"Allah ya bamu yatsu biyar mu sa mu tsaida sunnah" ni kuwa na d'aga murya yanda zai ji ni na ce,

"Ai ya kamata a fara tsaida ita sunnar ne tin fari ba sai an nemi magana ba wajen aikata bidi'a"

Mamaki na ya qara kama shi, kawai sai ya kad'a kai ya shige parlour, ina jiyo shi yana hira da Abubakar, ban san dai akan me suke magana ba, mu kuwa muka ci abincin mu muka tashi.

Isma'il be daddara ba ya fito zai maida plate kitchen tsabar neman magana, ga takalmin shi nan amma se ya jawo na Yah Maheer da nake kaiwa gefe na ajiye in ya fita, ya tura qatuwar qafar shi zai saka, cikin sauri na isa gaban shi na janye takalman na ce,

"Wai kai me ke damun ka ne? Ko rashin kunyar taka ta kai ka dinga ganin kan ku d'aya da miji na ne? Kar ka qara tab'a kayan shi na fada maka, ba tarbiyyar da aka mana ba kenan a gida yaro ya na saka kayan manya"

"Ni kenan bani da tarbiyya ba a min tarbiyya ba a gida?"

"Wannan kuma kai ka fad'a, amma kar a qara saka takalmin miji na"

"Sannu me miji, muma dai Allah ya aurar da mu"

"Ameeen ya Allah"

Sai ya maida abinda ya faru wasa, ya ajiye plate ya koma d'aki.

Bayan kwana biyu muna zaune da Maimunah a tsakar gida kowa na aikin da yake gaban shi yara na makaranta, se ga Ismail ya dawo daga wajen aiki, bayan ya mana sallama se ya shige ciki,mu ka ci gaba da aikin mu da hirar mu,se ga Isma'il da butar da Yah Maheer ke amfani da ita zai wuce mu ya shiga bayan gida, ban bata lokaci ba wajen amshe butar na ajiye gefe na ba tare da na ce masa komai ba,kallo na ya yi cikin jin haushi dan da alama a matse yake da koma menene ya koro shi gida, ni kuma na ci gaba da aiki na ban kula shi ba, k'wafa ya yi ya koma ya dakko butar su ya shige band'aki, muna zaune sai tusoshi muka ji suna fita da qarfin tsiya, nan fa muka dinga kokawar rugawa cikin d'akunan mu saboda kar ya ji dariyar mu, a guje na shiga parlour na na dinga zuba dariya, har da hawaye, se dariya zata tsaya se qarar tusa ta qara karad'e gidan, ina zaune a haka na jiyo motsin shi zai shigo parlourn kifa kaina na yi a hannun kujera ina kallon waje ta window fuskata ta yi jawur saboda dariyar da na sha ga kuma wata na neman kwace min, kallo na ya yi ya kad'a kai ya shige d'akin su ya rufe qofar da qarfi, wata mahaukaciyar dariya ce ta kwace min na kuwa bud'e murya na dinga dariya kamar zan yi yaya, bud'e qofar ya yi ya kalle ni kamar ze yi magana se kuma ya fasa, ya dau takalmin shi ya bar gidan, ni da Maimunah me za mu yi banda dariya, ranar haka muka wuni da mun tuna sai mun yi dariya.

A kwana a tashi sai ya fito da d'abi'ar kwashe min ruwa a drum, ba ya tashi wanka har sai an d'auke ruwan pampo, se idan ni ko yaran mun tara ruwa daga pampo sannan zai zo ya kwashe wanda aka tara ya ce zai wanka, ni kuma haka ne ba zan lamunta ba, duk randa ya bari aka d'auke ruwa be d'iba ba to fa ba zan bari ya kwashe wanda aka tara ba, domin kuwa idan ya kwashe zuwa yamma muka zo amfani da shi se fa yaran sun fita rijiya a waje sun samo ruwa, hakan da nake yi na rashin bari a taka ni se ya jawo min tsana wajen Isma'il.

Watarana mun gama tara ruwa ya na d'aki be fito ba har aka d'auke na pampo, na kuwa ce ba zai d'iba a drum ba, dan ko mu bamu gama d'iba ba aka d'auke ruwan, nan da nan ran shi ya b'aci ya hau bambamin masifa, na masa banza na ce ba dai zai d'iba ba, maimunah ce ta fito ta ce,

"Isma'il ka deb'i ruwan drum d'ina dama muna so mu kwashe a zuba wani"

Nan fa ya d'auki bokiti ya hau kwasan ruwan drum d'in Maimuna,tare da fad'in,

"Ke dai Allah ya tsunduma ki a aljannah ya sa oga ba zai maki kishiya ba, Allah ya maki albarka"

Ni kuma na ce,

"Ameeen in da gaske ka ke, in ma ka fad'a ne dan na ji haushi to ban ji ba, domin kuwa kullum ta Allah se miji na ya samin albarka ya min addu'a,kuma na ga aljannar nan dai ba kai za ka kira ni ka ce zo ki shiga ba balle ka hana ni, dan haka ka gama dad'in bakin ka kai ka sani"

MAHREEN Where stories live. Discover now