shafi na uku

599 10 0
                                    

*_GURBIN IDO_*
*Huguma*
*Free page 03*

          Duk wani taku da takeyi tana yinsa ne da taimakon sandar dake riqe a hannunta,a yau madadin sandar ta zame mata ta saita dabbobin da take jan ragamarsu,sai ta zame mata mataimakiya wajen sanya diga diganta zuwa qasa.

       A yau din da baki ta.dinga saitasu tana basu umarni,duk da yadda magana ke mata wuya ainun,duk kalma daya idan xata fitar sai taji kamar kanta zai tsage,sun dan dauki lokaci kafin su isa inda suke qyale dabbobin,kowacce ta ni'imtu ta kums amfana daga rahamar ubangijinmu.

          Tana isa kamar koda yaushe,mabanbantan makiyaya dake wajen kowa ya fara qoqarin tattare dabbobinsa don gudun afkawa ko cakuduwa da nata dabbobin,ba yaune farau ba,nan da anjima kadan ma tana iya ganin wajen babu kowa sai ita daya da nata dabbobin,abune data saba da ganinsa,canfi ne da suka riga suka dasawa ransu,wanda batasan ranar da zai goge ba,hakanan babu me cire musu shi sai mahaliccinmu.

           A yau dinma bata damu ba kamar kowanne lokaci,bayan ta tabbatar da sun iso inda ya dace,saita fara zame jikinta daga cikinsu,tana wara manya kuma fararen idanunta da kalarsu ta jirkita saboda zafin ciwo dana zazzabi,tana neman inuwar da zata dace da ita.

          Babbar bishiyar mangwaro ce,mai yawam sanyi da kuma inuwa,wadda bata da wani tsaho.mai.yawa amma sai yawan 'ya'ya,daga nan inda bishiyar take basu da nisa da inda zata hangi dabbobinta,hakanan ba nisa da inda zata gangara dasu susha ruwa da zarar lokacin hakan yayi.

          A hankali ta zame malafare(hular kaba da suke amfani da ita" ta ajjiye a wajen,duk da hular ba nauyi gareta ba,amma sai takejin kamar ta dora wani dutse saman kanta,ta zare jakar dake qugunta itama ta ajjiyeta,da zata iya kwanciya zatayi,amma tana jin nauyin sallar da batayi ba takai mata ko ina,don haka ta juya zuwa sashen da ruwa ke gudana,ta daura alwala ta dawo ta tada salla saman dankwalin kanta data cire ga yane kanta da mayafin da akoda yaushe bata rabo da yafashi,duk kuwa da cewa baqon abune cikin al'adarsu,zata iya cewa ma kaf fadin rugar ita daya ce cikin matasan yara masu shakaru irin nata dake amfani dashi.

"Maimunatu!.....maimunatu" da sauri ta daga kanta daga durquson da tayi masa,tana ware idanunta cikin matuqar kaduwa da razana,murya mafi muni da razanarwa a wajenta.....muryar da mamallakin muryar abubuwane da tunda take a rayuwarta bata taba jin abinda ta tsana cikin duniyarta sama dasu ba

"Yaushe ya dawo?" Ta jefawa kanta tambayar tana wurga idanunta don tantance daga wanne bangare yake dosota.

          Daga can nesa ta hangeshi,tsabar kauri da qarfin muryarne ya sanya ta dinga jinta kusa da ita kamar yana gab da ya cimmata,qasa tayi sosai don kada ya hangota,sannan ta miqe a hankali,ta tattare dankwali hula da jakarta waje daya ga wurga saman bishiyar da take zaune qasanta,karo na farko da tayi ala wadai da rashin iya koyan hawa bishiya irin nata,saita saita mayafinta ta lullube jikinta da kyau,sannan ta zagaya ta bayan bishiyar ta lafe sosai a jikinta,ta yadda zata iya hangoshi,zuciyarta na wani buguwa ɗik ɗik,tana cike da fata da kuma addu'ar rashin samun sa'ar ganinta.

      Dube dube da waige waige ya shiga yi,yana kuma sake qwala mata kira iya qarfinsa,fuskarsa a firgice da alama ya zaqu da son ganin nata,bai kuma tsammaci rashin samunta a wajen ba,dube dube yaci gaba dayi,yana sake kiran sunan nata dai,har zuwa sanda ya sare,jikinsa da zuciyarsa kuma suka gaya masa bata a kusa

"Kayyasa" ya fada da kaushin murya,yana kaiwa bishiyar dake kusa dashi karta da wani kakkaifan abu dake hannunsa,da sauri ta zame kadan saboda gudun samuwar ciwo a jikinta,saura kadan kartawar da yayi ta hada da tsintsiyar hannunta,ta dauke numfashinta cak sanda yake sake takowa da baya,sai kuma ya dura wata ashariya,yasa giyaa zuwa gaba ya taka ya fara barin wajen.

          Bin bayansa tayi da kallo farincikin boye masan da tayi yana saukar mata,kwata kwata kuma ko sau daya bata taba yiwa buderi kallon mutum mai hankali ba,hasalima tsoro yake bata ainun,buderi kenan,baqin bafulatani na usul,wanda ke ciie da wasu irin baudaddun halaye na wauta jahilci da hauka,irin nau'in haukan da jahilcin ne ke haifar dashi,zuciyarta cike take da mamakin me yasa shi din baya gudunta kamar yadda sauran samarin qauyen ke gaza rabarta bare su furta mata kalmar so?,me yasa shi bai gujeta ba?,ta jima tana yiwa kanta wadan nan tambayoyin.

GURBIN IDOOnde histórias criam vida. Descubra agora