Alhaji Muhammad mutum ne shi mai adalci a tsakanin matan shi da yaran shi da qannen shi, mutum ne mai tsananin ladabi da biyayya ga mahaifiyar shi wadda ta rage masa bayan rasuwar mahaifin shi, da zaka tara matan Alhaji Muhammad da 'ya'yan shi a d'akuna daban-daban ka tambaye su shin wa Baban ku ya fi so da qauna ne a cikin ku? Kowannen su zai ce Maka shi/ita, haka abun yake wajen iyayen mu mata, zama kowa ya San ba a rasa samun saba'ni to tabbas muma a gidan mu akwai irin saba'nin da ake samu tsakanin harshen da haqori, in Kuma an samu cikin iKon Allah komai ya na daidaituwa ba tare da an samu rarrabuwar Kai ba.

Saboda tsananin yanda yake tsaida adalci a cikin iyalan shi kowa abin so ne a wajen shi, dan haka ni MAHREEN Ina bada wannan labarin ne da kwatankwacin soyayyar da Baba da Mama suka nuna min.

Tin Ina qarama ta iyaye na ke fama da d'awainiya ta na kasance an haife ni da nakasa ta gurgantaka, inda qafafuna suke da matsala ta yanda ba na iya tafiya d'aya biyu ba tare da na fad'i ba, wannan abu ya d'aga hankalin iyaye na a wannan lokacin da duk Wani masoyin su, iyaye na basu huta ba har sai da suka yi shige da fice har aka yi min aiki a qafafu na dika biyun a nan garin kano, Dr. Shaban shine sunan likitan da ya yi min aiki mutumin qasar India,na sha Jin labari a wajen iyaye na yanda likitan da matar shi ke nuna soyayyar su a gare ni da yaba kyau na a Koda yaushe.

Ba a bar 'yan uwa na a baya ba wajen dawainiya da ni musamman babbar yayar mu, a haka har aka gama jinya ta na samu lafiya, nake takawa kamar kowanne d'a Mai cikakkiyar lafiya.

Na taso yarinya Mai kazar kazar da shiga ran mutane duk Wanda ya ganni sai ya ji dama wannan 'yata ce ko qanwa ta ko Kuma dai ya zamana Ina tare da su, saboda chubby yaro na da ban sha'awa a ko Ina.

Hakan ne ya yi sanadiyyar zama na a gidan qanwar Babana da nake kira da Goggo, Goggo na ta na so na hakan ne ya sa ta roqi Baba da ya bata ni ta riqe ni,duba da cewa Allah bai azurta ta da haihuwa ba a lokacin nan, dan haka ba tare da Wani tunani ba ya shawarci mama ta tattara min kaya na aka Maida ni gidan Goggo na da zama, mijin Goggo na Alhaji Nafi'u mutumin kirki ne Wanda ke son Yara Allah bai nufa zai samu nashi na kan shi ba, Goggo na na da kishiya wadda muke Kira da Baaba, Allah ya yi masa rufin asiri a wannan lokacin ya na riqon Yara uku a gaban shi kafin na je na zama ta hud'u, duk Wani Jin dad'in duniya daidai arziqin shi, Alhaji ya na wadata mu da duk abinda muke so, musamman ni da nake Qarama a gidan, na taso wajen Goggo na cikin kulawa, kishiyar ta da Kuma mijin ta Suna so na matuqa, inda ta bangaren Goggona kuwa kwata-kwata bana Jin dad'in zama da ita, a cikin zuciyar ta na tabbata akwai soyayya ta, amma a halayen ta da ayyukan ta babu wannan soyayyar, kowa ya shaida cewa ni yarinya ce ba mai qiriniya ko rashin ji ba, bana manta wa saboda haka kaka ta Hajiya Innah ke Kira na da Salihar baiwa,amma dik da haka ban samu tarairayar Goggona yanda ya Kamata ba, duk da cewa ba a rasa wasu lokutan da take kula da ni amma rashin kulawar shi ya fi yawa,ana haka muka samu matsala mai girma har ta Kai ga ta karya min hannu na na dama, mahaifi na ya yi kawaici dik da ran shi ya yi masifar b'aci, ya bar ni ta ci gaba da riqo na be karb'e ni ba, kwatsam da Allah ya kawo rabuwar mu da kan ta ta d'auke ni ta Maida ni gidan mu, wajen mahaifiya ta wadda ta cire rai da yakice soyayyar da take min duba da cewa bana gaban ta, ana Maida ni gidan kuwa ta sa hannu bibbiyu ta rungume ni na ci gaba da zama cikin 'yan uwa na cikin farin ciki da so da qauna.

Ba a jima ba Kaka ta ta wajen Uwa wadda muke Kira da Hajiya Innah (Allah ya miki rahama ya sa kina cikin ni'imar shi) ta d'auki riqo na itama, na taso a wajen ta cikin tsananin gata da kulawa, bata so ta ga b'acin raina ko kad'an, gatan da ta bani bai sa tarbiyya ta ta gurb'ata ba, domin ita macece Mai kula da tarbiyyar yaran unguwa ma balle nata, zama na da Hajiya Innah zama ne da na yi shi Mai aminci har na gama makarantar primary ta islamiyya da mahaifin mu ke Saka mu wadda take a Fagge Mai Suna Simarul qur'an, a lokacin da iyaye na da kaka ta suka ga Ina ta girma bana zuwa makarantar boko sai suka yanke shawarar na koma gidan mu da zama inda za a Sanya ni a makarantar bokon da 'yan uwa na ke zuwa, wannan shi ne dalilin dawowa ta gidan mu da zama, kafin a Sanya ni makaranta sai Allah ya kawo wa babbar yayar mu miji ta yi aure a Lagos muka sha bikin Addah Babba suka wuce ita da mijin ta, bayan an kwana biyu da yin auren ne ta roqi mahaifin mu da ya bata ni, Babu bata lokaci kuwa Baba ya bata ni na koma wajen ta da zama.

MAHREEN Where stories live. Discover now