PAGE 1

5 1 0
                                        

*S A L M A N*
*A 2026 NOVEL*
*AWA*

001

"Kada ka taɓani Salman! Kawai ka matsa baya."

"Dan Allah ki saurare ni Hauwa..."

Cikin wani irin taratsi ta sake ɗaga sautin muryarta ta ce.

"Ba za a saurarekan ba! Na ce ba za a saurare kan ba Salman! Ni za ka rainawa hankali?"

"Hauwa please..."

" Wallahy Salman kaci ƙarya ka kwana da yunwa ka ce wai zaka yi min kishiya a ranar da zamu cika shekara ɗaya da aure. Wallhy tallahy na rantse da Allah ko Sama da Ƙasa za su haɗe ba zan taɓa yarda ba. Saboda haka idan ma wasa kake ka daina..."

"Wallahy ba wasa bane Hauwa,bakin gaskiyata nake faɗa miki wannan maganar...."

"To na rantse da Allah baka isa ba! Daman ashe baka so na jikina kawai kake so? Duk son da kake ta iƙirarin kana yi min ashe duk na Ƙarya ne na yaudara ne? Ni za ka kunyata Salman? Ni za ka tozarta ka kunyata a idon mutanen duniya? To yaushe ma akayi daren ballantana ace gari ya waye..."

Salman dai still cikin sigar lallashi ya sake ɗan ƙara matsowa ya ce.

" Wallahy ina son ki Hauwa, ina son ki son da ban taɓa yiwa wata mace ba..."

Da wasu irin hawaye ta girgiza kanta cike da karyewar zuciya ta ce.

"Ƙarya kake Salman! Wallahy ƙarya kake baka so na. Da ace kana so na da gaske ba za ka tsiri yimin kishiya da haihuwa ɗaya ba ko cikakken wata biyu ban yi ba. Da kana so na da gaske banga wata macen da za ta burgeka shekara ɗaya da aurenmu ba."

"Hauwa mi zan faɗa miki ki fahimce ni?..."

"Daman mi kake da shi da za ka faɗamin bayan ka riga ka cuceni ka gama dani. Mi na gaza maka da shi? A ɗan zaman da mukayi mi na aikata maka da zafi haka da har kake sha'awar kasancewa da wata Mace?"

"Wallahy Hauwa babu abinda kika mini.."

Wani irin tuƙuƙi take jin zuciyarta na yi mata. A yau ba ƙaramin mamaki Salman ya shayar da ita ba. Ko a mafarki aka ce zai iya aikata mata hakan tabbas zata Ƙarya ta. Salman ɗinda ke nuna mata tsananin so da ƙauna. Salman ɗinda ke nuna mata cewa duk duniya babu wata mace bayan ita. Mutum nawa ya zo neman aurenta amma ta kafe tace sai shi? Amma wai shi ne yau babu kunya wai ya ɗauko ƙafa ya zo mata da magana wai zai ƙara aure a ranar da za su cika shekara ɗaya cif da aure.

"Hauwa..."

Hannu ta ɗaga mai da sauri alamar ya dakata tana mai kafe idanuwanta cikin na shi ta ce.

"Na tsaneka Salman! Bana son ka kuma bana son ma ƙara ganinka a kusa dani. Kasani, a yau aure ya ƙare a tsakaninmu domin na gama zama da kai har abada ko kai ne kuwa ɗan autan Maza. Ka ci amanata kaje na barka da Allah.."

Hannunta ya riƙe cikin zafin nama tare da rungumota zuwa jikin shi, sai dai bai samu damar riƙe ta ba sanadiyyar saka dukkan ƙarfinta da tayi ta ture shi ta juya ta fice kai tsaye ta bar masa parlourn.

Komawa ya yi ya zauna daɓas kan kujera ya saka dukkan hannayensa ya dafe kansa gabaɗaya. Ya yi mamaki sosai da irin reaction ɗinta. Mace ce ita mai hakuri da sauƙin kai. Yanzu gashi ya zo da dukkan ƙwarin gwiwarsa amma kuma gabaɗaya ya ji ya karaya.

Ya ji ma zaune a parlourn yana mai saka rai da burin cewa za ta dawo amma shiru har tsawon mintuna talatin bata dawo ba. Wayar sa da ta fara ringing ne ya ciro ya duba, yana ganin sunan Hafsah ya buga tsaki tare da mayar da wayar a aljihunsa domin gabaɗaya ma ya ji har ita ɗin haushinta yake ji.

Yana nan zaune sai ga ƙanwar Hauwar mai bin ta wacce ake kira Hannatu ta shigo. Direct wurin Anwar dake bacci kan 3seater ta nufa ta ɗauke shi kurum ta juya ba tare da tace mishi ƙala ba. Idan ma idonsa ba ƙarya yake gaya masa ba kamar ganin ya yi Hannatun tana harararshi.

SALMAN Stories to obsess over. Discover now