page2

31 1 0
                                    

https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
KISWAH

(Linked through surrogacy)

    By

CHUCHUJAY

Book1⃣

Page 2⃣

MONDAY MORNING.

   Cikin gidan Na Alhaji Aliyu kowa ka gani yana sauri ne da kimtsawa domin tafiya aiki

,Kiswa wadda idan tayi sallar asuba bata iya komawa ce ta kamawa Baraka mai girkin gidan duk da kuwa yarda bata san Kiswa din na zuwa taya ta aiki amma nacin Kiswa ya saka ta barta dan Babu yarda zatayi da ita tun kafun ta kai haka.

    Zazzaune suke baki ɗaya kan teburin cin Abinci suna jiran Kiswa wadda bata kai ga ƙarasowa ba ,rules na gidan bai barka kaci abinci ba tare da kowa ya hallarci gurin ba ,idan kana saurine to ranar sai dai kaci abincinka daban,wani irin tsaki Barrister JUWAIRIYYAH taja tana mai kallan mijinta tace"wai kai Alhaji mene damuwarka da sai anjira kowa za'a karyane?wannan yarinyar sanin haka ya saka take miƙe kafafu a ɗaki sai lokacin da taga dama zata fito ,gaskiya abinci zanci dan ina da abunyi a court haba."

Cup din dake gabanta ta ɗaga dan haɗa tea,Alhaji Aliyu bai tankata ba har ta fara haɗa tea ɗinta sanin koda yace ta yi hakuri bayi ɗin zatayi ba,sameer da maganar mahaifiyar tasu bata gamshe sa Bane yace "Amma Mother jiya Sageer yafi kowa fitowa latti and we waited Babu wanda yayi complain,after all Babu mai latti tunda baifi mu ɗauki minti talatin ba wajen karyawa kowa ya kama gabansa,its 6:30 am saboda Allah.

Cike da masifa ta kalli Sameer tace"zaneni mana Sameer sai nasan kana shigar wa uwarka juwairiyyah faɗa,bana san iskanci fa Zan bata maka fiye da yarda baka zato,"kafin wani yayi wata magana Kiswa y

Ta fito cikin shirinta Na zuwa aiki tana mai faɗin"kuyi hakuri na saka ku jira ,Im sorry da kun fara without me"

Tsaki Mother tayi tace"su da zasu iya jiranki ai gashi nan suna jiranki tunda basu da abunyi ,Ina ga zubaida ta sassaƙasu"

Da ƙarfi Alhaji Aliyu ya daki  table din wanda da bashi da girma da yayi Bari,cikin yanayi na karsashi yace"sau nawa zanna faɗa miki ki cire zubaida daga fitinarki Barrister,ya isheni fa bana san kina saka ƙanwata a al'amarinki na rashin kirki na faɗa miki ba yau ba ba jiya ba "

Kallansa tayi narainarai da ido ganin yarda yake mata tsawa gaban yaranta which is not like Him,aje spoon ɗin ta tayi tace"Its okay ka cigaba da mun tsawa gaban yara amma hakan bashine zai boye gaskiyar cewa ƙanwaka Zubaida is a disappointment ba,sannan hakan bazai taba chanzawa ba so kama daina pretending caring brother cos kasani na sani its a pretence ,quit it already,excuse me"tashi tayi tana gama maganarta ta ɗauki jakarta ba tare da ta tsaya kula Sageer dake faman kiran sunan ta ba ta fice ,a hankali Kiswa taja kujerar kusa da Farry ta zauna tana mai faɗin"Im sorry about that,ba niyana nayi causing matsala ba ,na cire kayan da zan saka ne tun jiya so dana saka yau da safe yaki shigana since dama na daɗe ban saka ba so dole na sake neman wasu and i had to look responsible cause yau muna da baƙi masu muhimmanci and nice host dinsu sannan..."

    Dariyar da suka saka ne a tare ya katse ta,dan taune lebenta tayi tace"well i didn't think i sounded funny,"Sageer dake gefenta ne yace"Aikin jarida ne kawai ya dace dake mai ya kaiki karanta Public relation?,".

Ɗan murmushi tayi tace "dalilin da yasa Appa karantar Kasuwanci sannan abunda yasa Farry karantar kasuwanci,abunda ya saka Mother karantar Law,abunda ya saka Ya Sameer shiga Immigration da abunda ya kai ka Ya Sageer karantar Accountancy which is Passion "

"Case closed"Alhaji Aliyu wanda suke kira da Appa ya kara yana mai jin Kiswa har ransa,She's smart beyond expectation,yaso tayi aiki karkashin kamfaninsa amma taƙi wanda take ganin kamar alfarmace inda shi kuma ya rabu da ita dan baya san takurata amma ko yaushe idan ta shirya dawowa Akwai gurbinta.

KISWAH 1✔Where stories live. Discover now