page 3

30 1 0
                                    

KISWA

(Linked through Surrogacy)

            Na

CHUCHUJAY ✍️

Book1⃣

Page3⃣.

ALIYU'HAIDAR TUKUR BULA shine asalin sunan sa matashin saurayi mai shekara ashirin da tara ,haifafen cikin garin Abuja ne amma asalin su mutanen dutse ne dake cikin garin jigawa amma a tashin Haidar Abuja Ya sani gidan dan tunda yake da iyayansa biyu basu taba cewa yau Haidar shirya muje usulin Garin ka ba a yayin da shi ma bai damu ba ganin yan uwan nasu na chan garin suna zuwa inda suke.

Haidar ɗa guda ne tilo wurin iyayen sa Alhaji Tukur Bula da Matarsa Hajiya zainaba Bula dan haka suka dauki soyayya ta duniya suka ɗora masa ,Babu wani abu da Haidar yake nema a rayuwar sa ya rasa tun yarinta indai kuɗi ne zai bada su ,irin girman sangarta da akayi masa kawai ya ishe sa lalacewa a yayin girmansa Amma sai Allah ya rainesa cikin sahun mutane masu nutsuwa da sanin ya kamata,sau da dama mahaifiyar sa kan ɗorasa a abu mara kyau wanda zahiri tasan mara kyau dinne amma saboda dabia ta nasara sai ta danne inda shi kuma idan ya hanga rashin dacewar wannan abun sai yayi kokarin wajen ganin ya dorata a hanya.

Iyayen sa shahararrun masu kuɗi ne domin mahaifiyar sa babbar sananniyar yar kasuwace a garin wadda keda boutiques ɗin da zaka gaji da irgawa a yayin da mahaifinsa yake babban custom,magana ta rashi a gidansu Haidar fa babu ita domin kuwa Allah ya azurta iyayensa wanda dalilin hakan yasaka basu damu da subi danginsu inda suke ba sai dai su su biyosu inda suke su dan lasa.,

Rashin samun wani haihuwar bayan haidar baya damun iyayensa illa shi din da suka samu suka duƙu fa wajen tara masa abunda yake nasu ne ma'ana dukiyarsu,

Sanin iyayen Haidar Nada kudi bai taba kashe masa zuciya ba wajen neman na kansa duk da kuwa yarda mahaifiyarsa ke nacin yaji dadin rayuwarsa kawai domin kudi sun tara masa ba sai ya wahalar da kansa wajen nema ba amma yayi fafur akan cewa su barshi yayi aiki domin career ɗin abunda yake mafarkinsa ne kuma abune wanda yake da sha'awa tun yarinta wato aikin Likitanci,ganin ga abunda yaran nasu yake So shi yasa suka bude bakin jaka wajen ganin sun bashi ilimi isashe wanda ya samu ƙwarewa a harkar inda daga bisani suka tamfatsa masa Asibiti wanda yaci sunasa "AL'HAIDAR PRIVATE HOSPITAL "Haidar kwararren likitane wanda ya taba fannika daban daban ,sabida san zaman komai dai dai a asibitin Nasa yasaka yake daukar likitoci wadanda suka san mai suke ,a kalma guda Asibitin Al'Haidar asibitine wanda baza kace likita daya ke duba zuciya ba sannan ya duba hakori ya duba kunne ,ya duba ƙashi  da dai sauransu,asibitine da ke dauke da zuga na komai da ruwanka.

    Da kansa ya samawa kansa ilimin addini duba da iyayensa sunfi bada muhimmanci akan bokonsa cos bai taba zama ajin islamiyya ba sai dai malami yazo gida yayi masa wanda shima bayan fara tasawarsa aka sallamesa acewar Hajiya zainaba 'ya samu 'na sallah ,sanin yana bukatar bunkasa saninsa akan addininsa 'ya saka ya dage wajen sanin littattafai domin duk yarda yake san iyayensa yayi alwashin idan ya haihu bazai taba Bawa yaran sa tarbiyya irin wadda 'ya samu ba,mutum ne shi mai nutsuwa kamili wanda bai damu da sabgar yan mata ba duk da harin da suke kawo masa domin shi din mai kyaune da kyawun kira irin wadda duk wani namiji ke fata,sau da dama idan aka tada ma mahaiffiyasa maganar 'ya kamata yayi Aure sai tace "duka nawa Haidar din yake,abarsa yayi rayuwarsa cos life is too short duk lokacin da ya gama gwara kan yan mata ya samu ta Aure"jin Wannan furucin yasa ƙanwarta mahaifiyar Tasleem ta kawo tasleem gidan da zummar tana daukewa haidar din kewar rashin dan uwa amma a kasan zuciyarta ta kawo tasleem ne domin ta Auri Haidar nan gaba.

    Kowa yana saka da warwararsa a yayin da Haidar yayi gamo da tauraruwar da ta sace masa dukkan nutsuwarsa da tunaninsa a lokaci guda wata rana da tazo  asibitinsa,yana kokarin fita daga Asibitin tana shiga a motarta wanda ta shige da zuciyarsa at first sight,bai wata wata ba 'ya koma Asibitin 'ya jirata har ta fito 'ya bita, babu kasa a gwiwa 'ya fallasa mata asirin zuciyarsa,ya dan sha wahala kafun 'ya samu hadin kanta cos a ranar bata kulasa ba sai da yayi ta bincike 'ya gano inda take aiki ya sarrafi addabarta wanda a hankali ta bude masa tata kofa zuciyar da ta gama karantarsa,yarda bai taba budurwa in a Serious way ba Haka nan Kiswa dan haka suke ma juna mayyar soyayya cos akan juna suka san daɗin ta.

KISWAH 1✔Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt