page 6

7 0 0
                                    

_*🍇SILAR AURENA🍇*_
         
TAKU NA 1
Book 1📖

*NA*
Rabiatu Bashir Abdullahi
*_UMMU MAHER(MRS GREEN)_*🍃

_*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*_

*UMMU MAHER COLLECTION👜👜*
_Domin siyan kaya masu sauƙi da rahusa danna wannan link ɗin na ƙasa_👇🏽
https://chat.whatsapp.com/C3tsX4CqiEp939DhYvJ3SZ

*_KARANTA SILAR AURENA TA AREWABOOKS HANKALI ƘWANCE👇🏽_*
https://arewabooks.com/book?id=65bd172f88cb015808e5fc25

*_KARANTA SILAR AURENA TA WATTPAD HANKALI ƘWANCE_👇🏽*
https://www.wattpad.com/1420716493?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rabiatu333

SHAFI NA 6

______________sai kusan magriba na farka, daga nannauyan barcin daya ƙwasheni sosai naji wani iri ajikina, tamkar anyi min yasa na fara shafa cikina ya yinda wata likita take kusa dani, ta matso kusa dani tana ce wa" madam kina buƙatar wani abu ne"?.
  da sauri na shafa cikina, sai naji zafi zafi ta ƙaraso da sauri tana ce wa" yi haƙuri tiyata akayi miki ne, yaranki kuma suna waje danginki suna ganinsu, bari in kira likita yanzu sai ya duba ki".

  tana fitowa Sulaiman ya taso da sauri sannan ya ce" likita ta tashi ne"?.

ta ce" eh ta tashi bari in kira muku likitan sai ya duba ta ko"?.

Murna da son ganin matarsa suka haɗu suka cika masa zuciya, Allah ya sani yana tsananin son matarsa mero, sai dai mahaifiyarsa ce ta ƙeƙashe ƙasa ta tsaya atsakiyarsu taƙi ta barsu su mori rayuwarsu.

sai kallon yaransa yake yana me cike da farin ciki, har likita ya shiga ya duba ta sannan ya fito ya basu ixinin shiga, ai kuwa da sauri suka shige su dukansu ya Umar ne ma yaji kunyarsu ya tsaya abaya baya.
yana shigowa ta kallesa gamida sunkuyar da kanta irin na asalin fulani wai kunya, shi kuwa ko ajikinsa jin matarsa yake tamkar yau ya aure ta sabo da so da ƙaunarta, sai sunne kanta takr shi kuwa yana zuwa ya ajje mata macen akan cinyarta, cike da xolayarta ya ce"maman twins sannu da fama dafatan basu gajiyar dake ba ko"?.

ta ɗanyi murmushi sannan ta ce" ni fa bani ce babarsu ba". ya dara sannan ya ce" ok to wacece ɗin"?. sai tayi sauri ta nuna Halima ƙanwar Sulaiman.  da sauri Haliman ta nuna kanta tana ce wa" kamar kunsan kuwa ina son ƴan biyu kyautar Allah, Allah dai rayasa mana su".

Sai lokacin ta lura da ya     Umar, wanda ya amsawa Halima addu'arta sannan ya ce" oh yau naga rashin kunya, yanzu Maryam baki ma san ina wajen ba? shi ne kika wani ɓoye fuska daga ganina"?.
Tuni kunya ta kamani na ce" to ya Umar ba shi bane yake tsokanata, kuma alhali ni ba ni ce na haifesu ba, ina tashi fa daga barci na gansu". na faɗi hakan ina me ɓoye fuskata don har ga Allah kunya nake ji sosai har dama yaran nawa duk kunyarsu nake ji abinka da ba fulatana.
ya Umar ya ce" ah lallai kice dasu zan koma, sai in kaiwa Habiba duk ta haɗa dasu Sadik".
ko ƙala bance ba, ni dai kunya kawai nake ji ana cikin hakan likita ta shigo  ta ce" yauwa idan kun ganta zaku iya barinta haka saboda anason ta samu isasshen hutu sosai, sannan inason mijinta ya biyono ofis ɗina".
Dukkanmu kallonta muke,musamman ma ni da gabana yake faɗuwa don bansan abinda zata faɗa masa ɗin ba.

  Ya umar ya ce" to ni yanzu ma zan huce Maryam, tunda naga ai jikin naki ya yi sauƙi dama inada aikin da zanje yi sokoto gobe".
Sai ya ciro kuɗaɗe a aljihunsa kusan dubu ashirin ya ajjemin su agefe na, sannan ya ce" to ni na tafi Maryam in sha Allah kafin suna Habiba zata zo, ko ƙwana uku sai tayi miki su sadik su tafi gidan Innarmu".

sosai naji wani irin abu me kama da dukan mashi acikin ƙahon zuciyata, tabbas ina tsananin tausayin kaina yanzu ace saboda ba kada shi iyayenka basa ko neman ka? musamman ma Innah, sam bata nema na ko awaya ne kuwa nasha aron wayar Sulaiman in kirata, amman idan ta ɗaga taji muryata sai ta katse wayar, gamida yin tsaki duk a SILAR AURENA da talaka tayi min hakan amatsayinta na uwa, saboda ban auri me kuɗi ba kamar dai yadda sauran ƴan uwana sukayi.

SILAR AURE NAWhere stories live. Discover now