CHAPTER 5-6

Depuis le début
                                    

                   tana fita da wasu yan mintuna, sai ga jiniyar motarsu Hamid mikewa Sadiyya tayi daga in da take, yana bude kofar ta nufi in   da yake, mamaki ne ya cikashi na ganinta da kaya da ya fita ya barta dasu,sanan palon kacha-kacha da alama bata gyara komai, fadawa jikinshi tayi tare da cewa "Welcome back My Solder", wani ƙarin rana ne ya daki hancinshi, numfashinshi ne ya tsaya chak na tsawon lokaci kafin ya ci gaba da aiki, da sauri ya matsa da ita daga jikinshi ya wuce sama...............



                 da sauri ta dauki wayarta, ganin Jamseey ta turo mata sako yasa ta bude voice note din sai da ta gama saurara ta mayar mata da amsa kafin tace, "ban fada miki ba My Solder ya dawo yanzu, mai kike ganin ya kamata nayi", dariyar kyeta Jamseey ta saki, kafin ta fara cewa, "to yanzu abun da zakiyi, kice kiyi wanka ki shirya, sai kije bedroom dinshi" mikewa tayi ta shiga bedroom dinta, wankan tayi ta shirya tare da cewa, "to na gama gani zanje bedroom din nashi", ta fada tama tura kofar shiga, ko da ta shiga baya ciki,hakan yasa ta zauna kan bed tare da cewa "gani nazo ma  baya cikin bedroom din da alama wanka yake", murmushi ta kara saki tare da cewa, "to in ya fito ki tarɓeshi da salo, ki kwantar dashi ki mishi tausa, sannan ki ringa shafashi sai  ya hau network  ki gudu dan banason ki bashi sai kin wainashi, yarda zai fi rikeki da daraja" dariya Sadiyya tayi tare da cewa "gaskiya ne Ƙawata nagode da shawararki",,tana gama voice note din Hamid na fitowa daga wankan da ya shiga................



                   da sauri ta mike ta taroshi, mamaki ne ya kamashi sai dai da yake shiɗin Namijim duniya ne bai yarda ta gane mamakinshi ba ko kaɗan,tsane mishi ruwan jikinshi ta shiga yi, bayan ta gama ta shafa mishi lotion  vest da boxer ta bashi ya sanya, kallonshi tayi tare da cewa "nasan ka gaji kwanta na maka tausa", ta fada tana kashe mishi ido, ba musu ya kwanta tare da ringinginawa, hannunta ta daura kan tattausar fatar jikinshi ta fara tausa mish a hankali, cikin minutes kadan yanayi ya chanja gaba daya ya fita a hayyacinshi, tana ganin haka ta,zame jikimta tare da ficewa da gudu, ta datse bedroom din ................



                     rasa yarda zaiyi ya yi, hakan yasa ya shiga bathroom ya sakarwa kanshi ruwan sanyi mai sanyi, hakan kuma ya yi dai-dai da saukar ruwan sama mai karfin gaske, wanda gaba daya ya kara dagula mishi lissafinshi................



          **********


            Asubar fari Jaririya ta fara tsanyara kuka, mai matuƙar sauti, da firgitarwa, sai kace wadda ake yankar naman jikinta haka take kukan da ihu , kukan da takeyi kuma shine ya yi sanadiyar tashin Lawan daga bacci,cikin ruwan masifa ya fara kiran "Maryama! Maryama!! Maryama Wallahi ki tashi ki dauki Yarinyar nan ku fita a ɗakin nan in ba haka ba,zanyi ball daku ke da ita,haba wannan wace iriyar masifa ce, kinzo kawai kin haifar wa mutane Yarinya mai masifar kuka, ki tashi ki dauketa nace ko", ya fada yana shurin hannunta, a firgice itama ta farka tare da daukar Babyn ta sanyata a jikinta tana rirrigawa..............



                    tsawa ya daka mata tare da cewa"tashi ki fice ki bat ɗakinan nan da yarinyar nan , kafin na ɓaɓɓalaku ke da ita", a hankali ta mike ta fita da Babyn a hannunta, gefe chan ta samu ta zauna, tare da fara feeding din Yarinyar, dan-danan kakejin Yarinya tayi shiru, sai da ta ƙoshi kafin ta kona cikin ɗakin jikinta na karkarwa kasantuwar  har lokacin lemar da aka kwana da ita na ruwa bai tsane ba, kwantar da Yarinya tayu tare da kwanciya itama, bacci ne ya kara daukarta...................




                 tun 7 Iya tazo ta daura musu ruwan wanka, wannan karon Maryama da kanta tayi wankan Babyn kawai Iya tawa wanka, Maryama na fitowa ta Umarci Haleeem maza yaje ya yi, baya ta gama shiryawa ta fito tare da fara tsaftace tsakar gidan da shara ta fara kafin ta haɗa yan kwanikan wanke-wankensu ta haɗu kunfa wankewa ta shiga yi, sai da ta gama fes ta kikkife, kafin ta fara kiciniyar haɗa wuta, Iya ce ta shigo, zare ido tayi tare da cewa ",duk wa ya yi wannan aikin haka ?", kafin Maryama tayi magana Haleem yace "Umma na ce Iya", zare idanu ta karayi tare da cewa.........



NAZLAHOù les histoires vivent. Découvrez maintenant