su Adda Dariya suka fara wa Haleesa dan sosai take zuba santin sama nata ne gashin, duk kuwa da cewa suma sun cika sa matsanancin mamakin yarda Yarinyar ta tara abubuwa da yawa, na daukar hankali.

            gyaran gashin aka shiga yi mata, cikin kankanin lokaci aka gama, dan gashinta yana da taushi kamar na jarirai gashi da suɓi uwa-uba bashi da cunkushewar nan,a yaryare yake, duk kuwa da cewa yana da yawa amma bai cunkushe ba, bayan an gama Adda ta bada Ribbons guda huɗu aka daure mata kanta dasu.

         izuwa lokacin idanun Nazlah sunyi jaa, dan gaba daya hankalinta ya fara tashi da yarda ake jaan gashin kan nata , dan bata son abun da zai taɓa kan, dan ma tana jin kunyar su Adda ne ba zata iya musu, musu ba da tuni ta mike .

           lokacin kuma Yan taya mai shagon aiki suka zo, umarnin fara hakafarawa ta basu, hakan yasa suka farawa su Adda Zainab, Nazlah kuwa Abin ci Adda Zainab ta sa aka kawo mata , ta zauna chan  bayansu suna ci ita da Yar Adda Zainab.

             ba a dau wani lokacin mai yawa ba, aka gama musu dan nasu bai dauki lokaci kamar na Nazlah ba dan wankin kai ne kawai da wankin ƙafa, bayan sun gama, suka tafi gidan su Nazlah gaba daya, lokacin Yan Uwan Iya duk sun hallara gidan ana ta hada ², ana gyaran kayan miya da sauran kayan Abinci.


.

           Tara ta mutunci aka musu , aka kawo musu Abin ci da Lemu wanda Iya ce ta bada aka karɓo musu, bayan sun gaisa suka bawa Ummu haƙurin kayan lefe da ba'a kawo ba, sai taje chan zasu bata kayanta, murmushi  Iya tayi tare da ce wa "Ba komai ai gwara ma da baku kawo ba kuka barshi chan, dan wahala za'a sha sai an kawo kuma a mayar", basu wani jima ba sosai suka tayi suna godiyar karamci irin na Yan gidan.

           Washe gari, Nazlah da rigama ta tashi,wanda hakan ya haddasa mata zazzaɓi , sai dai Iya ce ta dauketa zuwa gidanta, domin chan ne mai rangwamen  hayaniya.

        Tun 10 mutane suka fara daddala, zuwa gurin daurin Auren duk kuwa da cewa ba wata Gayya sukayi sosai ba, dan Bangaren su Nazlah Yan uwa kawai suka gayyata, Chan gidan Ango ne suka yo gayyatar mutane, 12 bata  ƙarasa ba Adda Zainab da Haleesa da Hameed duka zo gidan .


            lokacin da Hameed ya fito, ya yi mugun mamakin ganin Abokanshi a ƙodar gidan , dan shi kanshi jiya yaji zancen Auran, bai kuma fadawa kowa ba dan har Sadiyya bai faɗa mata ba, gurinshi duk suka tattaso suka zo, Khalil ne ya dan duku ƙafadarshi yace "Buddy ashe dama shirin shigewa kake daga ciki, amma ka bari ciwo zai kashe ka, amma wallahi ka shammace ni,kawai sai dai Invitation card naga yana yawo a media , na nemi wayarka kuma shiru ba'a samunka", dafe kanshi ya yi, tare da  cewa "yi hkr pls kasan yana yin abun ne sai a hankali, dadin media din kenan ai, amma naji dadin ganin ka wallahi, na gode maka".


               Ammar ne ya dan duki kafadarshi daga baya yace "mu da baka ji dadin ganin mu ba, ba komawa zamu yi ba ai", juyawa ta yi, yana dariya suka rungumi juna, fira suka ci gaba dayi irin ta Abokai, Adda Zainab da Haleesa kuwa tuni suka shige ciki.


               Ko da suka shiga ciki ,cikin  girmamawa ake gaishesu har ƙasa, har suka shiga Ɗakin Ummu da take cikin shiga mai kyau shar³ da ita sai murmushi take, nuna wa Adda Zainab kusa da ita tayi, zama tayo suka gaggaisa, fira suka shiga yi da dangin Iya, da yake duk fara'a garesu ga saurin sabo yasa, suke firarsu cikin jin dadi, da tattauna yarda zancen Auren yazo, Haleesa ce tace "Ummu ina Amaryar Auta,da Iya?, naga ban gansu ba", dan murmushi Ummu tayi tare da cewa "Suna gidan Iya ko asa a raka ki chan din ?".


          dan gutun murmushi tayi tare da ce wa "Laaaah Ummu nasan gidan bari na je", ta fada tana mikewa, Amsar Yar Adda Zainab tayi ta fice da ita zuwa gidan Iya.


You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 12, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NAZLAHWhere stories live. Discover now