Wani irin dariyar rainin hankali hidayat ta saki kan ta juya manyan idanunta tana kallon gidan tace

"Gida fa kace? Ai ni ban ga gida ba banda kasungumin daji me cike da namun dabba masu hatsari da ban tsoro, jikin hidayat kuwa daga kwana bakwai baya ka datse duk wani alakarka da ita, datsewa ta har Abada kuwa... Ashe se yau ka san Aisha ƴar ka ce? To kaji da kyau Aisha da Muhammad Raed ƴaƴan hidayat shine sunansu, basu san wanene yusuf ba kuma ba za su san shi ba. har Abada sunansu ya tashi daga Aisha Yusuf zuwa Aisha hidayat Abubakar, ni nice uban su kuma ni ce uwar su don haka ka kiyaye alakanta kanka dasu"

Gabaɗaya idanunshi a waje suke yana mamakin wannan sabuwar hidayat da be taɓa gani ba, kwarjininta da yadda take kallon shi cikin idanu babu tsoro se ma hango wani wutar bala'i dake tashi a cikin idanunta yasa yaji wani sanyi sanyi na kokarin lulluɓe shi.

Cikin karfin hali yace
"kin san a yau na sake ki zan iya auren mata huɗu rus? Kuma a yau na sake ki baki da wurin zuwa so dole ki dawo nan ɗin ki tsuguna a gabana ki roki gafara a lokacin kuma ina ga lokaci ya riga ya kure miki..."

Hannunta ta harɗe tace
"babu macen da zata iya zama Da Mugun Miji irin ka Yusuf idan ba hidayat ba har Abada ba'a yi macen da zata iya shigowa wannan kurkukun kaddarar ba, kuma ka ji da kyau idan har na saka kafafuna na fita daga gidan nan wallahi wallahi ko mutuwa zan yi a waje na gama taka harabar gidan nan kenan  gwara in mutu da in sake alakanta kaina da kai... Azzalumi, Fasiki, makashi..."

Tayi maganan hawaye na gangaro mata sede fa ba shi ya nuna gazawarta ba, hawayen na wutar bala'in dake cin ƙasar zuciyarta ne..

"Ni kike kira da waennan sunayen? Kije na sake ki saki BIYU"

Wani dariya tayi tare da haɗe hannunta ya bada sautin clap tace
"tafi nono fari, ko baka sakeni ba dama bani da ra'ayin ci gaba da zama da kai.."

Har ya fara tafiya tace
"Baka ji ba!"

Waiwayowa yayi tana murmushi tace
"Karka yi tunanin Idan hidayat ta tafi ta tafi kenan fa, Hidayat zata dawo idan har ta Rayu zata dawo ta zama WUTAR DAJIN da babu zato babu tsammani se de kawai a ganta ta mamaye dajin, se ta tabbatar ta yagalgala rayuwarka ta yadda baka yi zato ba, nayi alkawari ni hidayat daga yau a gareka kadangariyar bakin tulu ce a bar ni na ɓata ruwa a tabani kuwa a fashe tulun... Daga rana irin ta yau jinin Usman ba ze barka ba har se ka je inda ka tura shi....
Kuskurenka ɗaya Yusuf! Shine na taɓa wutsiyar damisar dake bacci cikin yunwar kwana da kwanaki.. Ka ga ko me kwatarka se Allah.."

Gabanshi ta karaso ta Haɗa yatsunta biyu suka bada wani sautin ɗas har sau uku kan tace
"put this at the back of your thick lunatic skull!! Zan dawo.. Hidayat zata dawo"

Tana kai nan ta juya ta ɗauki junior tare da kama hannun Aisha suka shige ɗaki, sabbin kayansu na suna ta fitar musu tare da shirya su a wani jaka ta Haɗa na Junior ma daban, wani Waist bag wadda daga gani ya ji jiki ta dauka ta ɗaura a kwankwasonta kan ta goya junior ta dauki hijab ta sakawa Aisha ta dauki nata ta saka suka fito..

Tunda ta kama tafiya ko waiwayen gidan bata sake ba, tana fita kuwa taji wani sabon iskar ƴanci ya lulluɓe ta, tafiyar kafa suka yi sossai in Aisha ta gaji su huta, ruwa kuwa in sun ga masallaci se su je randar wurin su sha.

Dab magrib suka isa gidan Abba, tana da yakinin baza su karɓe ta ba sede bata da wurin zuwa da ya wuce nan, bata da ko sisi a jikinta.

Da sallama ta shiga parlorn ganin umma da Surayya tayi zaune suna kallo Dukda chanje chanje da ta gani na ja baya a garesu hakan be hana ta duƙawa ba tace
"Umma ina yini?"

Wani taɓe baki umma dake aika mata da kallon uku saura kwata tayi tace
"da ban wuni ba kya ganni?"

Tayi maganan tana dauke kai, Surraya ta maka mata harara don har yau takaicin dukan da taci take yi tace
"me ya kawoki wurin mu? Ina da kafafunki kika je police station kika sa suka mana tsakani? Me kika zo nema yanzu kuma"

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now