Mu na nan kwance mu na jiyo hirar su sama sama, tun mu na jiyo hirar su da shewar su har muka dena ji alamun kowa ya samu inda ya dora haqarqarin shi kenan, bamu jima da kwanciya ba sosai aka kawo wuta alamu ne na sha biyu na dare ya yi kenan hamdala na yi na sake bajewa a katifar da muke bazawa a parlour dan Shan iska.

Washegari da safe qamshin soye soye ne ya cika min hanci na farka daga nannauyan baccin da na ke, waya ta na ja ina murza ido na, da sauri na tashi ina addu'ar tashi daga bacci, gani na yi gari ya waye sosai qarfe wajen tara na safe, da alama Suwaidatu ce ta gama soya dankalin turawa da kwai ta dafa ruwan tea sai qaton bread da ta dora a babban faranti ta ajiye mana a kitchen ɗin tunda har a wannan lokacin ina kwance a parlour ne inda muke bajewa mu ci abincin daga nan ta wuce makaranta, godiya na yi ga Allah da na koya mata girki da wuri ba dan haka ba yanda na makara ba su tashen ba wa zai mata?

Tashi na yi na daga katifar da kyar ina jin bani da wani qarfi a jiki na, daga baya na naji an kama katifar tare da dukan kafadata sannan aka mammatsa min ita, cikin jin daɗin tausar da ya ke min nake bin dukkan wani motsi da hannun sa ke yi a kafad'u na, ina sauke ajiyar zuciya kamar wadda ta yi wani qaton aiki ake mata tausa, ido muka haɗa da Yah Maheer da ya fito daga dakin Suwaidatu bayan ya ajiye kayan shi da ya cire ya saka a wajen wanki,murmushi ya min ni kuma na kyabe baki irin na shagwababbun nan na ce,

"Shine baku tashe ni ba ko? Yunwa ce ta tashe ni ina bacci na ji qamshi shine na miqe"

"Kin san dai bana so ki na bacci ana tashin ki, tunda ba koda yaushe ki ke samun baccin ba, baki ga har tokare qofar na yi ba dan kar ta dinga qara ta dame ki? Maza ki je ki wanke baki ki zo mu ci abinci yunwa nake ji"

"To gani nan zuwa, ni fa ina idar da sallah na san dai na yi istighfari uku daga nan ban san me na sake cewa ba se gani na na yi anan"

Dariya ya yi ya shige da katifar ba tare da ya amsa ni ba, bathroom na shige na watsa ruwa na wanke baki na, hayaniyar da na jiyo ana hira ne ya sa na tuna cewar ba fa mu kaɗai bane ashe a gidan, murmushi na yi a raina ina jin inshaa Allahu wannan baiwar Allah daban take za mu zauna lafiya da ita.

Ina fitowa na shige d'aki na sanya kaya masu dama dama a cikin kaya na saboda akwai mutane bana son zama ba wadatattun kaya a jiki na.

Abinci muka ci muka qoshi sannan na ce wa Yah Maheer bari na leqa maqotan mu mu gaisa, ya ce ya kamata saboda sun zo ya ce musu ina bacci.

Koma wa na yi na zauna ina fuskantar shi da kyau, dan ina so maganganu na su shiga kunnen shi da zuciyar shi, cikin marairaice fuska na ce,

"Dan Allah Yah Maheer ina so na roqi wata alfarma a wajen ka"

Kallo na ya yi shima da kyau dan ba wa magana ta mahimmanci.

"Dan Allah ina so ka rage yawan kulawar da ka ke min gaban mutane, ka ga ina kyautata zaton ita ta jawo mutane ke jin haushi na, ka na gani ko a can gida Bauchi qiri qiri za ka ji ana nuna ba me dorewa bace in dai namiji ne in dena sake jiki, ko a ce na mallake ka da sauran su, dan Allah mu na yin komai baya baya"

Tashi ya yi ya shige d'aki ya bar min wajen dan tunda ya ji inda magana ta ta dosa ya ja guntun tsaki ya maida hankalin shi wajen shanye tea din da ya rage a mug din shi, galala na sake baki na bi bayan shi da kallo, wato wannan ba abu bane me mahimmanci a wajen shi ko? Shine har ina masa magana ze min tsaki ya shige d'aki to da kyau, na tsani tsaki a rayuwa nan da nan kuwa na ji rai na ya ɓaci, da qarfi na furta.

"Allah baka sa'a ka ci gaba ina ruwa na ni"

Shima da qarfi na jiyo muryar shi ya na ban amsa har da buɗe qofar d'akin wato na ji shi da kyau ya ce,

"Da ruwan ki mana, ke kuwa ki ke da ruwa yarinya, in be dame ki ba meye na magana?"

Murgud'a masa baki na yi na yi fari da ido Ina wawwatsa 'yar rashin kunya ta yanda na ga dama, murmushi kawai ya yi ya rufe qofar ya barni tsaye ina b'ab'atu.

MAHREEN Where stories live. Discover now