ABUJA

Ahmad komai fa ɗan hakuri ne dan haka inaso ka kwantar da hankalin ka duk da nasan bakaso nace ka kwantar da hankalin naka amma ya zame mun dole na faɗa maka,idan baka kwantar da hankalinka ba bafa ta yanda zamuyi musamo bakin zaren,dole zaka maida komai ba komai bba a idon wayan da muke zargi sai ka iya takunka kafin kasamu abunda kake nema.

Ajiyar zuciya ya sauke mai karfi ya kalli Faisal da rinannun idanun sa da suka ƙanƙace suka canza kamannin su yace'ba zaka gane bane broo"zan gane mana Ahmad nasan irin ciwon da kakeji amma duk da haka hakurin nande shine,abunda hakuri be baka shi ba,rashin sa baze baka ba,sannu sannu bata hana zuwa saide a daɗe ba'azo ba dan haka ka tashi kayi wanka kafin nan bara na gyara maka ɗakin muje munemi abunda zamu saka cikin mu idan kazo ka kwanta ka nutsu zakafi jin daɗin yin tunani wani abun ko ɗan ƙanƙani ne musamu muriƙe ze taimaka mana wajen gano inda take"amma kafin wannan duka ko zamu je asibitin da kaine musake dubo jikin Alhajin?ya tambaye shi yana tsare shi da ido"No kaje kai kaɗan ka dan zuwanka da ni ze haifar da zargi kasan fuskana ba wani ɓoyayye bane awajen ire iren su Na Allah.

Gyaɗa kai Ahmad yayi cike da gamsuwa toilet yafaɗa ya sakarwa kansa ruwa mai sanyi yajima yana tsaye ruwa na sauka saman kansa tunanin sa be wuce wani hali Aeshow ɗinsa take ciki ba,me ta musu yarinya da batasan komai ba,yarinya da ba ruwan ta da shiga harka da bata shafeta ba.

Ya ilahil alamina ga baiwarka nan karka bawa duk wani mai hannu da ɓatanta kwanciyar hankali data ruhi baki ɗaya ya rabbi karka bawa kowa dama dazasu cutar da ita,haka yayi ta addu'oi harma ya manta a inda yake saida Faisal dake cikin ɗakim yaji shirun yayi yawa almost 1 hour yasashi buga masa ƙyauren bayin dan yanajin saukan ruwa amma bayajin motsin mutum buga ƙofan da Faisal yayi ne yadawo dashi daga duniyar tunanin daya lula gyaran murya yayi yana mai kai hannun sa ya kashe shower yafito ɗaure da towel a ƙugun sa,shap shap ya shirya kansa ya fito zuwa falo da kallo Faisal din yabisa dan yasan ba abune mai sauki ke saka Ahmad damuwar sa tafito fili ba.
"Muje kawai yace dashi yana mai zeran key din sa yayi waje Faisal na biye dashi a baya.

Daidai sannan kuma Fauza da wasu ƙawayen ta suka fito daga cikin gida suka nufi parki lot da alama rakasu tayi ganin Ahmad din yasata canza akalan tafiyan ta zuwa wajen da Ahmad yake tsaye da Faisal suna ƙara tattauna yanda zasuyi da mai gadi Malam Barau batare daya basu matsala ba,tunda sun rigada sun ƙarɓi lambayar wayan sa dama wanda sukai kiran sa baki ɗaya kuma yatura ma Mansur lambar yamasa ayi masa traking fuska a washe tazo inda suke tsayen sai wani yauƙi take ganinta yasaka suyin shiru da barin maganan da suke,kallo ɗaya Ahmad yayi mata ya dauke kansa dan wasu kayane dasuka kamata sosai suke nuna komai na jikin ta,kannan nata yasha ƙitso kalaba anyi mata ƙari yazubo a gadon bayan ta,sai takalmi both irin ta samarin nan ne a ƙafarta"Hi tace da isarta inda suke da "Hi shima Faisal ya maida mata idonta ƙyam akan Ahmad dayaƙi kallon ta take"Dear A ni nayi fushi da kai yau birthday ɗina guda amma ko wishing ɗina bakayi ba.

Ta ƙare maganan cike da shagwaɓa irin ta sangartattun yara,zungurin sa Faisal yayi sannan ya ɗan waigo ta gefen ido ya kalle yace"oh ashe birthday kikayi yau?yayi kyau kice girma yaxo miki amma har yanzu hankalin ki sai a slow,shagwaɓe fuska tayi jin abunda yace mata suko ƙawayenta sai kallom su suke cike da sha'awa dan ba karamin burgesu Ahmad ɗin yayi ba,ko wacce daga cikin su burin ta be wuce ace Ahmad ɗin yasota ba,sun dauka hira suke dayake bajin abunda suke cewa sukeyi ba.

Hannu ta miƙa masa tana cewa"kyauta na zaka bani ko kuma yau ɗaya ka sadaukar mun da lokacin ka koda awa uku ne cikin lokacin ka na yau.

"Wani kallo ya watsa mata na ashe ke baki da hankali,suko ƙawayen ta gani suke kaman kallon soyayya Ahmad din ke binta da shi"ina da abunyi ko zaki bamu waje"nide dan Allah tace tana bubbuga kafa a ƙasa"ba yau ba"sai yaushe tasake jifa masa da tambaya cike da ƙosawa da magana yace"ba yau ba ba  gobe ba,maybe next time yana cewa haka yabude motan sa yashiga Faisal shima yashiga yaja motan suka fita a gidan daidai bakin get yama Malam Barau mai gadi alama da idanuna yana kanka muƙut ya haɗiye wani abu cike da tsoro.

Suna fita Faisal yace"ita wannan din wacece?"ɗiyar Na Allah ce wai a haka mahaifinta bashi da lafiya amma ita ko ajikinta shiyasa wani lokaci iyaye suke yin kuskure wajen bawa yara tarbiya yanzu dubeta sai kace bayahudiya sai wani karya murya take ita adole zata burgeni mtssss"Allah ya kyauta kawai Faisal ya iya cewa.

Hajia balki zaune take cikin katafaren falon ta daya sha kayan alatu gefenta Hajia mariya ce zaune da wasu cikin ƙawayen su"nifa ina ganin harkan nan tafi kawo ransom ko shi zamu komayi ne kalli Hajia Asma'u zuwanta ɗaya harta tayi fice tazama big madam zata iya gogawa da kowa.

"Hmmm Hajia balki kenan ke samun kawai kike kallo bakya ganin hatsarin da ka iya biyowa idan aka kama mutum da wannan abun kanshi za fille a ƙasar saudiya.

Duka suka amsa da fille kai kuma suna zaro idanuwan su waje"kwarai kuwa nide abar wannan batun a kamo wata kingannin nan harka duk da zata kasance da rasa rayuwa bana cikin ta duk samun ta,cewar Hajia lantana.

"Nikike ma rashin kunya ko to wallahi yau sai nayi ɗaiɗai da rayuwarki.

"Innalillahi tashiga faɗi da karfi"dan Allah sangami au dan Allah bawan Allah kayi hakuri kamun rai wallahi matar aurece ni karka taɓamun mutuncina dan Allah"kima dena roƙona dan ba barin zanyi ba,tunda matar aurece ke kinga ba wanda ze gane harma shi kansa oga dan nasan koshi ba kyaleki zeyi ba,kawai ya ɗaga miki ƙafane.

Afka mata yayi suka shiga kiciniya ita tana kiciniyar ƙwatan kanta yayinda shi kuma yake ƙoƙarin ganin sai ya kaita ƙasa,karfi mace kuma yarinya mai karancin shekaru irin Aisha ba daya bane da wannan dargagegen ƙaton basamuden mutumin ba,ko namiji ne dan uwansa sai yaji tsoron haɗa ƙirji dashi balle kuma mace irin Aisha lange lange.

"Allahumma ajirni fi musibati tashiga karantawa da karfi ganin fa da gaske neman ƙeta mata haddi yake tashiga kiran sunan Allah tana cewa Ya Allah ga bawanka nan karka bashi iko akaina ya Allah ina da yaƙinin zaka ƙuɓutar dani daga sharrin sa ya Rabbi ka kawo mun dauki.

Idon a ritse take kaima Allah kukan ta jikinta sai ɓari yakeyi hatta da laɓɓenta rawa suke saboda tsaban tsorata da tayi hawaye ma rahmane da hawayen ta kafewa yayi sai wani irin dauyi da ƙirjinta yayi mata,jinsa shiru be taɓa taba sama wani irin gurnani da takeji a gefenta haka yasata buɗe idonta bata sauke su ako inaba sai saman kyakkyawan fuskan sa,mai cike da haiba maida idonta gefe tayi sai ko taga wannan ƙaton sheme a ƙasa ai vatasan sanda ta mike ta rungume shi tasaki kuka ba...

ALLAH YASA MUDACE

AUREN WUCIN GADI 2Where stories live. Discover now