p-8

8 1 0
                                    

_*🍇SILAR AURENA🍇*_
         
TAKU NA 1
Book 1📖

*NA*
Rabiatu Bashir Abdullahi
*_UMMU MAHER(MRS GREEN)_*🍃

_*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*_

*KOYON MAYAFI DA HULUNA DA RIBOM*
Ki shiga wannan grp ɗin domin dogaro da kai.👇🏽    https://chat.whatsapp.com/FHgAO8onZ0LHIRTHPG2qY4

*_KARANTA SILAR AURENA TA AREWABOOKS HANKALI ƘWANCE👇🏽_*
https://arewabooks.com/book?id=65bd172f88cb015808e5fc25

*_KARANTA SILAR AURENA TA WATTPAD HANKALI ƘWANCE👇🏽_*
https://www.wattpad.com/1420716493?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rabiatu333

SHAFI NA 8
________________da sauri ya kalli maryam, yana mata kallon baki kyautamin ba sannan ya juya zuwa ga ya umar, wanda shi kuma tuni ya fuskanci kallon da ya yiwa maryam ɗin, abin ya basa mamaki sannan ya gitgiza sa yanzu daman Maryam da gaske ne tana cikin wannan mummunan yanayin kenan? indai kuwa haka ne yasan ta inda zai ɓillo mata.

Sulaiman ya ce"a'a ya Umar kawai dai haryanzu Baba hari bata gama gane halin maryam bane, amman in sha Allahu nan gaba komi ze yi dai dai".

   Ya umar ya ce" haba Sulaiman? kunsan da haka kuma kuka yi shiru da bakinku? duk da mahaifiyarka ce amma yana da kyau asamu wani babba ya takawa abin burki, ta yadda zakuyi rayuwarku cikin aminci da kuma farantawa juna, amman zama hakan ba zai haifar daɗa me ido ba".

  shiru mukayi mu dukanmu, kowa da tunanin da yake sai Halima ta ce" gaskiya ne ya Umar, ka faɗi gaskiya sai dai wanda za'a samo ya yi wannan aikin shi ne babnan abu, don wallahi Baba hari bata tsoron kowa daga cikin danginta ko na babanmu, sai dai yayyinta dake can ƙauyen sokoto ina ganin su zasu iya yiwa tufkar hanci".
Ya Umar ya ce" to ai abune na zamani yanzu sai asamu waya akirasu azo a gyara abun, idan ma ita Maryam ɗince take wa Babar taka wani abun sai asan yadda za'a sasanta lamarin".

Sulaiman yayi na'am, sai dai yasan halin Baba hari ba barinsa za tayi ba masifa da mita ma kaɗai ya ishesa don cewa za tayi maryam ɗince ma ta zuga ta daga bisani kuma abij ya dawo jan maryam ɗin.

  Nima dai atawa zuciyar banji daɗin abinda ya Umar ɗin ya faɗa ba domin nasan wata ran abin zai dawo kaina ne daga bisani ma ta ce nice na zugasa, don ba yun yau baba hari ta saba yimin hakan ba.

   ya umar yana tafiya Sulaiman ya matso kusa da ni, ya harari Halima sannan ya ce" munafuka ke kika faɗa masa ko? yanxun miye amfanin faɗa masa ɗin? kin san daj halin Baba babu wanda baki sani ba, kada muzo muyi wannan taɓargazar abin ya dawo kan maryam, alhali ma ita bata san lokacin da muka yanke hukunci ba".

Halima ta ce" yaya ba fa za'a zubawa Baba tana baƙantawa ƴar mutane rai ba, yanzu mu idan mukayi aure akayi mana haka za taji daɗi? ko kuma kai zakaji daɗi? to rashin jini ai rashin ba'a tsaga ba, saboda haka yaya Sulaiman atashi tsaye kan wannan matsalar idan ba haka ba za'a samu matsala babba nan gaba".

  Sulaiman ya ce" hakane Halima, amman kada ki manta Baba mahaifiyarmu ce duk abinda zamuyi mu dinga sara muna duban bakin gatari ne, idan ba haka ba zamu janyowa kanmu matsala me girma idan tayi fushi damu".

  "to ai yaya ita Baba fa ko baka yi mata komi ba yi maka banbami take, abu ɗan kaɗan sai faɗa da hayaniya? kana ganinka fa matarka ce ta haihu fa? amman Baba ko awaya batayi barka ba, ai kasan tsana tayi tsana ace mutum ya haihi ya wuce siraɗin haihuwa na mutuwa ko rayuwa amman ta kasa zuwa? itama fa ta ɗanɗana haihuwar nan har guda goma, don dai Allah bai bar mata biyar bane amman yanzu da tana da yara har goma".

  Ni dai ina jinsu, amman ban iya ce wa komi saboda yadda jikina yake min ciwo, tamkar in ƙwalla ƙara ga kuma wani irin barci dana ke ji ga kuma haushin halin Baba hari dana ke ji, domin abin ya bani haushi sosai ace mutum ya haihu don ka tsanesa kuma ka kasa zuwa? babu zuwa babu ɗan aike?.

Sulaiman ya ɗauki yaran yana musu kiran sallah da kuma raɗa musu suna.

  ganin har ya gama yi musu kiran sallar da raɗin sunan bai ce min komi ba yasa na ce" har ka gama ne? sai kace me raɗa suna ɗari?".

ya ɗan murmusa sannan ya ce" ai gwara in daɗe inyi musu addu'ar baki saboda kyaunki da suka ɗakko kamanni ne kawai nawa".
Na murmusa sannan na ce" kyawuna kuma? to ai kace bamuyi kama ba ko dai kyaunka suka ɗakko ne"?.
  Halima na kallonmu muna bata sha'awa, ba don Allah yasa na samu miji nagari ba da abin yayi min yawa, ga babu miji nagari ga wahalar uwar miji.

  sai kuwa Halima ta ce" wai ni kuwa yaya wani suna aka sanyawa yaran"?.

  ya ɗan murmusa sannan ya ce" sunayen iyayena HARIRA da AMINU".

  Amatuƙar razane nake kallonsa, bama ni ba har dama Halimar da tayi tambayar ta razana da jin sunan, ba wai sunan Aminu ɗin bane abin haushi, sunan Baba hari da aka laƙabawa yarinyar ne ya baƙanta musu rai, har da Halima ƴar baba harin.

~~~~~~~~~~
Ibrahim ya gama shirinsa tsaf, kai tsaye shawarar zuwa wajen iyayensa yayi don tunda ya auri matarsa Hajara bai taɓa zuwa da niyyar gaishesu ba, shi dai yasan tunda ya aure ta sai yaji duk duniya ba shida maƙiya irinsu saboda sun tsani matar da yake so, gashi kuma ita wacce yake so ɗin ta wulaƙamtashi tana tallan jikinta atiktok, wannan baƙin cikin yaƙi fita daga zuciyarsa wai matarsa ta sunna tana tallan jikinta amedia, daga ita sai kayan barci wannan takaicin ya kasa fita daga zuciyarsa.

  Ko abinci bai ci ba ya gama haɗa dukkanin kayansa tsaf acikin aƙwati, ya kira direbansa awaya ya sanar masa ya shirya zai kaisa garin zaria.

  Sosai direban yayi mamaki, don yaga basu wani daɗe da ɗakkosa a airport ba, amman kuma yanzu zai yi tafiya zuwa Zaria? lallai Allah abin godiya ne daya karkato fa hankalinsa zuwa Garin  mahaifansa biyo bayan wasu shekaru kusan biyu da yayi ba tare daya haɗu dasu ba.
Domin shi direbansa yasan komi, kuma kafin ma yayi aure shi ne yake kaisa har zaria suyi ƙwana biyu uku har zuwa huɗu sannan su dawo.

sosai yayi kyau cikin wani yadi fari silk, yayi kyau sosai da yake ba fari ne can ba, za'a iya kirasa da wankan tarwaɗa sai dai yana da kyaunsa da kuma dogon hanci wanda yayi ɗos afuskarsa tamkar an zana, ga sajensa me masifar kyau da ƙwanciya tamkar na ƴan asalin indiya.
dogone sosai, kuma yana da ƴar ƙiba amman ƴar kaɗan ba dai shi da irin ramar nan.

  tun daga nesa mubarak ya matso da mota, ya ce" Allah ya taimaki oga dafatan ka fito lafiya"?.
ya ɗaga masa hannu kawai amman bai amsa ba, ba kuma haka halinsa yake ba kana dai ganinsa yau kasan aƙwai abinda yake azalzalar zuciyarsa, yin maganarsa dai dai yake da fallasa asirin zuciyarsa, shiyasa ma yayi shiru ba tare daya amsa ba.

  Suna tafiya Mubarak ya ce" oga duk da yau bakasan magana, to me zaisa ka hau jirgi zaka fi saurin zuwa zaria tunda dai ka daɗe bakaje ba"?.

  sai yanzu yayi magana, ya yinda ya ajje computer ɗinsa agefensa sannan ya ce"Mk ba zan iya hawa jirgi ba, ka manta sanda kake kaini zaria? aƙwai abubuwan da nake tunowa matuƙar muka biyo wannan hanyar, wanda bazan taɓa mantawa dashi ba shiyasa nake son mu biyo ta mota, sannan abu na biyu ina jin daɗi da kuna farin ciki idan ina ganin hanyar sai inji tamkar anyi kin wanka ne sa ruwan zam zam, saboda haka ka samu amsarka Mk".

Mk ya ce" wai shin oga me yasa ka daina zuwa gida tsawon shekara biyu"?...

  tambayar tazo masa abazata, ya haɗiye wani irin malulu sannan ya ce".................

Ko yaya iyayen AD zasuji idan suka ga ɗansu ƙwatsam yazj gare su? sai ashafi na gaba za kuji komi.
MRS GREEN CE🫵
SHARE
COMMENTS👏🏻

*MAMAN AMEER DILKA SOAP*

*muna siyar da kayan gyaran jiki, jikinki ya yi silɓi da kuma shining ki zama tauraruwa acikin mata*.

muna siyar da dilka
soap
mulato soap
white scrub
da dai sauran kayan gyaran  jiki har ma dana ƙamshi kamar👉🏽

Gab gab
Layal
Hawi
Cus cus
Coucounot sandal,
Marshoosh,
Frami
Kajiji,
Sandal.flask
Qalbul oud,
Noor hayaty,
Kindikaye,
Sultana,
Kajiji,
Sandal asly
Malika
Night queen
Misk humra,
White humra
Dufur khumura,
Khumura mukabassiya.

ga lambar wayata, don siyan ɗaya ko sari MAMAN AMIR GIDAN GYARA ƘAMSHI.
0806614 9923

SILAR AURE NAWhere stories live. Discover now