tun shigowarsu cikin Unguwar, tasan da zuwanshi, dan jiniyarsu ma kaɗai ta isa ta sanar da ita, bayan hargowar mutanan Unguwa da sukeyi na murnan ganinshi, tana jin karar dirar motarshi cikin gidan ta mike ta nufi ƙofa,  cikin farin ciki , kafin ta ƙarasa ya danna belt dib da yake jikin kofar.

         da Sassarfa ta karasa zuwa gurin ƙofar, tana budewa ya fada jikinta, tare da sauke numfashi mai nauyi, cikin siririyar muryarshi mai amsa amo yace "Miss you so much Maa", shafa kanshi tayi, tare da sakar mishi wami ni'imtaccen Murmushi wanda a fuskar Mahaifiya ne kawai ake samushi , ta sakar mishi , tare da cewa "ya hanya ?", kanshi ya daura akan kafadarshi, tare da cewa "Alhamdulillah", jaan hannunshi tayi suka fara takawa izuwa cikin palon gidan, zaunar dashi tayi akan kujera, tare da zama gefenshi tana kallon.


         cike da mamakin ramar da ya yi, tace "Muhammad", a hankali ya Amsa mata cikin sanyin murya, taɓa kashin wuyanshi tayi tare da cewa "me ne ne wannan, ciwo kayi ne", ta fada tana zazzaro idanu.


         Siririn Murmushi ya saki , tare da cewa "Qlau nake Maa, kawai yana yin aiki ne ba hutu", jinjina kanta tayi bawai dan ta yarda da cewa aiki ne ya sanyashi rame ba ,haka sai dai in wani abu, amma da yake bata son sanya wani abu tsakaninsu yasa tayi shiru.



           Shafa cikinshi da yake mishi kuka , ya yi tare da kallonta yana kwaɓe fuska, alama ta mishu da ido alamar me ne ne , cikin muryar Shagwaɓa da Sakalci yace "I'm feel hungry", fa fada yana yamutsa fuska.


           kama hannunshi tayi suka nufi dinning room , tare da cewa ,  "ai dama komai an gama kai ake jira, " ta fada tana jaa mishi kujara, zama ya yi, yana kallon coolers din da aka jajjera akan dining din, zama tayi kusa dashi, tare da bude wata babbar cooler , haɗɗaɗiyar fried rice ce ta bayyana, wadda kallo daya zaka mata kasan ta hadu saboda yarda take daukar ido da yarda tayi kyau, tasha kayan haɗi sosai.

      zuba mishi tayi kafin ta kara bude wata cooler farfesun kifi ne ya bayyana a ciki sai kamshin kayan kamshi yake,  ya yi kyau shima, cikin dan bowl ta zuba mishi, tare da kara bude wata cooler tuƙƙaƙen tuwon Shinkafa ne  , ya bayyana, zare ido ya yi , ganin zata zuba mishi.

        kwaɓe fuska ya yi, tare da cewa "ni da wa?", harararshi tayi, tare da cewa "kai da wanda ka gani a kusa" ta fada tana ƙoƙarin zuba mishi, da sauri ya rike hannunta tare da cewa,"wannan ma is okay ", ya fada yana sanya spoon s ciki, cikin natsuwa ya fara ci da Bissimillah dauke a bakinshi.


        tun da ya fara ci, baiyi magana ba, har ya tsame spoon din daga cikin Abincin tare da furta "Alhamdulillah", kallon shi tayi da mamaki ƙarara akan fuskarta, "mai kake nufi?", ta fada tana kallonshi.


       kwaɓe fuska ya yi, tare da cewa "Allah kuwa na ƙoshi", ya fada yana kwantar da kanshi akan kafadarta, "Baka cin Abinci shi yasa ka rame ka lalace haka, to ba zan lamunta ba, maza² dauka kaci kafin na ɓata maka rai", ta fada tana haɗe fuska, shiru ya yi, dan baisan kuma mai zai kara cewa ba, dan ya mugun ƙoshi.

      ganin ya yi shiru, yasa ta dauki Spoon, ta dibi abin cin ta fara bashi, bai mata musu ba ya bude baki, baifi 3 spoon ba ya fara kakarin amai, a dan tsorace ta jaan ye hannunta, daga kan spoon din, mikewa ya yi, da sauri ya nufi toilet din dake cikin dinning room din.

      kafin ya ƙarasa shiga, aman ya taho mishi, da sauri ya duƙa ƙasa, ya fara kwarara amai, a dan tsorace ta biyu bayanshi, duƙawa tayi kusa dashi, tana shafa bayanshi, tun yana aman cikin hayyacinshi, har ya fita a hayyacinshi, aman ma har ya koma babu komai cikinshi, sai kakari da wahala.


      dakyar aman ya tsaya, wanke mishi bakinshi, tayi ta kamashi suka fito palo, zaunar dashi tayi akan kujera, tare da zama, kanshi ya daura akan cinyarta ,yana sauke numfashi, ganin yarda yake yasa Nadama saukar mata, tasan tun yana Karami in har yaci Abin ci da yawa to karshenshi sai dai ya Amayar dashi, bacci ne ya dan daukeshi, baiyi ko 3  minutes yana baccin ba ya farka , a hankali ya fara bude idanunshu, har ya budesu tarrr akan fuskar Hajiya , da sauri tace "Sannu ya jikin naka", ta fada cikin tausayawa.

NAZLAHWhere stories live. Discover now