9

10 1 0
                                    

💥KISWAH💥

(Surrogacy was the cause)

          Na

CHUCHUJAY ✍️

Book1⃣

Page 9⃣

AL'HAIDAR PRIVATE HOSPITAL.

    Cikin Yanayi na nutsuwa Haidar ke takawa domin isa office ɗin sa inda yake mai karban gaisuwar ma'aikatan sa yana miƙa musu cikin girmamawa , yana isa bakin office din sa Ya saka key domin buɗewa amma ga mamakin sa yaji kofar a bude ,turawa yayi yana mai tunanin Ko jiya bai kulle ba Ya wuce,turus yayi lokacin da Ya shiga office ɗin ,roses ya ganin an cicire su an rubuta Good Morning love da kuma tambari na heart,kan desk kuma dauke da food pack wanda ba a bude ba ,dan kalle kalle Ya fara dan ganin Ko zaiga giftawar wani ,a hankali Ya taka dan sake dubawa,kofar shigowa da yaji an buɗe ne Ya sakashi waigawa,Kiswa ce tsaye bakin kofar hannun ta dauke da leda yayin da fuskar ta ke dauke da babban murmushi,dafe fuska Haidar yayi yana mai sauke ajiyaar zuciyar ganinta Kafun Ya ƙarasa gareta hakoran sa washe kamar anma yaro kyautar candy.

Ledan hannunta Ya karba yana mai fadin"Good morning my romantic heartrob to what did i owe this?"

Faɗaɗa murmushinta tayi ta shigo ciki tana mai cewa"to love masoyi,i woke up naji yau ina san ka fara sakani a idanun ka idan kazo office ɗin nan and of course i made you breakfast dan na sanka da rashin san karyawa idan zaka fita office which you will have to work on dan idan mukayi Aure bazan dauka ba,yanzu abunda za'ayi ka zauna nayi serving maka breakfast Then na wuce aiki cos kar ka manta i work for someone and i cant afford being sacked".

Cike da wani irin santa dake faman fuzgarsa ya zauna inda ta masa nuni yana mai binta da ido fuskarsa dauke da wani irin murmushi na farin ciki da ya kasa cirewa ,.

Buɗe food pack din tayi ta ciro Kulan dake dauke da plantain mossa,sannan ta dauko plate ta saka masa guda uku manya a kai Then cutleries Kafun ta aje a kan cinyansa then ta ciro Cup ta buɗe karamun flask ɗin dake dauke da kunun gyaɗa a ciki ta zuba sannan ta dawo Gefensa ta zauna tace "bismillah hero and mind you sai ka cinye mossa ɗinn nan da kunun gyaɗan nan,"rufe idanunsa yayi ya buɗe yana mai shaƙar kamshin abincin dake gaban sa Kafun yace "my favourite,ya akayi kika sani ban taba faɗa miki ba idan Zan tuna"

Haɗa hannayenta tayi guri ɗaya tace "well idan ban san favourite abunda mijin da zan Aura nayi rayuwa ta har abada dashi ba mai ya kamata na sani?,well just eat already"

"What about you?"ya tambaya yana mai zuba mata ido.

Wani fari da ido tayi Kafun tace "well ni a ƙoshe nake burina kawai kai ka ƙoshi,"murmshi yayi yayi bismillah ya fara cin abincin Cikin nashaɗi, bayan ya gama Ya kalleta da soyayya yace"Allah yayi miki albarka Kiswa,Allah ya mallaka mun ke a matsayin matata uwar ƴaƴana wallahi ina sanki da yawa sannan a kullum sake sanki nake sosai ba wai so na wasa ba,dan Allah ki dage da yin Addu'a kema Allah yasa mu mallaki juna kafun mu koma ga mahaliccin mu".

  Tashi tayi ta fara haɗa kwanikan kafun tace"na faɗawa Mama maganar ka jiya da mukayi waya and ta ƙosa na kawo ka Bauchi ta ganka,i can tell tun Kafun ta ganka kayi mata already"

Cike da zumuɗi yace"OmG Baby i love you ,dan Allah ki samu free time muje cos ni kaina yakamata na ga macen da ta haifa mun macen da bana da nutsuwa idan akanta ne"dan shiru yayi kafun yace"Yea kafun na manta ina ganin ya kamata ace by this time Mother ta san dani a rayuwarki sabida rashin sanin yasa ta samu Ummi jiya a office tana san haɗani da Farry na Aura and im sure dan bata san muna tare bane ,but i told Ummi jiya about us and tayi farin ciki sosai dan idan da dan ranta ne yanzu ma na kaimata ke ta ganki,ba kiga yarda take murna  ba".

KISWAH 1✔Where stories live. Discover now