HAR ABADA
Alƙalamin: Mukhtar M Nafseen
(Abou Aleey).
*Da Sunan Allah mai mai Rahama mai jin ƙai.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata gun Allah maɗaukakin sarki, wanda ya bani lafiya sannan ya bani damar rubuta muku wannan littafin.
Allah ya ƙara dubun salati a gun mafificin halitta shugaban Al'umma, Annabi Muhammad (S. A. W), da Ahlin sa da sahabban sa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin Alƙiyama.*
*Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu da zai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda ka bani damar fara rubuta wannan littafi lafiya, Allah kabani ikon gamashi lafiya, kura-kuran da zanyi ciki Allah ka yafe min da wanda nasani da wanda ban sani ba*.
SADAUKARWA.
Na sadaukar da wannan littafi ga duk ɗaukacin masoyan dake a cikin wannan duniya tamu, walau Bahaushe ko wata Ƙabilar daban, tare da duk wani maraya, maras galihu dama sauran talakawa gaba ɗaya.
Wannan littafi ƙirƙirarre ne, bai faru da gaske ba, duk wanda yaji suna, ko wani abu wanda yayi daidai da rayuwarsa to yayi hakuri.
Allah ya ƙara zaunar da ƙasar mu lafiya.
1 - 2.
Kamar kullum yau ma a gajiye suka fito daga lectures ɗin, jiki ba kwari ta fito zuwa harabar makarantar tana ɗaura niƙab ɗin da ya ke hannun ta, ɗaya daga cikin matan da suka fito tare ta dafa ta ta na cewa,
" Jamilah manyan gari."
Ta waiwayo tana kallon ta cike da mamaki.
" Rufa min asiri Fa'iza, ai wannan sunan sai ku, mu kuma sai dai mu kasance yan koran ku."
Ta ƙarasa maganar tana maida kallon ta ga hanya, murmushi ita ma Fa'izar ta yi, suka cigaba da jerawa har suka isa bakin hanya suna jiran abin hawa.
Jamilah mace ce mai matsakaicin jiki, bata da tsayi sannan ba gajera bace, kyakkyawa ce mai tsarin zubin fuska, farin ta ba mai yawa bane, saidai da ka ganta kasan ba a jinsin baƙaƙe ko chocolate ta ke ba, tana da dirarren jiki, sai dai ciwon da ke damunta shi ya janye kaso mafi tsoka na cikar jikin sai sirantar da kana kallonta zaka fahimta, tana da manyan idanu waɗanda a koda yaushe sune suke ƙara jan samari zuww gareta, saidai kash ita sam soyayya bata a cikin ranta.
Ita ko Fa'iza fara ce sosai, domin kallo daya zakayi mata ka gano jinin fulani a tattare da ita, bata da ƙiba, amma tana da tsayi Masha Allah, dan har ta ɗan gota jamilah da kaɗan, tana da fara'a, sannan tana da saurin sabo da kowa, hakan yasa a set dinsu kowa nata ne a department.
Duk da yamma ba tayi sosai ba, biyar ne da rabi( 5:30pm), hakan bai hana wahalar samun abin hawa ba, kusan mintina goma sha biyar suna nan tsaye, kafin daga bisani suka samu, sai dai wurin mutum ɗaya ne. Fa'iza ta kalli jamilah tare da nuna ma ta napep ɗin tana cewa.
" Ki shiga tunda kin fi ni nisa, nasan bazan daɗe ba nima zan samu."
Ba dan ta so ba ta shiga, sai dan kar Fa'iza ta ji ba daɗi, haka ta wuce suna ɗaga wa juna hannu.
Kusan tafiyar mintina ashirin sukayi sannan aka sauke ta, ta cire kudi a jakar ta ta miƙa wa direban ta juya ta nufi gidansu na marayu cike da gajiya.
A bakin ƙofar ta gaida Baba Habu me gadi, cikin fara'a ya amsa mata ya na yaba tarbiyyar ta. Ya na da tabbacin kaf 'yan matan gidan babu yarinya mai sauƙin kan ta, kuma kullum cikin yi mata addu'a yake akan Allah ya bayyanar mata da iyaye ko dangin ta.
Cikin gidan kuwa, Jamilah na shiga ta tarar da Abbas zaune yana wasa da ƙaramar ƙwallon sa, yaro ne da bai wuce shekara ɗaya da rabi ba, shi ma wasu bayin Allah ne suka tsinto shi a bakin hanya tare da takardar da ake sanar da duk wanda ya tsince shi ya kaishi gidan marayu, Jamila ita ce uwar riƙon sa, domin tun ranar da aka kawo shi taji tana matuƙar son shi, ita ce ta zaɓa mai suna, sannan ita ce mai kula da duk wani lamarin shi.
Niƙaɓ ɗin fuskar ta ta cire tana ƙara ƙawata fuskar ta da murmushi, Abbas ya miƙe da sauri yana ƙarasowa gabanta ya na bude baki alamun murna yake yi da dawowar ta, duƙawa ta yi tareda buɗe masa hannu, ya shige jikin ta, tare da shi ta miƙe tana kakkaɓe masa ƙurar jikin sa, sannan ta nufi ofishin shugabar da ke kula da gidan.
A bakin ƙofa tayi sallama, saida aka amsa tare da bata izinin shiga sanan ta tura ƙofar ta shiga, sai da ta samu wuri ta zauna tare da ɗaura Abbas a cinyar ta, sanna ta ɗaga kai ta soma gaishe da Hajiya Zainura cikin girmamawa, ita ma cikin mutuntawa ta amsa, tana buɗe firij ɗin da ke dab da ita ta dauko gorar ruwa mai sanyi ta miƙa mata.
Cikin jin nauyi ta karɓa tana cewa, " na gode umma" cikin kulawa Hajiya Zainura ta ce.
" Yi maza ki je ki dauki abincin ki, kafin sauran yaran nan su fito daga makaranta ki kasa sukuni."
Murmushi ta yi mai sauti tana miƙewa, sai da ta ƙarasa bakin ƙofar fita sannan ta ce, " Umma ai su ne farin cikin mu, sune dangin mu, ba mu da waɗanda suka fi su."
Ta ƙarasa ficewa tana dariya, Hajiya Zainura ta sauke ajiyar zuciya, tana kara jin son yarinyar har cikin ranta, sam ba ta da hayaniya tun yarintar ta, tana da sanin ya kamata da kyawun lafazi a duk maganar ta, sosai take tausayin yarinyar ko dan lalurar ta, wacce ke tashin mata lokaci zuwa lokaci. Sauke ajiyar zuciya tayi, tare da miƙewa ta soma harhaɗa abubuwan buƙata, sannan ta rufe office ɗin.
Can ƙasan bishiya ta hango Jamila zaune a kan tabarma, sai Abbas a gefe da gani ka san Abinci ta gama ci tana jiran ya faɗa mata. Ganin Hajiya Zainura ta fito, ya sa Jamila miƙewa ta nufe ta tare da amsar jakar hannunta ta nufi mota ta buɗe gidan baya ta ajiye mata sannan ta rufe ƙofar, makullin office ɗin ta miƙawa Jamila lokacin da ta ke shiga cikin motar, cikin ladabi ta amsa, dan ta san me hakan ya ke nufi, sai da safe ta yi wa Hajiyar, sannan ta matsa gefe lokacin da motar ke silalawa, wurin da take zaune ta koma tana kallon bakin ƙofa har motar ta fice gaba ɗaya mai gadi ya rufe garejin gaba ɗaya.
Shida da kwata (6:15pm) daidai aka tashi sauran yaran daga makaranta, cikin ihun murna mafi yawan su suka nufo inda take zaune, kowa da abin da ya ke son faɗa mata, bakin famfo ta nuna musu inda aka ajiye butoci, mazan ne suka fara zuwa, saida suka gama sannan matan ma suka miƙe, tabarmar ta naɗe ta ɗauki Abbas a kafaɗa suka nufi ɓangaren mata tare da tawagar ta, dan tasan matasan gidan suna gab da soma shigowa da zarar an idar da sallah.
Harabar ɓangaren su babu kowa, alamun yawanci duk suna cikin ɗaki, ɗaki bayan ɗaki haka tabi ɗakunan suna gaisawa da 'yan uwanta bayan ta tura yan mazan masallaci, sauran 'yan matan kuma ta sanya yarinyar da suke ɗaki ɗaya ta jasu salla, tun da alamu sun nuna alwala tayi.
Saman katifa ta ajiye Abbas tana kwanciya a kai cike da tausayin rayuwar su, shi kenan su ba su da 'yan uwa, ba su da dangin da za su yi tinƙaho da tutiya da su, ta cire rai ta sawa ranta HAR ABADA ba zata haɗu da wani ahalin ta ba.
Hawaye masu ɗumi suka zubo mata, tasa hannu ta goge, tana tashi zaune, jin ƙirjin ta ya soma yi mata nauyi yasa ta miƙe ta fice zuwa harabar bangaren, yara ta tarar saman babbar tabarma, kitchen ta nufa tare da kiran masu ɗan girma a cikin yaran, abinci ta zuba a babban tire, guda biyu kamar yanda aka saba, ta ba wa yaran akan suje su ci, ci gaba tayi da aikin gyara kitchen ɗin har ta gama, sanan ta fita jin ana kiran sallar isha'i.
Ko da ta koma ɗakin ruwan wanka kawai ta haɗa, sai da ta fara yi tukuna ta yi wa Abbas, kayan bacci ta saka mai, sanan itama ta shirya cikin kayan baccin ta ɗaura babban hijabi a sama.
Babbar harabar gidan ta fita, inda ɗakunan masu kula da gidan yake, waɗanda su ne suka kasance tamkar iyaye a wurin su, ɗaki ɗaki ta bi tana gishe da su, sun nuna jin daɗin su, domin ganin yanda Jamila ta ɗauke su iyaye, kuma take basu girma yanda ko ɗan cikin su iya abinda zai basu kenan.
Bayan ta baro can, cikin yan matan ta koma Abbas da ke kafaɗarta har ya soma gyangaɗi, zaman hira aka dasa, kowacce da abinda take fadi, wani abin tayi dariya wani abun kuma sai dai ya ba ta mamaki, yaushe suka san waɗannan abubuwa, ita dai bakin ta gum.
Ganin tana da ajin safe yasa ta miƙe tayi masu sallama ta wuce ɗaki, sai da ta sa sauran ƙananan yaran suka je suka kwanta, Sannan ta shiga daki, Abbas ta sanya wa famfas ta kawantar da shi, ƙofar dakin ta tura amma ba ta rufe ba kasancewar Amina ba ta shigo ba, hijabin jikin ta ta cire, ita ma ta kwanta tana yin addu'ar kwanciya bacci, ji take yi yau ba za ta iya karatun ba, bata dau wani dogon lokaci ba bacci ya ya dauke ta cike da begen ahalinta can ƙasan zuciya.
#Abou Aleey.
YOU ARE READING
HAR ABADA
Short StoryBan cire rai ba, ban kuma yarda zuciyata ta karaya ba, kowanne ɗan Adam da kalar ƙalubalen da yake fuskanta a rayuwarsa. Soyayya! Soyayya!! wannan halitta ita ce ƙaddara ta, ita ce ke shirin wargaza ɗan ƙaramin mafarki na, sam ba ta yi min adalci ba...
