Tinani na ya katse ne a daidai lokacin da na ji Addah Ummu ta ja hannu na muka kama hanyar fita daga gidan namu, a soron gidan muka tsaya muka ga yanda matasa ke biye da bayan Baban mu su na sallah,bamu fita ba sai da suka yi ruku'u sannan muka lallab'a muka Yi sauri muka fita

A hanya Addah Ummu na ta bani labarin Yah Sulaiman mijin da zata aura kenan, Wanda yake d'an uwan mahaifin mu ne, an Sanya ranar auren su ita da Addah Firdous, sai sauraron ta nake Ina Jin yanda soyayya take da dad'i da Sanya nishad'i, se da muka Isa gidan sannan Addah Ummu ta yi shiru da hirar da take min wadda ke jefa ni cikin wata duniya ta mafarki kala kala.

Ina zuwa na tadda an ninke min kayana an daure su a d'ankwali na, gaishe da matar gidan kawai na yi na dauka muka fita dan komawa gidan mu, mu na Isa qofar gida muka tarar da har an idar da sallah Yah Maheer na zaune a gaban Baba su na tattaunawa, Ido ya d'aga ya kalle ni cikin sanyin shi, sannan ya mayar kan Addah Ummu,a tare muka gaida shi, ya amsa muka shige gida,Ina shiga qani na Wanda shi ne autan maza yazo da gudu ya kama hannu na, sannan ya ce,

"Addah MAHREEN kin San me? Yanzun nan na ji Baba da Yah Maheer Suna magana akan ki, Yah Maheer ya ce ya na son ki, baba Kuma ya ce ya amince ya bashi ke amma da sharad'in ya nemi soyayyar ki,domin baya yi wa yaran shi auren dole"

Wani abu na ji Wanda ba zan iya fassara ko menene shi ba,, daga saman Kai na har qafata, jiki na ne ya yi sanyi kamar wata kifin da bai da qashi haka na ke ji na.

Da sauri na shige d'akin Mama Addah Ummu kuwa ta wuce d'akin mu na 'yan mata ta tada sallah, zama na yi a bakin gado da kaya na Ina jinjina girman wannan magana da na ji, na rasa me ma zan yi,shin farin ciki zan yi ko baqin ciki da Jin wannan lamarin da ya tinkaro ni ba zato ba tsammani?

Ya zan yi idan wannan maganar ta tabbata gaskiya ce?

Shine Baba ya bada ni da gaske ba tare da ya ji ra'ayi na ba? Anya yaron nan ya ji me su Baba suka tattauna kuwa? Kaii inaaaa wannan maganar ba gaskiya bane.

Ina tsaka da tinani na ji sallamar Yah Maheer, Mama ce ta shigo d'akin ganin parlourn da duhu dindim ya sanya ta kwala min Kira dan kuwa ta na kitchen ta ga dawowar mu da shiga ta d'akin, bani da wajen zama da ya wuce d'akin ta, dik da cewa mu na da d'akin mu na 'yan mata.

"MAHREEN ko baki ji bane? Ki kawo mana fitila mana, waje duhu qirin haka"

Cikin wata iriyar matsananciyar kunya na d'auki fitilar na nufi hanyar parlour sai dai na kasa qarasawa, Ina nan tsaye a tsakanin parlour da d'aki da Kuma toilet na sake Jin muryar mama na min maganar na qaraso na kawo fitila mana, qafata na ja na qara takun da be fi uku ba, na miqa hannu na na Dora fitilar a saman allon kujera mai cin mutun d'aya ba tare da na fita gaba d'aya na ba, kasa komawa na yi ba tare da na gaishe shi ba.

Cikin murya mai matuqar sanyi na ce,

"Yah Maheer Ina wuni?"

Idanun shi da ke kaina ya lumshe sannan ya saki murmushi ya ce,

"Lafiya qalou MAHREEN, da fatan kin wuni lafiya?"

"Lafiya qlou"

Shine amsar da na bashi na yi saurin fad'awa bayi dan yin alwalar sallar magariba,lokaci ya gama tafiya, Ina shiga na samu waje na sake tsayawa, Ina tinanin maganar wai ni Yah Maheer ke so.

A haka na yi alwala na fita na tada sallah, kafin na idar sun gama gaisawa da Mama da d'an tab'a hira kamar yanda suka Saba, ya fita ya koma can bangaren mazan gidan mu.

Ko da na idar da sallah na jima Ina addu'a, da tinanin shin wannan maganar da gaske ne ko wasa.

Kafff mutanen gidan mu sun tattara sun yi qofar gida, kasancewar unguwar mu sabuwar unguwa ce ba mutane sosai, muka fita mu zauna a waje idan babu wuta mu sha iska gaba d'ayan mu, watarana da iyayen mu, watarana mu kad'ai Yara, tinda alhamdulillah gidan mu muna da d'an yawa ba laifi.

MAHREEN Where stories live. Discover now