tattaro min yanzu, kuma ban yarda kici abincin gidana ba, ki koma BQ ɗin gidan nan ki zauna kar na ƙara ganin kafarki a parlourna domin ban shirya mutuwa ta dalilin cutar dake tattare dake ba, yanzu nake son ki ba no komai nawa ba sai anjima ba."
          Tun da ya fara magana take kuka.
     'Wani irin rayuwa ne wannan? Ashe mahaifi yana komawa makiyi? Anya ma sune suka haifeni kuwa?Anya sune mahaifana? Anya sun san zafin 'Ya'Ya kuwa? A tunani da sanina in kana ɗauke da ko da cutar kuturta ne iyaye suke fara rungumar ka kafin duniya su soka, wayyo Allahna, wayyo rayuwa, wayyo Allah ka kawo min agaji.!'
       Tsawar da ya daka mata ne ya dawo da itah daga duniyar tunanin da ta faɗa.

         Hanci ta ji haɗe da cewa.

"Na ji Abba zan yi yadda ka ce amma Don Allah ina son ka faɗa min su waye iyaye na? A ina suke kuma a wani gari suke Don Allah Abba ka faɗa min."
      Duk cikin kuka take magana.

"Kina tunanin wasu ne iyayenki bamu ba? To ina mai shawartarki da ki buɗe kunnuwanki da kyau ki ji ni baki da wasu iyaye sama da mu, mu ne mu ka haifeki, ga uwarki nan itace tayi nakudar ki har kika kawo yanzu, muka ba ki duk wani gata da ake bai wa autar yarinya amma ki rasa abinda zaki saka mana da shi sai mummunar cuta, bamu rageki da komai ba, babu inda muka tauyeki da shi daga Islamiyya har boko mun baki ilimi daidai gwargwado amma kika wasa mana ƙasa a idanu kuma wallahi in har kika je neman taimako a gurin 'yan'uwana da 'yar'uwarki Allah ya isa ban yafe miki ba Faineesat."
            A razane ta ɗago kai tana kallon Abba. ya ce.

"Eh abin da na faɗa kenan, kema Hajiya daidai da gishiri kika ba ta wallahi ban yafe miki ba, bazan tsine miki ba amma ki je ke da duniya, tashi ki kwaso min kayana kuma ki fice min a cikin gida."

"Abba zan fita kuma na yi maka alkawari ba zan nemi taimako daga gurin dangin Umma da naka ba, amma Abba ku sani wallahi Tallahi, Na Rantse da Girman Littafin Allah Mai Tsarki BAN AIKATA BA ban yi abin da kuke zargina ba, kuma nima ban san ta yadda na samu ciwon nan ba."
         Da rawar murya ta ke magana , ta ja hanci ta ci gaba.

"Abba kafin na tafi ina neman yafiyarku tare da albarkar ku don Allah.!"

"Wallahi in kinga na yafe miki na tabbatar da ba zina kika yi kika samo wannan cutar ba. Ke ko Ummanki ban yarda ta yafe miki ba Feesat. Ki je duniya ta yafe miki domin ita ce za ta fara miki dariya domin kuwa kin tashi har kin taka rawar gani a gangar da ta yi miki, don haka ki tashi ki kwaso min kayana ki fita ki bar min gidana."
           Ta tashi jiki a saɓule ta tattaro duk wani abu da tasan mallakin Abba ne ta kawo ma sa, kayan sawa ne kawai ta fita dasu sai sallaya tare da Al'Kur'Ani, ta mika masa komai hatta babbar wayar hannun ta ya karbe baby nokia kawai ya barta shima ban san dalilin daya bar mata ba, harta fita ta dawo ta ajiye masa wayar ta ce.

"Abba nagode da komai na rayuwa da ka min amma bazan iya tafiya da wayar nan ba ga shi domin shima mallakin ka ne Abba, gurin zamar daka bani ma In Shaa Allahu inna samu gurin zama zan bar maka gidanka nagode da arzikin gurin zamar daka min.!"
       Da sauri tabar ɗakin saboda kukan da yake son cin karfin ta, sai da ta yi mai isarta sannan ta ja kafarta zuwa ɗakin da aka bata, tana buɗe kofar katon ɓera ne ya yi mata sallama a razane ta fito daga ɗakin, mai gadi ne ya taso da gudu domin ganin abinda ya razana ta amma tun kafin ya kai ga kofar ɗakin ya ji an da ka masa tsawa.

"Kai Audu bar yarda ka taimakawa wannan yarinyar ba, daga yau na cire ta a cikin gidana, ka ɗauka 'yar haya ce take zaune a gidan nan, in kuma baso kake aikin ka ya kare a gidan nan ba."

"Toh yallaɓai In Shaa Allah bazan tsallake dokarka ba."
             Audu ya ba shi amsa cikin ladabi amma zuciyarsa a karye take na rashin hana shi taimaka wa Faineesat da bai yi ba.

Haka ta na ji ta na gani Audu mai gadi ya koma ya zauna jiki a sanyaye, cikin ikon Allah da dakewar zuciya ta kashe wannan ɓeran amma kuma sai me? Wani katon ramin ɓerayen ne yake mata marhaba da zuwa.

'Yau na ga ta kaina ya zan yi da wannan rayuwar? Wallahi ba dan kashe kai haramun ba ne da babu abin da zai hanani kashe kaina yanzu, amma bana so Annabi yayi fushi da ni domin na bijirewa dokar Allah, wayyo Allahna! Wayyo rayuwa! Wai me ke faru wa dani? Mai yasa duk irin haka bai faru da kowa ba sai ni?  Wallahi ban taɓa zina ba ban taɓa kusantarta ba to garin yaya hakan ya faru?'
         Kiraye-kirayen sallar da ake yi ne ya dawo da ita duniyar zahiri ba ta zuci ba. Ta ce.

"Yanzu ya zan yi ga shi babu ruwa a ɗakin nan ya zan yi to na yi alwala? Wa zai ba ni ruwar alwalar da zan yi sallah?"

'Babu wanda zai baki ruwan sha balle kiyi sallah in zaki tashi ki nema gwara ki tashi. Domin a ahalin gidan nan babu tausayi a zukatan su balle imani ya samu matsugunin zama a zuciyar su.'
        Zuciyarta yake bata shawara.

"To ina zani na nema? Waye zai ba ni duk abin da nake bukata?  Waye zai taimaka min? ko ba kwa jina ne? Don Allah ku bani amsa ko zan ji daɗi.!"

_______________________________

To waye zai baki amsar Faineesat? Wata ƙil da abokan kwanarki kike yi su Alhaji ɓeraye ba domin ko ni ban san amsar tambayarki ba.

Karamar Su Babban Suce Ni 'Yar Nadabo


Basira Sabo Nadabo

BAN AIKATA BAWhere stories live. Discover now