5

32 1 0
                                    

KISWAH

(Linked By surrogacy )

                Na

CHUCHUJAY ✍️

Book 1⃣

Page5⃣

  Monday Morning.

Safiyar litinin ya kasance Kiswa bazata fita aiki da wuri ba sai 10 da rabi dan haka bata fito breakfast ba lokacin da dukkan su sunayi sai wurin Tara wanda lokacin kowa na gidan ya fita har da Baraka mai Aiki wadda ta tafi kasuwa domin siyan kayayyakin da Babu 'na amfani.

Fridge ta buɗe domin dauko fresh milk dan ita kawai zata iya sha tunda bata craving wani abinci mai nauyi Cos yau suna da lunch Da chairman Basil ya shirya a kamfanin ta tarbar ɗansa da zai fara zuwa office din yau.,tana kan danna wayarta a yayin da take shan fresh milk din taji kamar ana kallanta,daga kai tayi sabida yarda jikinta ya cigaba da bata Eh tabbas ana kallanta ɗin,kan ya Sageer ta sauke su wanda ke tsaye in a mess Cos daga ganinsa ba sai ya faɗa maka ko wanka baiyyi ba,singlet ce baka a jikinsa sai boxer wanda ke nuna mazantakarsa ta ɗa namiji wadda turawa kewa laƙabi da" morning bone"saurin dauke idanunta tayi cause This is not like Him.

    Ganin abunda tayi ne ya sakashi yin karamun murmushi kafun ya tako yana mai dauko Cup ya karbi kwallin fresh milk ɗin gefenta ya zuba 'ya fara sha yana maiyyi mata wani irin kallo kafun yace"Kiswa baki ganni bane babu ko gaisuwa"?

cup dinta ta kai cikin sink tana mai kunna tap dan wankewa kafun tace"ina Kwana 'ya Sageer baka fita ba ashe ,And Yes you need to get dressed dan you're semi naked,Nasan nima dan baka expecting dina a nan ne ka shigo hakan ,nima yanzu nake san wucewa gurin aiki ,hope you're okay "Murmushi yayi kafun ya tako inda take shedan yana hura masa wata irin sha'awarta wadda ya jima yana faman dannewa,aje nasa cup din yayi cikin sink din sannan ya zauna a gefe yana mai kallanta tana ɗauraye nasa cup din,hannunsa yasa a hankali ya shaafa nata wanda taji zuwan a bazata ,ɗago kai tayi ta kallesa ta ɗaga masa gira ɗaya tace"lafiya dai ya Sageer"?

Cije lebensa guda ɗaya yayi yace "lafiya ba lafiya ba,taimako ne nake san kiyi mun wanda ke kadaice zaki iya yinsa a duk duniyar nan".

Da mamaki ta kallesa sannan ta taka Dan zuwa aje cup din a ma'adanarsu tana mai cewa"Nikam 'ya sageer wanne irin taimako ne da ni Kaɗai zan iya yinsa duk duniyar nan?Just shot it Allah yasa wanda zan iya ne dan bana fatan wani dan uwa na ya nemi abu gurina na kasa masa kar ma ace 'Kai,'ya sameer ko Farry ,sai dai idan yafi karfina ko kuma ya sabawa mahaliccina".

Taune lebensa na ƙasa yayi kafun ya sa hannunsa yana mai rufe gabansa da ke neman fita masa,yana ƙokarin magana muryar Baraka ta katsesa wadda ta shigo kitchen din kai tsaye saboda mantuwan pack ɗin da tayi,a tare suka daga Kai suka kalleta, sallama tayi Kiswa ta amsa tana Mai fadin"baki wuce ba ashe baba baraka"

Kallan Sageer tayi kafun tace"wallahi har naje titi nayi mantuwa na dawo,ashe Alhaji karami ma bai fita ba"wani banzan kallo Sageer ya bata ba tare Da ya tanka ta ba ya  sauko yana Mai kakare gabansa ya rabe ta gefenta yana Mai cewa Kiswa"sis chat you up later"

Okay kawai tace masa tana Mai binsa da kallo saboda ba Haka ta san ya SAGIR ba,tabbas wani abun ba dai dai bane ba,shigowa Baraka tayi itama tana Mai binsa da kallo kafun ta dawo da kallanta kan Kiswa tace "kiswatu Anya sagiru kalau yake"?'dan tabe baki Kiswa tayi tace nima dai Bansan Mai ke damun sa ba Cos ko niyar fita aiki banga yana da ita ba kilan dai yana da uzuri ne,dauko pack din nan rage miki hanya Cos nima yanzu zan fita,

"To" kawai baba Baraka tace amma yanayin sagir da yarda ta shigo taga yaana kallan Kiswa abu ne da a matsayinta na babba tasan akwai wani abu a ƙasa,har suka bar gidan ita da Kiswa abun yana ranta tana tunanin ta yarda zata fara fadarsa,kasa hakuri tayi domin tana ganin Kiswa ne matsayin diya a gurinta 'dan haka bazata iya ganin abu zai cutar da ita ba ko ba dai dai ba tayi shiru dan Haka cikin hikima irin ta babba tace"Nikam kiswatu ina san faɗar wani abu ina tsoro Ban san ya zaki dauki magana ta ba"

KISWAH 1✔Where stories live. Discover now