Book1 page1

20 1 0
                                    

*TARKON ƘADDARA🔗*
        Mom Islam

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.

Ayi haƙuri ba kullum zan dinga posting ba.

Idan kinason ganin posting koda yaushe kiyi following channel ɗina ga link nan 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaMBjPlIXnlqjwkPyQ2l

Book1
Page1

A hankali Hakeem ya durƙusa ƙasa tare da dire guwaiwoyinsa, gabaki ɗaya damuwa tayi wa zuciyarsa ƙawanya, sakamakon jinin dake faman zubowa a tsakan kanin babban ɗan yatsansa na dama, "ya Allah.."
Kalmar da ta fito daga bakin Hakeem kenan, yakai tsawon wasu lokuta bai miƙe ba kansa yana sunkuye yana faman ƙarewa ƙafar tasa kallo, a hankali ya miƙe jikinsa na faman karkarwa sakamakon jiri dake ɗibarsa, ga wata gagarumar yunwa dake ƙwaƙularsa, hannunsa riƙe da cikinsa ya cigaba da tafiya, ba wata tafiya mai tsayi bace tsakaninsa da inda zai je, sai dai a yanayin tafiyar da yake yi wanda ke bibiyarsa zai ga nisan tafiyar, koda yazo ƙofar wani gida wanda ya kasance babu ƙofa sai labulen buhu, sanya hannunsa yayi ya dafe goshinsa kana ya kutsa kai ciki jiki a sanyaye,
Koda ya shiga gidan bai ƙarasa ciki ba, yakai 30mins yana kallon Ammu dake ta faman haɗa wuta a murhu, zuciyarsa cunkushe da tarin takaicin halin da ya tsinci kansa ya kai kallonsa ga murhun da Ammu ke haɗa wuta, ledoji ne sai goruna da buhu, hayaƙi sai tashi yake kamar wacce take gasa kan rago, "inka bibiya ma zallar ruwa aka ɗora"
Hakeem ya faɗa a zuciyarsa yana mai karasawa ciki.
"Sannu da dawowa ɗan albarka, har na haɗa wuta kafin ka dawo Allah yasa an samo..."
Jinin da taga yana faman fitowa a ƴan yatsun nasa ne ya katse mata maganar da take yi, jiki a sanyaye hankali a tashe ta ƙarasa inda Hakeem yake tsaye, "ɗan Albarka mai ya faru dakai?"
Kansa a sunkuye yace "Ammu ana neman mai yin faskare ne shine nace na iya, na ɗaga gatari zan sari icce kawai naji na buga akan ƙafata, abin mamaki sannu kawai mutanen gurin sukayi min, Ammu rayuwar yanzu tana bani mamaki mutane sun koma babu tausayi sam?"
Ammu ta kasa bashi amsa, sakamakon kiɗimewa da tayi, ɗakinta ta  wuce cikin  sauri ta tsiyayo kalanzir a fitilar kwalbar magani da ta haɗa suke sanya kalanzir ko manja, tazo ta zuba masa a ciwon sannan ta koma ɗaki ta yago tsumma ta ɗaure masa ciwon kana ta nemi guri ta zauna.
"Wato Hakeem rayuwar yanzu ba'a cewa komai, wasu Allah ya wadatasu amma bazasu taimakawa talaka ba, wasu kuma basu dashi ne" Ammu takai ƙarshen maganar tata tana matsar ƙwallar data ke kokawar gangaro mata saman fuska, "Ammu tun fita ta ko sisi ban samu ba, amma barin gwada zuwa gurin mai shago tunda jiya na biyashi bashin da yake bina ƙila ya bani wani"

"Hakeem Allah yayi maka albarka Allah yaji ƙan mahaifinku Ubangiji ya ɗaukakamin kai bisa tafarkin gaskiya"
Ummu ta dinga kwararo masa addu'a har ya fice.
Kai tsaye gurin mai shago ya nufa, bayan yayi sallama sun gaisa yace, ”dan Allah mai shago yauma dai kamar koda yaushe kar a gaji damu”

Sai da mai shago ya harareshi kafin yace ”ka san da cewar komai ya tashi ko? me kake so a baka kuma gobe zani kasuwa da safe ka kawomin kuɗin idan ba haka ba wlhi tallahi ka kashe wutar gaba, irin ku ne masu kashewa mutane shago da mugunta ƙiriƙiri"

Sai da Hakeem ya jira mai shago ya gama yi masa tijara kafin yace "garin kwaki zaka bani rabin mudu sai suga na ɗari"
Kallon baka da hankali mai shago yayi masa kafin yace ”ko ina zakaje a faɗin gari nan babu wanda zai baka suga na ɗari, zan baka na ɗari biyu idan aka haɗa da kuɗin gari ya kama ɗari shida kenan"
Hakeem yace "toh na gode Allah ya bani ikon kawo maka goben"
Mai shago ya amsa da "Amin” kafin ya miƙawa Hakeem ledar ya wuce, "yaya..yaya...yaya" Ahlam ta ƙwala masa kira tana ƙarasowa da gudu, sai da gabansa ya faɗi tsabar ruɗu da firgici,
"Badai an koroki bane?"
Hakeem ya faɗa saboda yaji dalilin fitowar ta daga makaranta,
"Yaya kafin malam ya koromu sai da yayi mana duka wai duk wanda bai kawo kuɗin makaranta ba ya zauna a gida gashi yau zamu fara jarabawa"
Ahlam takai maganar tana kwaɓe fuska zatayi kuka.
Sai da Hakeem ya jinjina kai kafin yace "Ahlam ki koma makarantar kice gani nan zuwa, zan kaiwa Ammu abinci in taho" ihu Ahlam ta tsala tana bubbuga ƙafa tana cewa "yaya kullum haƙuri muke basu gashi nan har an fara yimin gori yau dai sunce bazasu haƙura ba nikam idan na koma dukana za'ayi"
"Yaro kenan"
Hakeem ya faɗa a fili yana jifanta da mugun kallo, sam batajin abinda yake cewa saboda kururuwar da takeyi ita bazata koma ba, ita dukanta za 'ayi, tsabar takaici bai san sa'adda ya daka mata tsawa ba, sai da ta razana sosai jikinta har rawa yake tana ƙare masa kallo, saboda bai cika yi mata faɗa ba, da sauri ta kama hanyar zuwa makarantar ƙirjinta na dukan uku-uku, sam ta kasa shiga ciki sai ta tsaya a bakin ƙofar shiga makarantar.
"Kee mekikeyi anan ba an koreki ba?"
Ɗaya daga cikin malam yayi mata magana, sai da ta turo baki kafin tace "yayana yace yana zuwa"
Babu wanda ya sake tanka mata har ta shiga aji ta zauna, sai dai kaf ɗaliban dake zaune ko wane hannunsa riƙe da takardar jarabawa itakam tsuru tayi tana ta rarraba idanu.
  Yana tafe yana ɗingishi ya ƙarasa gida, Ammu na durƙushe tana ci gaba da yayibo makamashi tana turawa a wuta, "Aslamu alaikum" Hakeem yai sallama yana ƙarasowa gurin Ammu,
Ammu ta amsa da cewa "wa'alaikumussalam ɗan albarka an dace ?"
"Eh an dace Ammu amma..."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 14 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

TARKON ƘADDARA Where stories live. Discover now