Page 4

14 1 0
                                    

KISWAH

(Linked through surrogacy)

              By

CHUCHUJAY ✍️

Book1⃣

Page 4⃣

     "Uhum Hajiya Farry ina jinki kince kina da magana dani"Kiswa ta faɗa tana mai taje sumar kanta mai madaidaicin yalwa,

Tasowa Farry tayi tazo inda Kiswa take ta zaunar da ita kan stool sannan ta karbi comb ɗin hannunta ta cigaba da taje mata kan tana shafa mai a hankali,daga kai tayi ta kalli mudubi wanda ta tarar da idanun Kiswa a ciki suna kallonta irin kallan nan na "nasan wani abu kike so"

Aje comb ɗin tayi tace "Fine i want you to do me a favour dan Allah Kiswa,"zagayowa tayi ta durkusa gaba Kiswa ta kama hannunta tace "Dan Allah Masoyiya taimako na zakiyi dan nasani kina mun soyayyar da bazaki So na faɗa halaka ba,a wannan karan kuma halakar ke kirana,Appa da mother ne ya suka haɗa mun blind date da wani yaran abokinsa wai muje mu sasanta kan mu,kin dai san abunda ya saba mun and i hate it sosai "shiru tayi tana kallan Kiswa wadda tayi mata alamu da hannu tace "uhum So?"dan tasan maganar Farry ɗin bata ƙare ba.

Cije lebe  tayi tace"nayi bincike akan sa and bincike na 'ya nuna mun he's not the guy at all dan ba mutumin kirki bane,dan shaye shaye ne sannan clubber dan ance mun har giya yana sha ga neman mata na bala'i"cije lebe farry tayi tana tunanin Ta ina zata fara roƙon Kiswa ,rufe idanunta tayi gam tace"ina son kije a maimakona nasan you can handle Him ta yarda bazai yarda da Alliance din nan ba"

Mikewa zumbur Kiswa tayi tace"na miki sau ɗaya sannan idan na tuna na faɗa miki shine na farko shine na karshe ,solution ɗin is simple,muje mu samu Appa mu faɗa masa dukkan ill halayyarsa da kika lissafo mun in yaso  ya sake bincike ,nasan dai babu yarda Appa zaiyyi ya Aura miki miji irinsa"

Ganin fa da gaske yanayin Kiswa yake ya saka farry fashewa da kuka tace"kina tunanin Appa Zai saurareni? Zaice kawai ina san kaucewa Aure ne amma ni ba Haka bane,and worst thing din im not even lying,na kasa zama na fadawa kowa sai ke amma kema da nake tunanin zaki tsamoni daga faɗawa halaka kince a'a ."kuka sosai Ta cigaba dayi wanda yazo ma Kiswa cikin rashin zato da tsammani,da saurinta ta koma ta kamo Farry tace "haba Farry mene hakan?Ban dauka wani abun ba sannan nayi zatan hakan zai zama best solution ne im sorry,when are you guys meeting sannan a ina ne"?.

    Da sauri Farry ta ɗago tace "kina nufin zaki je?"

Kada mata kai Kiswa tayi tace "Amma wannan kawai Babu next time dole ne kisan ya zakiyi da rayuwarki sabida you're not getting any younger,dole kiyi Aure kije gida wani no matter abunki,sannan wannan zanje ne saboda na san koda nice a situation ɗinki zakiyi mun Haka,but This should be the last time,no it has To be the last time".

Da sauri Farry ta share hawayen ta tace "thank you sister ina mutuwar sanki,lunch time zamu haɗu a "meet up restaurant. "

And ai kema Haidar bai motsa ba and ke ya kamata ma ayi maganar Auranki bani ba.,kallanta Kiswa tayi tana san kauda duk wani tunani kafun ttace"well gwanda Ni tunda ina ma da wanda nake kulawa sannan kinsan Auren nan is for your own benefit tunda kina san business dinki as a CEO ALIJUA company dole kiyi Aure kinsan dokan Appa and i work under wasu so stop compering ".

                       ********

1:30

MEET UP RESTAURANT ABUJA.

Cikin shiga wadda Kiswa batayi ta ke takawa dan shiga meet up,sanye take cikin body con mai dogon hannu mai kauri wadda ta fitar Da shape ɗin jikinta madaidaici mai kyan gani,boyfriend jacket ta saka a sama sai dan gyalen da kanta kawai ya rufe,fuskarta dauke take da hard Bitch make up wanda kana kallan ta sau ɗaya zakace wannan tab'ata kaji fitsarace yayin da bakin ta ke dauke da chew gum ɗin da take taunawa a hankali,inda Black lips ɗin da ta saka a lebenta dan charas ras yake motsawa cikin wani yanayi mai kyau,

KISWAH 1✔Where stories live. Discover now