8

23 1 0
                                    

💥KISWAH💥

(Surrogacy was the cause)

       Na

CHUCHUJAY ✍️

Book1⃣

Page8⃣

    Tun fitar Kiswa daga gida taga kamar ana binta a baya ,juyowa tayi dan ganin wanene dan for sure bin nata ake,"'ya Sageer ?"ta furta tana Mai kalllan sa ,Takowa yayi inda take yana Mai sosa ƙeyarsa yace "sai ina"?

Faɗaɗa murmushin ta tayi tace "wallahi im going out for a dinner date ne so bana san nayi dare nake san nayi making ɗinsa fast,".

Kallan agogon hannunsa yayi kafun 'ya maida kallan fuskarta yace"so my Baby sis have a man amma baki taba faɗa mun ba har ma kinyi girman zuwa dinner date da namiji"

Dan ƙaramun murmushi tayi tace "'ya Sageer mana,ina jiran lokaci ne nayi introducing ɗinsa gida wanda ina Ganin lokaci yayi cause i don cast,"maganarta ta ƙarasa tana mai ƙokarin saka humour a ciki amma ga mamakinta ya Sageer bai responding ba illa ma haɗe rai da yayi kafun yace"what if idan nace baza kije ba".

Ganin yarda yayi magana in a Serious tone ne ya saka Kiswa cewa"Dan Allah ya Sageer kar ma ka faɗa saboda bana san a tashi yau ina daga cikin masu yiwa yayyuna rashin biyayya,and idan kace kar naje inda haidar yake a yanzu bansan ya zan hana kaina ba saboda na saka masa rai tun dazu yake kira na,idan kuma banje ba i swear bazai ci abincin dare ba ni kuma i cant sleep with that fact!"

"Inyeeeeh"muryar ya Sameer ta bayyana bayanta"wani irin kunya ce ta lullube ta dan da saurinta ta juya ta bar gurin dan bata san mai zata kuma cewa ba domin sai da ta gama maganar kunya ta kamata ,She's so much in love da take mantawa da kawaicii akan Haidar  domin kuwa taga idan ta biyewa kawaici za'ayi mata sakiyar da ba ruwa .

Kallan Sageer sameer yayi yace "mai yasa zakace zaka hanata fita ,shes matured enough' sannan i trust Kiswa bazatayi abunda zamuyi Allah wadaran da ita ba,nasan abunda kake ma tarewa kenan,Chill and calm down dole wataran gidan wani zasuje and idan ba yanzu ba sai yaushe".

Dan murmushi sageer yayi yace "bro kasan mazan yanzu ne burin su su dauki advantage na mace ,ni kuma bana san wani abu makamancin haka yake samu sisters' ɗina ".dafasa Sameer yayi yace "insha Allahu sai dai Alheri bari na shiga ciki naga kamar zaka fita ne".

Wucewa Sameer yayi yayin da Sageer ya bi bayan motar Kiswa data fita da kallo yana

Mai jin wata irin fitina na dukan Ko wanne sashe na zuciyarsa dangane da ita.

                                ********

    Tsaye black BMW din mother take a bakin katafaren Boutique ɗin dake dauke da suna ZEE BULA Fashion House tana mai duba wayanta dan kar taran da take hari ta wuce bata gana da hajiya Zainaba Bula ba ,yau zata nunawa Kiswa mene ake kira da kuɗi da isa da kuma karfin burin Uwa,

Tana wannan tsayuwa kuwa motar Hajiya zainaba ta faka inda Bodyguards ɗinta suka fito su biyu suka buɗe mata ƙofar mota ta fito cikin shiga ta alfarma,yar gayuce mai harka da abunda ya shafi gayu shiyasa Mother ma ta kashe nata gayun dan zuwa ganawa da ita,sai da ta Bari Tayi wurin minti ishirin da shigaa ciki Kafun itama ta fito ta kulle tata motan ta nufi ciki ,bayan dan zagaye da tayi a ciki ta haura sama da taimakon ma'aikaciyar gurin domin ganawa da Md wato hajiya Zainaba,da fari basu bata dama ba amma da sales manager ɗin taga irin shigar jikin Mother sai jikinta ya bata ƙawar Hajiya BULA ce dan sukan yawan kawo mata ziyara shiyasa Mother na mata ihsani ta mata iso zuwa sama,bayan zuwan su PA dinta ta kira waya akan tayi baƙuwa,bata expecting kowa dan haka tace Ko ma Wane yayi booking appointment tukunna.

    Nacin Mother da persistence ya saka Daga karshe Hajiya Bula tace a mata iso ta shigo ,kallan katafaren ofishin Hajiya Bula Mother ta fara Kafun ta fito daga wani daki da yake na hutawanta fuskarta Babu yabo Babu fallasa,zama tayi tana mai kallan Mother cikin kallan Ban sanki ba Kafun tace"barka Ina fatan dai wannan zuwan naki mai amfani ne a yarda na karbeki babu Appointment sai gashi kuma yazo da ban ma san fuskarki ba,hope im safe."

KISWAH 1✔Where stories live. Discover now