MAHREEN PAGE 6

Depuis le début
                                    

Hankalin ta ta tattaro ta miqo min dika, tare da juyowa saitin inda nake muka fara fuskantar juna.

"Uhumm ina jin ki, akan menene?"

"Mama dama wannan watan ban ga period d'ina ba, kuma ya na min tsallake shine Maman Ihsan ta ce na sanar da ke akwai matsala"

Shiru ta yi kamar ba zata yi magana ba, can na ji ta ta na cewa,

"Iya sanin da na maki ba kya shashanci balle a ce ciki gare ki...."

"Ciki?? Ciki na me?"

Banza ta yi da tambaya ta, sannan ta ci gaba da magana,

"....Amma inshaa Allahu zai daidaita ai da yake kin fara ki na da qarancin shekaru wataqila shi yasa yake hakan"

"Ok kenan ze daina? Amma mama na ji kin ce ciki"

Bata sake kula ni ba ta juya ta ci gaba da jan carbin ta, ni kuma da tinani na kwana a raina.

Washegari mu na magana da Maman Ihsan nake mata bayani, ta ce.

"kwarai, nima ba dan na san halin ki ba sai na ce ciki ne, amma kuma sanin ke wacece shi ya sa ban ma kawo maki wannan maganar ba, tinda ba lallai ne ma ki fahimci me nake magaba akai ba, kamar yanda ki ka yi a yanzu"

Na sha mamaki sosai da na ji cikakken bayani akan idan mace ta dena jinin al'ada ya na iya yuwa ciki ne, wannan shine babban kuskure da aka tafka tin asali na qin tsananta bincike akan matsalar rashin yin jinin al'ada da bana yi a jere yanda ya kamata.

*******************************

Kasancewar asalin tushen Innata shine garin Daura muna yawan zuwa da ita lokacin da nake hannun ta sun sanni na san su sosai, haka ne ya sanya Innata tafiya da ni ana biki na saura wata d'aya, tafiya ce da ba zan tab'a.mantawa ba a rayuwa ta, saboda gata da qaunar da dangin mahaifiya ta suka nuna min, na sha addu'o'i da fatan alkhairi, ga abubuwan azziqi da akai ta bani a matsayin gudummawar aure na, abu d'aya Innata ta hana a bani shine kayan mata, bana tina sha ko cin komai da ya danganci maganin mata, illa tukud'i da na sha da madarar shanu tabbas na sha madarar shanu sosai da kindirmo ba iyaka, kasancewar  Sana'ar Inna Habi ne saida tukud'i kusan kullum sai an daka shi, nono da madara kuwa kusan ko ina muka je ana kawo mana da fura, ni ba ma'abociyar shan fura bace sosai a da,shi ne dalilin da ya sa nake shan nonon ko madarar na bar furar, haka muka gama zaga dangi muka juyo ana biki sauran sati biyu.

Direct gidan mu Innata ta maida ni, Mama na kwashe shanya a inda muke shanya wanki, ko shiga gidan Inna bata yi ba kasancewar magariba ta yi, a tsaitsaye mama ta leqa suka yi sallama a lokacin Addah Ummu ta zo biki na da cikin ta na fari wanda in ba ka kula ba ba zaka gane akwai shi ba, a tare muka qarasa nad'e shanyar kayan da Mama ke nad'e wa kafin zuwammu, muna kwashewa ina zuba mata hira da irin abubuwan da aka bani, da nasiha da addu'o'in da na sha a wajen manyan mutanen da muka je wajen su.

"Tabbas ga kaya nan niqi niqi an dawo da su Allah ya saka masu da alkhairi, Allah kuma ya amsa addu'ar su ya biya su da alkhairi"

"Ameen" na furta muka shige cikin gida, na tadda Addah Ummu kwance kamar ruwa,dan kuwa cikin ba qaramin wahala yake bata ba, hira muka fara sosai ina ta mata tambayoyi ita kuma ta na amsa min ba tare da gajiyawa ba, inda take sanar da ni Addah Firdaus na nan tafe itama, murna na dinga yi ina kumawa, baqin ciki na d'aya da ya kasance Addah Babba ba zata samu damar zuwa ba saboda tsohon cikin da take dauke da shi.

Tin da na tafi muke waya da Mansoor, shi kuwa Yah Maheer be damu da kira na ba, hakan kuma na mugun qona zuciya ta, ta ya za a yi ka zo rumi rumi ka nemi auren yarinya ya zamana ba ka kiran ta sai sanda ka so? 'yar I love you d'in nan tinda aka fad'e ta sau d'aya ba a sake ba, duk sanda zai kira waya har na harda ce abinda zai tambaye ni akai.

MAHREEN Où les histoires vivent. Découvrez maintenant