14

143 6 0
                                    

*GASHIN ƘUMA*


Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 14.

Washe gari ranar ɗaurin aure, gida ya cika da mutane duk ba ba ayi gayya ba amma makota sunyi mana kara sun cika mana gida, kamshin girki ne ke tashi da ya kusa dahuwa. Ni kuma ina tare da kawayena a dakin kaka dasu Hafsa, Indo ma ba a barta a baya ba saboda tunda taji angona yana da kumbar susa ta tsaya ayi hidimar da ita, hira muke yi Hafsa tana yi mini daurin dankwali, fuskata kuwa tasha kwalliyar zamani da Indo tayi mini, sabuwar atamfar ciganvy na saka wanda Inna Amina ta dinka mini, sosai kyawuna ya fito kamar ba ni ba. Kaka ce ta shigo dakin tana rike da karamar trolley sabo ta dire shi a gaba tana cewa.

Gashi yanzu aka aiko da shi daga gidan angonki wai kayanki ne da zaki amfani dasu a yinin yau. Saiki cire na jikinki ki saka wanda suka kawo wannan sai ki maidata anjima in za a kaiki.

To nace sai ta fita Hafsa ta tsuguna ta bude akwatin, kaya kala biyu ne wani tsadadden leshi da kuma atamfa mai shegen kyau, duka dinkin riga da siket ne, sai undies da kuma gyale tare da takalmi da jaka, dan kunne da sarka har da abin hannu tare da turare guda daya, nan fa kawayena wanda muke yin tallar awara suka saki shewa da guɗa, ni dai ba baka sai kunne dariya kawai nake yi cike da tsantsar murnar da bazai misaltu ba, haka na shige uwar ɗakan kaka na saka leshin mai ruwan zuma da duwatsu farare, dinkin kamar an gwadani dan yayi ɗas a jikina tsayin siket ɗin ne dai yaso yi mini yawa, sai da na daga shi ta sama, na fito hafsa ta yi mini dauri da dan kwalin, na yafa farin gyale, Indo ta feshe ni da turare na saka takalimi na rike jaka nan fa na fito amarya sak, suka dinga yin guda suna koɗani ni dai yage baki kawai nake yi dan murna, haka na fito tsakar gida jama'a suka dinga guda suna masha Allah, Hafsa ta karɓi wayar Inna Amina da yake touch ce ta fara kashe mini hoto suma su Indo masu wayar zamani suka shiga ɗaukata, Umma da kaka kuwa murnan dana gani a idonsu ya wuce misali, a lokacin ne ake cewa mutane sun hallara har dangin ango sun zo ɗaurin aure, dama ƙarfe sha dayan safe aka saka kuma ba ɓata lokaci aka soma gabatar da daurin auren dan muna jin komai daga cikin gida saboda an saka loudspeaker, tuni na shige dakin kaka muka natsu muna saurare. A wannan lokacin ba zan iya misalta yadda nake ji a jikina ba dan har rawa yake yi saboda wani bakon lamari daya ziyarce ni, naji mutuwar jiki ga kuma ɗan fargaba haka, ashe dai aure abu ne mai girma domin da na ɗauka kamar wasa ne, sai da naji ance an daura aurena da Bilal bisa sadaki dubu hamain yasa na fashe da kuka domin tabbas nasan wani abu ya tsirga mini a zuciyata na damuwar rabuwa da gida, duk da gashin ƙumar da suke gana mini amma na fara jin kewar rabuwa dasu. Nan fa kawaye suka shiga guda suna tayani murna ni dai da ido nake binsu ina share kwallar dake bin kuncina, Hafsa ce ta dafa ni tana cewa.

Haba ƙanwata ke da zaki yi murna meye abin kuka, kefa yanzu kin samu 'yancin kai ne kin mallaki gidanki na kanki babu wanda ya isa ya takuraki sai abinda kike so zaki aiwatar. Dan haka ki daina wannan kukan ki nuna farin cikin ki kodan ki bawa makiya kunya.

Tabbas maganganunta sunyi tasiri a zuciyata dan nan take na nima hawaye na rasa, sai dai damuwar rabuwa dasu yana manne a zuciyata, nan na saki muka cigaba da hidimarmu. Shigowar ango da abokansa shine ya kara hargistsa hayaniyar gidan, sun shigo su gaida iyaye mata, a tsakiyar gida suka rusuna suna gaidasu Umma, kaka sai shi musu da albarka take yi ni dai ina daki kawayena dasu hafsa suka leka suna kallonsu, ina jin Indo tana tambayar Hafsa waye angon Hafsat ta nuna musu shi da hannu, nan fa kawayena suka dawo ciki suna yi mini sambarka wai angon nawa kyakkyawa gashi fari kalar masu kudi, murmushi kawai nayi ina binsu da ido. Bayan su Bilal sun fita Hafsat ta bisu a baya da Indo har kofar gida, ba jimawa sai ga Hafsa ta dawo tace na fito zan gaisa dasu, a kunyace na biyo bayanta ina rufe fuskata da gyale, muna zuwa kofar gisan na tsaya daga dan nesu dasu Bilal dai ido ya zuba mini sai murmushi yake ina kallonsa ta cikin farin gyalena, a kunyace na gaishesu suka amsa suna yi mini fatan alkhairi ban iya amsawa a fili ba sai a cikin zuciyata, ina kallon Indo sai fi'ili take tana zuba surutu da daya daga cikin abokan Bilal, ni sai tama bani kunya yadda take zuba duk nasan da biyu take yi domin ta samu wanda zai shinshina yace yana so, haka suka matsa mini dole na bude fuskata aka shiga daukarmu hoto nida Bilal sai da duka yi mai isarsu kafin nace zan shiga gida nayi musu sallama, ba jimawa su hafsat da indo suka shigo, anan ne aka fara wandaƙa da abinci kowa sai karakaina yake da kwano, ni koda aka kawo mana kasa ci nayi saboda damuwar da nake ciki na barin gida. Ashe su Bilal sun zo da lafiyayyen abinci sun raba a waje, shi hafsat ta bani tace naci akwai dadi dan harda naman kaza a ciki, Abas ne ya bata guda uku ita da Indo. Ban iya ci ba na bar mata kayanta duk da ina kwadayin cin kazar saboda an dade ba a gamu ba. Dan ko da babbar sallar da aka yi munci naman rago ne amma ba mu samu na kaza ba. 

GASHIN ƘUMAWhere stories live. Discover now