p-11

3 0 0
                                    

_*🍇SILAR AURENA🍇*_

TAKU NA 1
Book 1📖

*NA*
Rabiatu Bashir Abdullahi
*_UMMU MAHER(MRS GREEN)_*🍃

_*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*_

*KOYON MAYAFI DA HULUNA DA RIBOM*
Kiyi shiga wannan grp ɗin domin dogaro da kai.👇👇👇👇👇👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/D6g00p1DxttAtHH1vmh54i

*_KARANTA SILAR AURENA TA AREWABOOKS HANKALI ƘWANCE👇🏽_*
https://arewabooks.com/book?id=65bd172f88cb015808e5fc25

*_KARANTA SILAR AURENA TA WATTPAD HANKALI ƘWANCE_👇🏽*
https://www.wattpad.com/1420716493?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rabiatu333

SHAFI NA 11
________________Andi tayi saurin kallonta, kasan cewarta mace me haƙuri sai ta gyaɗa kanta kawai ba tare da ta ce mata komi ba.

Alti ƙanwarta tayi ƙwafa kasan cewarta macece me matuƙar zafi ta ce" yo ai gwara mu da daman kurciya akayi masa su o'o fa? yawon banza ne fa aka tafi babu alamun dawowa kuma to har ayi mana wani batu".
Tuni ɗakin ya fara rikicewa, masu goyon bayan Alti na yi masu goyon bayan uwar gida na yi, ita kuwa Andi dakawa ƙanwarta tsawa tayi cike da jin haushi ta ce" haba Alti menene haka kuma? dukkaninmu fa muna da hankali da tunani, bai kamata fa mu zama jahilai ba zaman makoki mukeyi ba zaman faɗa ko gaba ba".

haba wannan maganar da ta faɗa sai ta ƙara rura wutar masifa, har sai dai Andi taja ƙanwarta suka wuce ɓangarensu.

Safna tayi ƙwafa ta wuce, gamida murguɗa bakinta ta ce" uhm ai ni dai babu abinda zance sai dai mu yiwa Allah godiya, kuma sannan ƴan baƙin ciki ai sai dai su mutu".
wannan maganar da ta faɗa sai Hajiya Nanne ta fara kuka wato uwar gida, tana kiran wayar Alhaji wai ƴar tatsiyar yarinyar nan Safnah ta samu bakin yi mata rashin kunya.
Alhaji kuwa bai ma san tana kiransa ba, yana can shima cike da alhinin abinda yake ganewa idonsa na dawowar ɗansa ɗaya tilo namiji, abin tinƙahonsa kuma abin sonsa tabbas Allah ne ya amshi roƙon da suka daɗe sunayi.

Hajiya Nanne ta janyo mama Amarya kusa da ita, ta ce" haba Shukra wannan kuma wani irin rashin mutunci ne? ta yaya zaki munafurce ni? ban kin faɗamin boka ya ce ba zai taɓa waiwayar gida ba? sai kuma gashi ya dawo yanzu? to me zan kira da hakan? cin amana ko me"?.

wata dariyar ciki tayi, tana ɓoye fuskarta don ma suna daga can ƙarshen babban falon ne ba lallai a jita ba, ta ce" ni fa duk abinda zanyi bana zurfafa mugunta ni na rasa me yasa kika tsani yaron nan haka, ni dai wallahi na yarda makamai na ahalin yanzu saboda wa'azin dana ke ji ba abanza nake jinsa ba, ance duk mutumin da yake zuwa wajen boka ba za'a amshi sallarsa har ta ƙwana arba'in, to ina dalili? da zan ɓata waɗannan sallolin nawa"?.

cike da masifa ta ce" oh to ina kuɗina dana baki ki kaiwa bokan"?.

da sauri ta ce" indai kuɗinki ne yana ɗaki, ni daman ban ma je wajen bokan ba saboda haka zan baki kuɗinki an jima, saboda haka ni na koma ɓangarena Allah ya bamu alheri, dama ance zaman makoki duk munafurci ne , ni da za'a gane ma da an daina sa da masu asiri da kuma masu munafurci duk ba a rasasu agidan zaman makoki".
Sosai maganar ta tunzura Hajiya Nanne ta hau faɗa, ai kuwa sai aka hau mata dariya ana nuna ta, matan wanda ya rasu su uku ɗaya ce kawai ta bata ƙwarin gwiwa akan cewa ta cigaba dayi ai ita aka ɓatawa.

bayan an gama karɓar gaisuwa ya shigo gidansu, duk jikinsa asanyaye ya rasa ma da wani irin ido zai dubi Andi da kuma Jadda kakarsa?.

ɓangaren Jadda ya fara shiga, shi da Saminu ƙaninsa ɗan gidan ƙanin babansa wanda ya rasu.
Tun daga nesa ta ƙura masa ido, daya zo gab da ita kuma sai ta juya tamkar ma bata gansa ba saboda tana son nuna masa kuskurensa ne.
babban falo ne, falon an tsarasa kamar ɗakin amaryar da aka kawo yau falon yasha kayan alatu masu matuƙar kyau, fentin kuma irin wanda akeyi agidan sarakai ne irinsa ne a falonta sai haske yake yana walƙiya, ga kujerunta na alfarma masu kyau da tsada kujerun kusan guda goma a falon.

SILAR AURE NAWhere stories live. Discover now