Mun koma Gesse ba jimawa gida irin ginin zamani mai kyau,nan fa na shiga tsaftace shi da kyau yanda ya kamata, nan da nan waje ya hau ɗaukan ido, daki ɗaya aka bamu me ɗauke da qatuwar katifa jibgegiya se mirror da sauran tarkacen kayan daki ,akwai babban parlour da tsakar gida wanda shima babba ne ba laifi, ga kitchen da store, nayi matuqar qoqari wajen kiyaye taɓa duk wani abu da be zama dole ba, misali,ta na da babban gas cooker Wanda ake amfani da shi da wutar lantarki da gas,ban taɓa tabawa ba da sunan zan girki, na tarar da babban deep freezer Wanda Ke dauke da naman kan rago a ciki ko da Wasa ban buɗe dan na yi amfani da shi ba na buɗe ne dan na gan shi a kunne nake mamakin gida ba kowa kuma a kunna freezer? Ina duba wa se na yi ido biyu da naman kan rago babba,da risho na ke amfani tukwane ma ban taɓa na 'yan gayu ba duk da cewa kafin na yi gobara wanda nake amfani da shi sun fi wannan amma haka na dauke kai na daga taɓa duk wani abu da na san tsautsayi zai iya sawa na lalata musu, kar mu je daga kyautata mana mu kuma mu zaqe.

Mutanen gida can Kano da Bauchi da suka ji labari sun jajanta mana ainun, domin ba qaramin jarabawar rayuwa mu ka shiga ba a wannan lokacin.

Akwai wasu lokutan da bawa kan shiga jarabawar rayuwa ko ina ya toshe masa, ya rasa inda zai saka ran shi ya ji dad'i,ya dinga ganin kamar mutane na sane da halin da yake ciki na neman taimako amma an qi a taimaka masa, a irin wannan lokacin wasu imanin su ke qaruwa wasu kuma ya ragu ko ma ya tafi gaba ɗaya su rasa shi, Alhamdulillahi halin da muka shiga bai raunata imanin mu ba, hasali ma ba mu ɗora ran cewa wani ne zai fidda mu daga wannan halin da muke ciki ba, mun yarda kuma mun amince sannan mun karbi jarabawar mu da hannu bibbiyu muna ta hamdala da istighfari, mun miqa wuya ga Allah mu na neman ya taimaka mana ya kawo mana mafita mafi alkhairi.

Gaba ɗaya kayan da za mu saka ma ba wasu masu yawa bane, domin gobara ta cinye kaso 90% a cikin kayan mu, Allah ya sa Baban Ameenah ya bamu atampa guda biyu shadda ɗaya, sai Malama Sa'a da ke da makarantar islamiyya a unguwar ta bamu atampa ɗaya, sai Maryam matar Uncle Inuwa ta bani kayan bacci guda biyu,to wannan kayan su muka samu wajen mutane, muka ajiye saboda gabatowar bikin Ameenah qanwata da za a yi nan da wasu watanni masu zuwa.

Abincin da za mu ci kuwa tun mu na iya affording ɗin siyan kayan miya, se da muka zo mu ka koma cin mai da yaji, har yajin ya qare muke saka mai da maggi da gishiri,Maggi ya qare mu ka koma cin shinkafa da mai da gishiri, mai ya qare mu ka hau duba jarkokin mai da muka tarar a store mu na Kalen man da za mu saka a abincin mu, can qasan zuciya ta ina mamakin dangi na da dangin Yah Maheer kowa shiru ba wani taimako da ya zo mana, daga baya na cire tunanin nan a rai na, na sa wa zuciya ta cewar wannan jarabawa ce daga Allah subhanahu wata'ala, ya toshe mana hanyoyin samun arziqin duniya a yanzu ne domin ya bamu na lahira, se na fara addu'ar rabbana atina fidduniya hasanatan wa fil akheerati hasanatan wa qina adhabannar, ina yi ina qasqantar da kai na wajen mai bayarwa da ya buda mana hanyoyin samu, su ma da da nake saka rai su taimaka mana ban sani ba ko akwai wani abu da ya hana su hakan, ban sani ba ko suma a wanne halin suke ciki, nan da nan na sake kwantar kai na da tunani da kuma jiran taimako daga wajen wasu saboda ba su suka halicce mu ba, wanda ya halicce mu ya san za mu iya jurewa ne shi yasa ya kawo mu wannan matsayin.

Yah Maheer ya umarce ni dama tun randa mu ka yi gobarar akan cewa duk wanda ya tambaye ni na ce ba wani sosai bane amma mun samu gidan da za mu koma da zama, haka na dinga faɗa wa 'yan uwa na, da na shi, duk da cewar na tabbata a yanayin yanda suke jin tashin hankali a murya ta da tashi sun san ba qaramar gobara muka yi ba.

Yah Maheer ya yi iya qoqarin shi dan ganin ya kwantar min da hankali ya kuma nuna min in har ya samu dama zai maida min duk abinda na rasa da ma mafiyin hakan, a kullum muka zauna se ya yaba min akan yanda nake handling situation din da muke ciki.

Ana haka ban san ina ya samo kuɗi ba ya siyo mana kayan abincin da za su kai mu sati ɗaya haka,da mai da maggi da yaji,buɗe freezer ɗin da naman kan da muka tarar a gidan na yi na ajiye kayan miyan da na wanke mana dan mu na diba a hankali kar su lalace.

MAHREEN Where stories live. Discover now