Yanda ya yi maganar ma ni se ya sanya ni dariya, sannan daga baya na gane ai duk abinda ya faɗa gaskiya ne zai kashe kan shi da yunwa ne in be ci abincin wani wajen ba a sanda bana nan? Hira muka ci gaba da yi ya na sanar da ni yanda zan dinga zama da mutane ba komai ne za a faɗa min in dinga dauka ba, wani burin shi ya hana ka zaman lafiya,a haka dai mukai ta hira kala kala har aka manta da zancen.

Ajiyar zuciya na sauke mai qarfi bayan na gama dogon tunani na,a daddafe na tashi na shiga kitchen na yi girki, taliya ce kawai na dafa dama ina da miya, se na yanka lemo da kankana na ajiye sannan na yi wanka na yi sallar la'asar da ta jima da wuce wa.

Wata riga ta na sanya wadda za a kira ta da net, Dan kuwa Shara Shara ce sosai, sai pant da na saka shi kaɗai, zaune nake ina shan iska Suwaidatu da ta dawo daga boko ina bacci ta yi shirin islamiyya ta tafi, dan ta makara sosai jira take dama na farka ta shirya ta tafi, nan take na tuna cewa BD na fa ya gabato December din nan zan cika shekara sha takwas cif-cif,murmushi ne ya kwace min, na hau murna,ni ma zan zama babba.

Maman Ameerah ce ta fito da daurin qirjin ta kamar kullum, zama ta yi a gefe na mu ka hau hira jefi jefi, cikin zumudi na ke sanar da ita cewar,

"Gobe fa BD dina,"

A d'age ta Kalle ni ta ce,

"Shekara nawa?"

"Inshaa Allahu gobe zan cika shekara sha takwaaaasss"

"Mtssswwwwww, ni na zaci ma kin kai ashirin ashe ke se yanzu ne zaki shekara sha takwas ɗin?"

Wani irin b'acin rai na ji ya kama ni, saboda ina da wani hali na tsani tsaki, ita kuma halin ta kenan, bata iya minti ashirin bata zabga shi ba, ni Ko ba da ni akai tsaki ba se na ji ba daɗi balle ayi da ni, kallon ta na yi ni ma a d'age dan na fara mayar mata martanin rashin kyautatawar ta nima a hankali ba tare da na sani ba ma.

"To ai dama kowa da shekarun shi a duniya nima iya nawa kenan, kuma ina alfahari da hakan na ji dad'i da zan cika shekara sha takwas Alhamdulillahi "

Surutai ta dinga yi ta kama hanya ta shige d'akin ta, mamaki ne ya kama ni menene na faɗa a cika shekara sha takwas? Da kai na na furta,

"Allah ya qara kema, me shegen surutun tsiya, komai se kin faɗa ai gashi nan"

Miqe wa na yi da kyar na shige nawa gidan raina a bace, da dare na zaci Yah Maheer ya manta da BD na, se na hau hira a fakaice ina fadan date of birth ɗina, ya na ji na be ce komai ba, haushi ya kama ni, saboda ni fa na ɗauki cika ta shekara sha takwas babban abu, ni ina ta BD ɗina shi ya na ta lafiya ta, dan rashin lafiyar da nake ba ta boyu a idon shi ba, sannan na sanar da shi ko map reading exam ban tsaya na qarasa ba gida na dawo, dan haka a dame yake, what if na zo ban samu na ci Geography ba da dai sauran tunane tunanen nan su suka haɗe masa suka hana shi kula ni.

Ina nan ina kumbura baki ya wuce masallaci sallahr Isha'i,ko da ya dawo na yi wanka na fito da katifa parlour,na yi readyn yin bacci, ina nan daga kwance mu na ta hirar gida dan kuwa ya ce da sallah can za mu je mu yi sallah,har qarfe sha biyu bacci ya qi dauka ta, kuma yau mu ne zamu kwana ba wuta se asuba a kawo, kamar jira suke kuwa  ina kwance kawai se dif an ɗauke wuta, wani irin kuka ne ya tokare min wuta saboda na san yau ba zan bacci ba, banda ma rashin baccin da zan yi ciwon da qurajen nan za su hau yi min ba kaɗan bane domin dama ranar an kod'a rana.

Lallashi na Yah Maheer ya hau yi, ya ja maficin da ke gaba na ya hau yi min firfita, ni dai shiru kawai na yi bahaushe ya ce da babu gwanda ba dad'i amma kam bana wani jin firfitar nan, kula da hakan ne ya sa ya ce min,

"Baby na ki qara hakuri, na san zaki ta jin maqota sun kunna inji mu kuma shiru, ga AC a kowanne gida akwai ta amma mu shiru, inshaa Allahu watarana zan sa maki AC zafi ba zai dinga damun ki ba, zan kuma sai maki gen in ba wuta kawai se mu kunna gen ɗin mu mu kunna Acn mu mu sha ko?"

MAHREEN Where stories live. Discover now