MIJIN YAYATA KO MIJINA? PAGE 1

6 0 0
                                        

MIJIN YAYATA KO MIJINA💅🏼


NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨ ✍️

PAGE 1.

'Wannan wace iriyar rayuwa muke ciki da mata basu da ƴancin zama lafiya ƙalau a cikin; gidajensu,makarantu,da duk inda Allah Ya nufa rayuwarsu za ta wanzu a wajen? Me yasa maza suke kasa riƙe kansu akan mace ko da kuwa jaririya ce? Meye laifin matan? Ohh na fahimta,zuwanmu duniya a matsayin mata shine babban kuskurenmu a rayuwa. To ai ba laifinmu bane ba da muka zo a matan.'

Guntun tsaki Samhah ta yi tare da sake kulle rinannun idanuwanta da suka yi mata nauyi saboda tsabar shan kayan maye.

Kidan zamani ne ke tashi da ƙarfi kamar zai fasa madaidaicin parlourn wanda maye suka yi wa saman center table din da ya mamaye rabin carpet ɗin wajen ƙawa. Mata ne matasa su uku ke busa tare da kora kayan maye kala-kala. Biyu daga cikinsu suna da matsakaicin kyau,sun mallaki fata mai tsananin haske da haskaka idanuwan mai kallonsu. Ɗaya daga cikinsu kuma tana da matsanancin kyau,sai dai sam bata kai sauran ƙawayen nata hasken fata ba. Samha irin matan nan ne da ake kira da full option ,domin kuwa tana da jiki irin wanda yake a murje da cikar halittar da ba kowacce mace take da wannan baiwar ba. Samha na da dogon gashin kai mai cika da tsawo irin na Hausa Fulani,ta na ɗauke da dogayen gashin ido da na gira wanda suka ƙara wa kyakkyawar fuskarta kyau.

Tsananin buguwa da kayan mayen da ta yi ne ya sa ta kasa ɗaga hannunta yanda ya kamata. Cike da nauyin jikin da ya danne mata duk wata gaɓa da laka ta jikinta ta saki hannun ya faɗi yaraff. Da kyar ta iya sake dafe hannun kujerar da take kai ta yunƙurawa ta miƙe tsaye ta shige bandakin dake cikin parlourn. Karan sigarin dake hannun Laɗifah ta zuƙa tare da ɗaga kanta sama ta busa hayaƙin. A buge ta kalli Maleeka dake gefenta ta ce.

"Besty Malikah kinga yanda Besty Samha ta tipse ko tafiyar ma kamar a taya ta? Yau fa da dikkan alamu ta hau network da yawa kowa zai maida ta gida oho? Dan dai ni ba zan je ba na hadu da wannan shegen mijin Yayar tata mai ido a tsakar ka."

Dariya Malika ta yi cikin maye ta ce.

"Laɗifah Besty ai sai dai ta kwana anan kawai, dan nima ba zuwa zan yi ba. Ko kin san kwanaki dana maida ita gida guy dinnan nema yai ya ƙwamushe ni ya kai ɗakinsa. Ni fa tunda nake ban taɓa ganin baƙin dan iska marar kunya da gudun magana ba kamar wannan guy ɗin."

Ba tare da sun kula da fitowar Samhah daga banɗaki ba suka ji muryarta tana faɗin.

"Shegu magulmata me kuke cewa akan Yayana? To duk na ji maganganunku ni da kaina zan tafi gida dan bana fatan ta dalilina wani abu ya samu ɗayarku. Sosai nake jin tsanar guy ɗin nan a cikin raina;musamman saboda mummunan tambarin da ya manna wa rayuwata. Na rasa yanda zan yi na fahimtar da mutane har yau bai taɓa samun nasara a kaina ba,duk yanda zan yi bayani sai na samu wanda ya nuna ƙin yarda da kalaman bakina...."

Cikin hanzari Malika ta kalli Samhah ta ce.

"Dakata Besty Samhah, idan fa zaki shekara rantsuwa da bayani babu wanda zai yarda wannan dan akuyan bai keta mutuncinki ba,ke ko ƙur'ani zaki dafa babu mai yarda dake,ke dai kawai ai sha'ani wai ɗan birni ya cuci na ƙauye,ko ba haka ba Besty Laɗifah?"

Ta ƙarasa maganarta tana kallon Laɗifah wadda ke kaɗa kai cike da amincewa da kalaman ƙawar tasu. Nan take wani baƙin ciki ya kama zuciyar Samhah domin wannan shine babban abinda ke damunta a rayuwa. Sanin cewar kowa kallon da yake yi mata kenan ya sa take ƙara jin baƙin ciki da tsanar Mijin Yayarta da Yayar tata ma kanta. Hancinta ta share ta kalle su ta ce.

"Babu komai,ku yarda da duk abinda kuka ga za ku iya yarda da shi,Allah shine kaɗai shaida ta akan kare mutuncina da nake yi."

Cikin sauri ta ɗauki doguwar rigarta dake saman kujera ta dora akan riga da wandon dake jikinta;ta shige daya daga dakunan dake gidan ta kwanta,babu jimawa bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita cike da mafarkan da ta saba yi a duk lokacin da ta rintse ido da sunan bacci.

Has llegado al final de las partes publicadas.

⏰ Última actualización: Aug 17 ⏰

¡Añade esta historia a tu Biblioteca para recibir notificaciones sobre nuevas partes!

MIJIN YAYATA KO MIJINA?Historias para obsesionarse. Descúbrelo ahora