"Yaushe za mu tafi to? Kaa bar ni se ihun murna nake baka ce komai baaa"

Murmushi ya yi sannan ya sanya yatsan shi manuni ya na kewaye lips ɗi na da ya ke masifar so ya ce,

"Baby na na barki ne ki yi murnar ki sannan in sanar da ke tsarin tafiyar, ai kin ga be kamata ki na tsaka da farin ciki ba na katse miki shi ko?"

Ji na yi hankali na ya tashi da jin yace zai katse min farin ciki, da sauri na sake mannewa a jikin shi na ce,

"Ni fa ban gane ba? Me ka ke nufi?"

"Ina nufin ba tare da ku zan koma ba kai tsaye, har sai na je na ga yanda wajen yake in yaso se na dawo na ɗauke ku mu tafi dika"

Ji na yi hawaye sun fara bin kunci na,raina na tafarfasa me yake nufi? Ya na nufin zai iya tafiya wani garin me nisa ya barni? Ina jin fa ya na faɗin in aka tashi daga Bauchi tin safe se an kai goman dare ko sama da haka kan a isa garin, me yasa ba zai je da ni ba?

Kwantar da kaina ya yi a qirjin shi ya sumbaci goshi na sannan ya hau jijjiga jikin shi ya na lallashi na,

"Habaa young lady? Kukan me ki ke kuma? Ke da zan tafi na bar ki ki zama shugabar gidan duk wanda ya yi ba daidai ba ki hukunta shi, ko ki bari in na dawo ki sanar da ni,dan Allah ki dena kuka bana so, ba fa yanzu bane tafiyar ma se next month ne fa"

Cikin kukan da na sake rikicewa da shi na ce,

"Lallai ma Yah Maheer ɗin nan jibi ne fa next month ɗin "

"Eh mana kin ga kuwa ai da saura, next month fa, month fa aka ce ba week ba"

Kawai sai na ji wani irin ɓacin rai ya kama ni, saboda hakan ba abun wasa bane, abu ne me mahimmanci a waje na amma yake wasa da shi.

"Yaushe ya zama next month bayan jibi jibin nan za ku tafi, kai yanzu baka ji komai ba za ka tafi ka barni?"

"Baby na da ace zan iya buɗe maki zuciya ta ki ga irin kewar ki da na fara tin a ranar da na fara neman aikin da sai kin tausaya min,ba yanda za mu yi ne tafiyar nan inshaa Allahu alkhairi ce inganta rayuwar mu zata yi nan gaba, na yi zaton ma za ki lallashe ni tinda ni ne zan je inda babu ke babu kowaaaa a dangi daga ni sai mutanen da ban sani ba, ban taɓa ganin su ba, ban san ya halayya da dabi'un su ya yake ba, Baby na dan Allah ki yi hakuri ki dena kukan haka ya isa"

Sauka na ɗan yi daga jikin shi sannan na daki qirjin shi, cikin shagwaba na ce,

"To ba kukan tausayin ka nake yi ba yanzu,ai ni ban san kai kaɗai za ka tafi ba, amma kar ka damu ka na da Allah, Allah ya kare ka ya biya buqatu na alkhairi, Allah ya sa ka je lafiya ka dawo ka tadda mu lafiya"

"Yauwaa My love ko ke fa a dena kukan banzaaaa"

Cakulkuli ya fara min muna ta dariya, lokacin sallar azahar ne ya yi, muka tashi baki ɗaya dan zuwa sauke farali, bayan fitar Yah Maheer ne na idar da Sallah sai na ji motsin Maimunah a waje da yara, ai kuwa se na fita nima,na kora su zuwa sallah muka dasa hira da Maimunah,cikin hirar mu ne take sanar da ni mijin ta ya yi mata alqawarin ba zai mata kishiya ba sam, daga jin haka sai na ji ita fa a duniya ta gama more wa,nan da nan na qudirta nima idan Yah Maheer ya dawo zan tambaye shi zai min kishiya ko ba zai min ba.

Murna fal ciki na, dan kuwa na gama yanke irin amsar da zan samu duba da yanda yake masifar so na, muna ta hira sai gashi ya dawo shi da mijin Maimunah da alama ya sanar da shi maganar tafiyar shi, dan na ji ya na ta zabga mana fatan alkhairi, ciki suka shige suka bar mu anan waje, ba jimawa nima na bi Yah Maheer ciki, zaune na gan shi bakin gado da wasu takardu a hannun shi ya na dubawa, ban katse shi ba sai da ya gama ya sanya a jakar shi da yake tafiya da ita sannan ya haye gado da kyau, hannu ya miqa min na kuwa tafi da sauri na kama na haye jikin shi na zauna da kyau a qafafun shi ina kallon cikin idon shi, dan so nake ya ji kunya ta nima ya min irin alqawarin da aka yi wa Addah.

MAHREEN Where stories live. Discover now