Daga chan cikin ɗakin taɓe baki tayi tare da cewa "Sai fa kayi ta yi, dan Wallahi bazan bude ba, kuma kuɗi ma yanzu na fara ƙarɓa", ta fada tana daukar wayarta, latsawa ta fara yi, tana ji yana dukan kofar amma tayi burus dashi...............




            Sai da ya gaji da dukan Kofar , kafin ya koma bedroom din da ya fito, yana jaan ƙafafunshi, yana shiga mata kofa ya nufa, budewa ya yi, haɗaɗan bathroom ne ya bayyana, fadawa ciki ya yi, tare da sakarwa kanshi ruwan sanyi, dukan kashin ruwan ya ci gaba dayi, yana tsaye ko motsi baiyi ba, ya dade sosai a haka,kafin ya fito jikinshi na ɗigar da ruwa, bai damu da ya goge ruwan ba, ya fada kan gado, yana sauke wani numfashi mai zafin gaske, cike da ƙunar rai..................





                    Dayan Ɗakin kuwa, gyara kwanciyarta tayi, jin ya daina buga kofar yasa, tayi kiran waya minutes kaɗan aka dauka, shewa tayi tare da cewa "Ahaayeeeee Naanaye, "murmushi akayi daga chan kafin wata muryar daban ta dakin dodon kunnena, cikin dariya tace "Duniya taki Kawata bani nasha yau kuma da wace kikazo", ta fada cikin sigar Ƙawaye masu kai mutum ga halaka.................





                    dariya tayi tare da cewa, "Ahhaf in da nake sonki kennan , ke da na kiraki kinsan da wata siga nazo miki da ita", "Uhmmm ai sai dai na fadawa wani halinki amma badai a fada min ba, yanzu dai bani nasha" ,,dariya ta kara saki tare da cewa "ai ban baki labari ba yanzun nan mutuminki ya turamin #5000k kuma na gudu na kyaleshi da abunshi, ai daga yanzu na gama yarda ya kusance ni sai ya bani cash, cash dib ma in naga dama ko ya bani na gudu", ta fada tana wani juya kwanciya daga in da take...............





                    Dariya ta sheƙe da ita tare da cewa "Kai wannan abun yamin Suga, kici gaba da gasa mishi aya a hannu, bamce ki bashi ba sai kin gama lale dan Iska, ke ko dattin Aljihu bance ki barshi dashi ba",ta fada cikin maganar mata yan duniya,wanda suka san takan tsiya, dariya tayi tare da cewa "ai dadina dake kina da man kai, yo dama ta ina zan yarda ai ko zan yarda sai na tabbatar da ba samu rabona", haka suka ci gaba da surutansu wanda basu da kai balle gindi, sai shawarwarin banza take bata, ita kuwa sai dariya take tana kara hawa kan motar ƙaiƙai.................







                   Cikin mugun yanayin nan ya kwana, yana murkususu, sai yanzu yake nadamar Auren Sadiyya da ya yi, gashi bata mishi komai,,ko bakutarshi in yazo da ita bata sauke mishi, gashi a rayuwarshi bashi da tsarin yin Aure-Aure balle saki...............






            *WASHE GARI*





            Tun Asuba bai koma bacci ba, dan yana dawowa daga Masallaci gurin motsa jiki ya nufa, motsa jikinshi ya fara yi, kusan 2 hours yana abu daya, kafin ya nufi cikin gidan tana share zufar da take yanko mishi, zaune ya tarar da ita a palo, ta chaɓa Ado cikin wani tsantsareran lass mai kyan gaske, ba wata babba bace dan ba zata wuce 19 to 20 years ba, ba laifi tana da dan kyanta dai-dai gargwado...............



            kallonshi nayi shima din  dai ba zai wuce 27 to 28 ba sai dai yana da garin jiki sosai, dan in ba fada maka akayi ba bazaka taɓa dauka Asalin shekarunshi ba kennan, saboda yana da babban jiki, yana da tsawo sosai gashi da ƙiba sai dai ba irin ƙiba ba sosai dai-dai misali dan ba za'a kirashi mai ƙiba sosai ba sannan ba za'a kirashi ramamme ba, tsaka tsakiya ne, sai dai Allah ya zuba kyau ,dan kallo daya zaka mishi kasan cewa shi cikakken Bafulatani ne, dan fari ne tas yana da matsakaicin baki mai dauke da ƙananan lips masu dan kauri kaɗan , dogon hancinshi har baka, idanunshi dara-dara fsrare tar sai golden Eyes ball da yake da shi, gashin girarshi da na idanunshi gazar-gazar gwanin kyau , Fatabaraqallahu Ahsanun qalikin ,Masha Allah , na furta dan ya haɗu iya haduwa yakai karshe a gurin kyau..............






NAZLAHWhere stories live. Discover now