MAHREEN PAGE 17

Começar do início
                                    

Cikin fushin kuwa na juya Ina kallon shi sannan na ce,

"Habaa dan Allah Husband sai da na gama had'a kaya kafff na kulle komai tafiya kawai nake Jira sannan zaka ce na warware ga kayan ka ba a sama suke ba ma, gaskiya ni dai ka bari in na je can zan cire Maka, and ni bana son wata darling Baba ma fa haka yake Kiran Mama da shi kana kirana darling kamar wata tsohuwa"

Dariya ya dinga yi sannan ya kama hannu na muka zauna a kujera mai cin mutum biyu, ya ce,

"To Baby na daga yau na dena Kiran ki da darling shi kenan? Kuma ai gani na yi Baba na ce maki darling yaran gidan ku ma wasu darling Mahreen suke ce maki....to yanzu daiii komai ya wuce zan je na cire kaya na in yaso se ki qara gyara inda ya b'aci ko?"

Ni dai ba haka na so ba, na so mun yi tafiyar ne tare fushin da nake kenan,ni bana son abinda zai na raba ni da shi na tsawon lokaci, shine dalilin da ya sa ko Kano zani asibiti yake raka ni, to amma wannan karon da alama hakan ba zata samu ba, dan haka washe baki na yi na nuna masa komai ya wuce zan cire masa kayan nashi sannan na masa addu'a da fatan alkhairi akan abinda za su yu d'in.

A ranar da za mu tafi na dinga jiran Habibah ta min maganar tafiya shiru, dan haka da muka gaji da Jira sai muka nufi tasha ko da muka je ashe su a motar gida za su tafi shi yasa bata min maganar tafiya ba tunda ba motar su bace,da samun labari sai muka shiga motar haya muka tafi ni da Suwaidatu, muna tashi motar bayan mu ma ta kusan cika ashe su Isma'il sun shige ta, dan haka gaba d'ayan mu sai muka isa kusan a tare, Yara kuwa aka hau murna kamar yanda suka saba wannan karon murnar ta zama biyu ga amarya ga Zaituna da tsohon ciki, haka muka tsaya sashen Yayan su Yah Maheer muka gaggaisa a tsaitsaye da su Maman Ummeeta sama sama, sannan muka shige sashen mu, muna shiga gidan Ummah da Mama suka taso su na mana lale maraba, sauran qannen Yah Maheer ma na yi mana maraba lale, gani na yi Ummah ta kama akwatin Habibah suka wuce suka yi d'akin Umman Mama ma ta ja na Zaituna suka yi d'aki Sai gani tsaye a tsakar gida zuruuu ba me Jan nawa akwatin Ina tsaye Ina tunanin shin me ya faru ne haka Sai ga Baba ya fito daga d'akin Shi babu riga saboda zafi da yake Ji, ya kama akwati na zai shigar min da Shi d'akin Ummah da sauri na kama na riqe na ce,

"Habaa Baba ka bari Zan Iya ja ba komai, na gode"

Suwaidatu na gani ta fito daga d'akin su bayan ta ajiye ta ta jakar, jiki ba kwari na ja akwati na na Kai d'aki a sannan ne Ummah ta hau min sannu da zuwa, na amsa mata Kamar ba abinda ya faru,cikin Ikon Allah kuma Sai na Ji bana jin zafin abinda ta yi d'azun,nan fa aka hau hidima da mu,hirace ta daban ta kuma musamman ke gudana tsakanin ta da Habibah ana jefa wa da ni sama sama, ko kuma in sanya kaina a ciki ko da ba a saka ni ba.

A haka muka kwana washegari muka yi wanka muka shirya dan zuwa ziyara, har gidan Addah Ummuna sai da muka je, mun sha yawo sosai na ziyara har sai da qafafun mu suka gaji Libus.

Ko da muka dawo gida da yamma lisss mun gaji, na shiga banɗaki na watsa ruwa na yi alwala, a inda na bar su suna hira da Ummah nan na same ta, dan haka se na musu sallama na wuce ciki na shirya sannan na tada sallah, Zaitunah na daki ita da su Suwaidatu suna tasu hirar Mama na kai wa Baba tuwon shi na dare.

Kafin na idar Habibah ta je ta yi alwala itama ta zo ta tada sallah,Ummah kuma ta fita tsakar gida dan su ci abinci da Mama se aka bar mu mu biyu a d'aki, hira muke ta zabgawa kamar wasu dad'add'un qawaye, muna tsaka da hira Kabeer  ya kira ta, ta kuwa kashe murya ta amsa sallamar shi, yanayin yanda take amsa wayar se ya bani kunya da sauri na kalli hanyar d'akin Baba wanda bamu da nisa da shi, da hannu na yi mata nuni da ta yi a hankali kar ya ji ta, domin shi mutum ne da baya maraba da irin wad'annan abubuwan, na kula yanayin yanda muke jin nauyin juna ni da Yah Maheer a cikin gidan ya na burge Baban, tinda a fili yanayin soyayyar mu, shaquwa, da kulawar mu yake amma bama bayyana wa ta yanda za a ga rashin kunyar mu.

MAHREEN Onde histórias criam vida. Descubra agora