"Lami gashi a raba"

Tsinke ta danna a baki ta hau sakace sannan ta miqe qafafu tare da tura d'ankwalin ta bayan kan ta ta na sosa kan nata can ta maida hannun tsakiyar cinyoyin ta ta ce,

"Ah ah yaya raba dai"

Ganin yanda ta yi maganar se na ji jiki na ya yi sanyi, ita kuwa Umma fuskar ta dauke da yaqe ta ajiye leda gaban ta, ta bud'e ta hau rabo.

Sashe shida ne a cikin babban gidan na su Yah Maheer amma se na ga ta yi kaso takwas,kowa ya samu Omo sabulu da biscuits da sweet, yaran da ke tsaye basu tafi ba Umma ta dinga kira ta na basu, suka karb'a suka tafi kaiwa kowanne sashe a gidan, sauran kason ta had'e su waje d'aya ta ce a zo a kai wa gidajen da ya kamata a sanar da su matar Maheer ta zo.

Ranar haka na kai magariba ina ganin gata da kulawar dangin miji kuma dangi na, murna da farin ciki duk ya cika zuciya ta,na gaza boye farin ciki na, amma sai dai ina da wani hali, wato rashin sakewa da mutane da farkon had'uwa, sai na gama sanin halin kowa sannan zan fito da nawa na addabi jama'a, wannan dalilin ne ya sa bana dariya sai dai murmushi bana kuma Uhmmm bana um-um,komai aka yi da ido nake bin kowa ina karantar kowa.

Bayan magariba ina zaune ni d'aya a d'aki yara biyu suka shiga, Hafsat da Safiyya suka sanar da ni iyayen su na can na jira na a ci abincin dare,sannan kuma mu yi hira.

Tashi na yi na gyara riga ta sosai a jiki na na sanya hijabi na bi bayan su, duhun dare ya fara dan haka sai na kunna fitilar jikin waya ta ina haska mana hanya har muka shiga sashen babban yayan su na gidan wanda yake da mata biyu a wannan lokacin, yara na gani da yawa da kuma sauran matan qannen Yah Maheer Aeesha da Maryam (Allah ya mata rahama) Maryam mace ce mai tsananin fara'a da tsokana, dan haka sai na samu kaina da qaunar ta cikin raina.

Sai Yaya wato Maman Ummee da amaryar ta Halima da suke kira da Umman Muheebbah,mata ne masu barkwanci da son mutane tare da girmama baqo, mata ne da in har zan bayyana dikkan  mutunci da soyayyar da suka nuna min to fa se mu qare page din nan kaf ban gama ba.

Aysha matar qanin Yah Maheer kuma ta b'angaren mahaifiyar shi a matsayin Innar shi take, macece mai fara'a ta nuna min qauna kwarai, hira akai ta yi ana abun dariya bayan mun kammala cin abinci ni dai daga murmushi se murmushi ba na jefa baki na a maganar su,cikin zuciya ta kuwa har na hango ni na sake a cikin su ba qaramin dariya za a sha ba, domin kuwa da alama kallon 'yar birni suke min se kace su d'in qauyawa ne, ita Yaya wato Maman Ummee a koda yaushe qoqari take ta jefa min kalmar turanci in muna magana, se a yi shewa a tafa jin Yaya ta yi turanci, ni kuma dariya kamar na yi yaya amma haka zan guntse ta in maye gurbin ta da murmushi.

Ban bar wajen su ba sai qarfe goma na dare da Baban Ummee ya dawo muka gaisa na yi musu sallama, da fari suka ce na yi zama na ai nan se a kai sha d'aya ma ko sama da haka ana hira musamman in an yi baqi, na nuna masu bacci nake ji, nan kuwa qasan raina ina so na zame ne na je wajen Yah Maheer da ke ta zabga min saqonni kala kala na ya yi kewa ta in je mu gaisa mana, ai kuwa miqewar nan da zan yi sai jin sallamar shi na yi, ashe tare suke da Baban Ummee suna hira a waje, murmushi na yi a raina ina ayyana,

'Ohhh Yah Maheer ba ko kunya, da kana tare da Yayan naka ka ke min wad'annan messages, Ustaz kam a ido gashi nan tsaf'

"Kallon kuma fa? Ai tinda kin zo gida yanzu kin barshi ya huta ko?"

In ji Umman Muheebbah da ke tsokana ta, Maman Ummee da muke kira da Yaya kuwa ta ce,

"Yo ai shine ya wani kafe ta da ido ba zai iya hakuri ba se da ya biyo sahun ta"

Nan suka shiga gaisawa da juna cikin mutuntawa da nuna tsantsar shaquwa da qaunar da ke tsakanin su, tin a nan na fahimci yanda matan yayan nashi ke son shi kuma suke wasa da dariya da junan su cikin nishad'i, ba su yi aune ba na zame jiki na na koma d'akin Umma wadda har ta gyara min gado ita ta sakko qasa wai anan za ta kwanta, ai kuwa na ce sam ba zai yuwu ba, se dai ni na kwanta a qasa ita ta hau gado.

MAHREEN Where stories live. Discover now