page 1

228 6 0
                                    

ABLA ADNAN 1

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH

Chuchu ce dai marubuciyar
HALAL VEER,
YAR AREWA
NOORURRAHMAN
MUZUBA MUGANI
HIS JEWEL
MEERAL
KALUBALENAH.
ta sake Dawo maku da wani salo nata a cikin littafin ABLA ADNAN ,
amma a wannan karan ABLA ADNAN na kuɗi ne ,ina fatan zai samu karɓuwa gareku wanda I'm certain bazakuyi dana sanin siyansa ba,
kuyi sharing fisabilillahi 🤲🏻 rokona ,
sai daku masoya❤

FREE PAGE
1
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
_________________tafe ABLA take tana Mai taunar chew gum ɗin dake bakinta kamar ita kaɗai ce akan titin ,a zahiri haka take ,idan tana tafiya a waje ji takeyi kamar ita kaɗai ce a duniyar nan sabida ita ɗin tasan babu abunda zatayi ta burge mutane ,sanin hakan yasa idan tana waje take dauka ita kadaice sannan tasa faranta wa kanta gaba da komai,

"ji mana baiwar Allah.
tsayawa tayi tareda yin wata irin juyawa ,
karasowa matashin saurayin da yayi mata maganan yayi ,
kallo daya tayi masa ta daure fuska ,
duk faɗin layinsu shi kadaine bata shatawa layi ba amma tana tunanin yau ce ranar da nasa layin zai shatu"
ehen tafaɗa tana Mai masa wani irin kallan banza,
gyara tsayuwarsa yayi yace ,Abla yarinya mai kyau ,komai naki mai kyaune ba sai an faɗa ba ,abla ke macece kada ki bari wannan kyan naki ya ruɗe ki,ki rufama kanki asiri ki samu miji kiyi aure shi ya fi maki da wannan gantalin,
idan abunda na faɗa kuma ya bata maki rai to kiyi hakuri ba niyata kenan na bata maki ba.

cire glass ɗin dake idanunta tayi ta kallesa da kyau tace "
kai alaramma kalleni da kyau kaga ,inace kasan sunan gidanmu ,inace kuna kiran gidan Mu ne da gidan karuwai sannan babu wani irin suna da baku kirana dashi a bayan idanuna dan mutum bai isa yazo gaba naba ya faɗa ban zubar mar da hakwaran gaba ba ,to kasan Allah ka kiyayeni ,wannan ya zama karo na karshe da zaka kuma tara ta a hanya da wata maganar banza makamanciyar wannan, idan ba haka ba wallahi tallahi kaga wannan gemun naka,
baiyyi aune ba yaji ta kama dan gemunsa da ya tsayar tace "nan gaba ka kara tareni a hanya sai na raba munafukin gemunnan naka guda bakwai daga habarka,
kalar rashin kunyata kakeji amma baka taba ganinta ba amma ka guji ganinta Dan bata da alheri .
Mayar Da glass ɗinta tayi ta juya ta cigaba da tafiyarya tabarsa da tsantsan mamaki da kunya musamman da yaga mutanen dake Gurin suna Kallansa,
kai tsaye gidansu ta nufa inda tun da taga gidan a bude tasan aunty ashana yau tana suyar doyar siyarwar balain wanda abla take kira karuwanci a kasko saboda wannan sana'a tata tana daya daga cikin abunda ke Kawo musu yan iskan maza gida.

tura kofar gate ɗin tayi tana mai cigaba da yamutse yamutsenta,
tana shigowa aunty ashana ta ce "A'a abla sarautar mata kitaka duk Wani wanda zaki taka babu yarda za'ayi dake ,kinci dubu dubu sai ceto ,
makiyanki fadawanki,
mahassadanki sai dai su mutu" daga ina haka .

Dan kallanta tayi shekeke tace uwar kasko in bakiyi wasa ba zafine zai ajalinki ,ko watarana ki faɗa cikin man doyar nan dan dama ba dan Allah kike yiba ,duk wani salan tara mana kwarata a gida kin iya.

ke baki da mutunci wani zubin abla adnan nan yabanki na gama aamma ke ba abunda kika iya Sai yima mutum mugun fata.

tabe baki ABLA tayi Tace "um ke kika jiyo sa ,kallanta ta mayar kan mazan da ke shakkar shiga shirginta Tace ,aci doya dai an bar iyalai gida ,mazan kawai ,
babu wanda ya tanka ta Dan sunsan hanya ba kyau indai abla ce,
da takunta ta isa bakin falonsu ta yaye labule, regular costumer din gidansu Alh lado tagani zaune a kan kujera gabansa shake da kayan ciye ciye ,sai mahaifiyarta a gefe tana ta mai kwarkwasa.
hanyar da zata sadata da dakinta ta nufa Dan
abu na karshe da zataso tayi shine zagin Alh lado wanda aciki take dashi sabida Alakar da ke tsakaninsa da mahaifiyarta ,sannan ta tabbatar idan ya shiga sabgarta sai ta figesa ,

ABLA sarauta,yafaɗa yana Mai lashe baki kana ya kara da cewa ba gaisuwa ne balle sallama,
yitayi kamar bata jisaba ta raba zata wuce ,amma Muryar mahaifiyarta ta katseta inda take cewa ke Dan uwarki bazaki dawo ki gaidasa din bane ba shegiya irin tsiya,
yar dariya tayi kana ta juyo tana Mai kallansu tace "yo ai ni mama banga abun gaidawa anan ba,
dama ke kikace na gaidaki na iya darajar haihuwa bata hidima ba amma wannan bunsurun wallahi bazan taɓa asarar sallamata da gaisuwa taba akansa sannan mama da kika kirani shegiya ai bakiyi karyaba itace sannan bani bace na maida kaina shegiya kece nan ,kece mai alhaki dan haka ki daina nuna mun wannan tsanar a ko ina ,ma'ana ki dinga koda bai kai zuciyarki ba kina boyewa ,
sannan kai kuma tsohon najadu wallahi idan na kara ganin kana kallan Mun baya kana lasar baki sainaci kutumar uban Tsoho ,

tana kai aya ta shige dakinta ta banko kofa ,kan gadonta da yake cin mutun daya ta faɗa ta kwanta tasaka wani irin kuka mai cin rai tana tuna irin adadin kiyayyar mahaifiyarta gareta tun daga yarinta har zuwa girmanta yanzu shekara ashirin kenan.

CHUCHUJAY✍🏽

ABLA ADNANWhere stories live. Discover now