“Fada masa kika yi? Ni fa bance ya kwashe kudin aikinsa ya kawo min ba, kar ya zo yana kuka da ni, kuma ban ce yayi sata ya ba ni ba, duk abun da zai biyo baya kar ya saka sunana a ciki”

Na yi shiru na rasa me zan ce, ban san taya zan kare Zafeer ba, haka kuma ban zan iya fitowa na fadi gasjiyar cewar kudin adashen Mama ne ba, kamar yadda kalaman Baba basa min dadi a yanzu.

“Wai ance ana kiran in ji Zafeerrr”

Almajirin da aka aiko ya fada bayan yayi sallama. Na kalli kofar Baba ma ya kalli kofar a daidai lokacin da Mama ta fito daga dakinta tana kallon ledar dake gaban Baba

“Je ka ce tana zuwa”

Mama ta fada, sai Baba ya mike tsaye.

“Bari na fara magana da shi daman ina nemansa”

Kan kace kwabo Baba ya mike tsaye ya fice daga gidan, ban ji komai a raina ba domin na san duk tsanani Zafeer ba zai tona min asiri ba ko da kuwa be san me na shirya ba ba zai taba fadar abun da zai haifar min da matsala ba. Bayan fitar Baba Mama ta dube ni ta ce.

“Fada masa kika yi Baban ki yace be bashi komai ba?”

Na sauke kaina kasa kamar ba ni ba, cikin na tsananin ladabi da ban san ta ina yake fito min ba na ce.

“Aa Wallahi ban fada masa ba, kawai dai kila anyi dace da yayi niyar aikata hakan ne”

“Amman wannan ledar tun dazun kika shigo da ita”

“Eh shi ya bani, acan ya siya komai sai ya ba ni tare da kudin”

“Allah yasa gaskiya kika fada, domin idan na gano rokon bawan Allah nan kika yi kudi saboda ki bawa Babanki sai na miki mugun duka a gidan nan”

A take cikina yayi kuka ba irin kukan yunwa ko wahala ba, kukan tsoron shan duka da na san idan Mama ta gane a gurin adashenta na karbo kudin nan sai ta fi cin ubana ma fiye da roko”

Ta dauke ledodin ta shige ciki ni kuma na juya na koma dakinmu ina ta tunanin matafitar da ban yi tunaninta ba tun farko. Bayan kamar minti talatin Baba ya dawo cikin gidan ya yana kwala min kira.

“Noor”

“Na'am”

Na amsa da sauri sannan na mike tsaye na fito.

“Tafi yana jiranki”

Na juya na koma cikin gidan ina jin faduwar gaban da ban saba ji ba, kuma ban san na Miye ba. Hijab dina na dauko na saka zuciyata bata raya min ransa zai bace idan na ba shi abun da na zo masa da shi daga gurin Kareem ba, kwalkwalwa ta mantar da ni gargadi da yayi min har sai da na fita rike da leda na tsaya a gabansa ina kallon yadda yanayinsa ya canja ba kamar yadda na saba ganinsa ba.

“Zafeer”

Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalleni.

“Noor Baby Noor”

Yanayin yadda ya kira ni ma muryarsa ta sauya, ina karantar damuwar dake tattare da shi tun kamin ya fada min.

“Baba ya maka wata magana marar dadi?”

“Mai dadi ce amman dacin mai daci ne a gareni yanzu”

“Me yace maka?”

Ya kalleni.

“Baku yi magana da shi ba?”

“Magana daya ce kawai? Ni dai ka fada min”

Na masa magana a shagwabe kamar zan masa kuka.

“Baba ya min godiya, me kika bashi?”

“Kyauta da kudi dubu goma na ce masa kai ne ka ce bashi”

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now