"Allah sarki Babana bawan Allah, an sa shi a kwana da wannan shagwab'ar, na san ya na can ya rikice ya rasa inda zai saka kan shi"

Da hannu na mata alamar ta yi shiru dan ba Baban nata bane, (Yah Maheer) murmushi ta yi ta zauna a gefe na itama ta na shan iska.

Ganin haka ne ya sa mu ka yi sallama da Mansoor ba dan mun so ba, hira muka dinga yi da ita, ta na sanar da ni d'azu bayan tafiyar mu shan iska yaran gidan su Yah Maheer sun zo gani na,suna roqon dan Allah gobe na je gidan su, murmushi na yi kawai, dan ko giyar wake na sha ba zan iya zuwa gidan su ba, to in je in ce na je wajen wa? Ban ma san gidan su ba tinda ban tab'a zuwa ba, zuwa na garin ma kwata kwata sau d'aya sau d'ayan ma ba wai na je gidan su bane, sannan time d'in be fara zuwa gidan mu ba, kallon Aunty Meenah na yi na ce,

"Su dai yi hakuri, me suke ci na baka na zuba? Indai wannan 'yar lukutar ce za su gan ta har sai sun gaji"

Dariya ta yi, ta na min surutun yanda nake yi wa jiki na tsiyar qiba,

"Ba za a kira ki da 'yar lukuta ba ai ke you are just chubby, masha Allah ina son irin jikin ki"

"Hahhhaaaa Aunty Meenah ba wani wayo fa, d'an lukuti d'an lukuti ne, siriri siriri ne,ba wani chubby duk salo ne na kar a kira me qiba da Fat"

Dariya ta yi ta na ta biye wa shirme na,har dare ya yi sosai muka shige gida dan mu kwanta.

A dakin matar Yayan mijin Addah Ummu za mu kwana, wanda dikka 'yan uwa muke na kusa ma kuwa, ina tsaka da d'aura zani Yayan mu ya shiga wato yayan mijin Addah Ummu,ya na gani na ya hau tasbihi ga Allah, a d'an rikice na juya na kalle shi, saboda a wannan lokacin a tsorace nake bamu jima da jin kukan mage ba, ni kuma a duniya ina tsoron ta sosai, a zato na ya ga magen ne shi ya sanya shi wannan tasbihin, yanda na riki ce ne ya sake sanya shi samun waje ya zauna,

"Ikon Allah, dama gidan Baffa Muhammadun akwai kalar wannan shine nima ban je ba?"

Wata ajiyar zuciya na sauke mai qarfi da ke nuna kwanciyar hankalin da na samu jin cewa ba mage bace.

Matar shi Aunty Khadeejah mai kirki dariya ta dinga yi, ko kad'an ban ga alamun b'acin rai ba a fuskar ta, duba da yanda Yayan namu ke ta yabo na da nuna maitar shi akai na, cikin murmushi ta ce,

"Ai se ka yi hakuri tinda dai Yah Maheer d'in Tafare ya riga ka,ba dan ma iko na Allah ba ai da tini yanzu ita ma ta na d'akin ta, to Allah be nufa za a had'a bikin ba,"

"Ke ki bari dan manzo, wai ki na nufin Yah Maheer shiru shirun nan har ya san ya zab'i mace kamar wannan?"

"To kai ma ka yaba balle shi da yake a nutse"

B'ata rai ya yi sosai har sai da itama ta sha jinin jikin ta,

"Ki na nufin ni banda nutsuwa kenan?"

Ganin yanda ta shiga taitayin ta ne ya sanya ni shiga maganar su, na dauke hankalin shi da hira, sannan ina jinjina yanda matar ke da tsananin biyayya, da girmama mijin nata, tinda a gaban ta ya tsaya yabon wata mace ba ita ba dik da cewa itan ma ba mummuna bace, ga ta da gashi masha Allah irin na fulani, inda wata matar ce yaushe zata zauna ana yabon wata a gaban ta? Na samu nasarar d'auke hankalin shi kuwa, har na fara hamma, ya na ganin haka ya mana sallama ya fita, mu ka rufe qofa mu ka kwanta.

Washe gari da safe aka tashi da gagarumin biki, domin kuwa sabon biki aka dasa, har da nad'in sarauta sai da aka yi wa Mijin Addah Ummu sarautar Yariman sarkin fulani.

Dik da buya da qin zuwa gidan su Yah Maheer da na yi ashe sai da qannen shi da yaran Yayan shi suka ganni, haka aka gama biki tsaf muka bar amare muka koma Kano ba tare da na je gidan su Yah Maheer ba, dik da roqo na da ya dinga yi ta waya akan na je na gaishe da Umman shi.

A gani na hakan be dace ba, kawai sai in je in ce ni ce wa? Akwai kunya ai, su qara hakuri watarana ma za su ji sun gaji da gani na, abinda na dinga ayyana wa a raina kenan bayan mun kama hanyar Kano.

Koma wa ta kano da sati biyu na fara ciwon mara sosai, amma period ya qi zuwar min,gashi dama na jima ban yi ba dan a qalla na kai wajen wata hud'u ban yi ba, wanda ni ban san hakan matsala bane, shi yasa ban sanar da kowa ba.

Gidan maqociyar mu na je inda nake koyon d'inki, ina kwance a qasan ledar parlourn ta ina ta juyi, sakamakon ciwon cikin da ya taso min,a hankali nake iya bud'e ido na, tinawa na yi da addu'ar da Baba ko mama suke yi min a qafa ta a duk sanda ta tashi da ciwo, nan da nan kuwa na kama ciki na na hau karanta

"Bismillahi bismillahi bismillahi A'udhubi izzatillahi wa qudiratihi min sharri ma ajidu wa uhaziru, " sau bakwai, sannan na yi fatiha qafa bakwai a ruwa na shanye, ban jima ba na hau zufa bacci me dad'i ya d'auke ni, ban farka ba sai wajejen la'asar, ina tashi kuwa maqociyar mu ke tambaya ta,

"Yaushe rabon da ki ga al'adar ki?"

Tinani na d'aga kai na ina yi, can na ce mata,

"Kafin wannan watan da muke ciki yau wata hud'u kenan bana ganin al'ada ta"

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un"

Shine abinda Maman Ihsan ke maimaitawa cikin damuwa, nan da nan nima na ji damuwar ta bi ta kama ni, me ke faruwa ne?Allah dai ya sa ba wani mummunan abu bane ya same ni, hawaye ne ya fara zuba a Idanu na, kamar daga sama na ji ta ce min,

"Kin sanar da Mama?"

Gyad'a mata kai na yi alamar ah ah,

"Ya salam,tashi maza ki je gida ki sanar da ita abinda ke faruwa dan a dauki mataki tin da wuri kafin ya girma"

"Menene zai girma?"

*Tooo makaranta ku biyo ni a Wattpad domin jin yanda Mahreen ke yin gwagwarmaya a rayuwar ta da dangin miji, rashin haihuwa da kuma kishiya*

Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love 💕 all.

MAHREEN Where stories live. Discover now