1

2.4K 109 10
                                    

MALAYSIA (SABAH)

..........A hankali sautin kukan ke tashi tamkar mai rairashi da gayya. Sai dai daga jin yanda salonsa ke fita kasan tsabar daɗewar da maiyin nasa ya ɗauka yana yine ya kaisa ga galabaita. Kasa jurewa nai na kutsa kaina cikin gidan madai-daici da ke ɗauke da dukkan kayan more rayuwa najin daɗi. Falo ne babba masha ALLAH, sai dai duk girmansa banci karo da kowa a cikinsa ba. Shiru nai alamar tunani, (to ta ina kenan sautin kukan da yaja hankalina ke fita?) rashin mai bani amsa ya sani fara waige-waige a falon. Tabbas ba'a nan ɗin bane, hakan ya sani kutsa kaina dan zuciyata ta banni tabbacin a window da naji kukan ɗakine.
            Takun sakkowa da stairs ɗin da'aka kawata adon falon da shi ya sani maida hankali can. Hamshaƙiyar mace kamila mai yanayi da fulanin ƙasar Nigeria ce ke taku cike da nutsuwa da kamala tamkar yanda shigarta ta kamala ta ƙawata mutuncinta ga mai kallo. Sam banyi zaton ko (zo na kasheki) ta sani da yaren hausa ba, amma a mamakina saina tsinkayi kamilar muryarta na ƙwala kiran sunan *_Anam!_* a ɗan kausashe. Ƙara kausasa muryarta tayi ganin babu alamar wadda take buƙatar ganin data kira da suna Anam ɗin ta fito.
         “Anam! Idan har kika bari na shigo inda kike ki tabbatar sai jikinki yayi tsami kafin kibar ƙasar nan. Shashasha kawai wadda bata kishin kanta. To banda mara kishin kai wake ƙin tushensa? Ba kukan hawayeba kiyi na jini ma babu fashi zuwa Nigeria ki zauna agareki, k idan ma kika ƙuleni ALLAH kin koma can da zama kenan keda ƙasar nan sai yawo”
      Sautin kukan da aka sake fashewa da shi ya sani waigawa da sauri, ƙyaƙyƙyawar budurwa black beauty mai ɗaukar hankali da sam bata kama da matar a yanayin jiki sai na kamannin jini kaɗan. A ƙiyasi na yanayin jiki kai tsaye zance bata wuce shekaru sha bakwai ba. Sai dai a mizanin hankali da sanin masu irin yanayin jikinsu wajen ɓoye shekaru zan iya karyata zuciyata. Amma kai tsaye ban san shekara nawa zan bata ba. Dan sam bata da wani tsaho, tana nan dai ƴar cif-cif ga karamin jiki ga rashin tsayi kamar wata ƴar kanwata can (😂🤣ban dai faɗi suna ba ato😜). Tabbas kyaƙyawa ce, dan duk da kukan da idanunta suka nuna alamun taci hakan bai hana bayyanarsu dara-dara ba duk da suna a cikin farin siririn gilashi. Ga gashin gira da dogon hancinta (kamar na bilyn Abdull🙄 saura wani yace ba haka ba, bansan jealous😒😜). Kai atakaice dai yarinyar masha ALLAH. Sosai hawaye ke cigaba da bin kumatun ta tamkar an bude fanfo. Matar daketa masifar ta sake zuba mata harara a kausashe tace,
          “Haɗiye min kukan nan kafin nazo na sassafa ki a wajen sakarar banza”.
     Da ƙyar ta shiga ƙoƙarin haɗiye kukan nata. Sai dai hawayen sunƙi riƙuwa. Cikin rawar murya ta dubi kamilar matar da take kamani da ita a ɗan fisge, “Mamie na tuba ALLAH na daina duk abinda baƙwaso ke da Abie ”.
      “Dainawar taki ko cigaba bazai miki amfanin komaiba ai, dan zuwa Nigeria dai babu fashi tunda kin san abu mai muhimmanci ne zai kaiki. Dolene kije kiyi saves ɗinki a ƙasar haihuwarki kodan gaba zai miki amfani, dan nan ɗin da kika ɗauka ƙasar uwa da uba ta aro ce lokaci kaɗan ya rage mu barta muma ta ishemu”.
       Kuka ta sake fashewa da shi tana daddaga ƙafa. “Ni wlhy bana son Nigeria, zafi, sauro ga shegen hayaniya. Ni basai nayi saves ɗin ba dan bazan taɓa rayuwar Nigeria ba balle har na damu dayin aiki saves yaymin amfani. Please Mamie....”
      Cikin katseta Mamie taja wani tsaki. Kota kanta batabi ba ta nufi wata ƙofa a fusace tana faɗin, “Ki wuce driver ya kaiki wajen gyaran jiki dan Abie ɗinki yace da wuri zaku wuce, kin san kuma baya son wasa da lokaci”.
     Kuka ta sake barkewa da shi kai kace Abie ko Mamie ɗinne aka aiko mata sun mutu. Harga ALLAH bata son zuwa Nigeria dan tana matuƙar wahala da yanayin zafinsu. Ga shegen sauro ɗinnan na kano tamakar kasuwancinsa sukeyi. Uwa uba zaman gidan Uncles ɗinta data tsana saboda mugun halin matar Daddy, na matar ma bai cika damunta ba dan sai ka shiga sabgarta take takuraka. Tafi tsanar babban ɗansa mai shegen baƙin hali da mugunta da har ya zarta uwar tasa. Sam bata ko ƙaunar ganinsa dan basa haɗa ko hanya bare shan inuwa guda, shiyyasa a mafi yawan lokaci idan taji zai zo malaysia take guduwa wajen Aunti Mimi. Da ance kuma zai je wajen aunty Mimi ɗin itama dake aure anan ƙasar malaysia ɗin sai ta gudo ta dawo sabah. Har ya gama zamansa bata yarda su haɗu. Kai itafa a kaf rayuwarta ma bai fi sau uku ta taba ganinsa ba. Tun kuma a ganin farko taji ta tsanesa saboda tsawa da yay mata dan ta fasa glass cup a mistake a gidansu, ita kuma ta murguɗa masa baki yako kama lips ɗin ya murje har sai da sukai kumburi duk da shekarunta basu wuci goma ba a lokacin ta kasa mantawa ta kuma kasa daina jin haushinsa. Hakama haɗuwarsu ta biyu sai da yay mata mugunta, kai idan bata mantaba ma dukansu yay ita da Aysha ƙanwarsa saboda sunje wajen bikin birthday na ƙawar Ayshan ba'a sani ba. Aiko dukan nan ya shigeta dan harda zazzaɓi kasancewar tunda ta tashi da wayonta da hankalinta ba'a taɓa dukanta ba sai shi mugu.........
          Ta jima a wajen tana saƙa mai fishsheta kafin ta haura saman stairs. Cikin mintunan da basufi sha biyar ba ta fito sanye cikin wando da riga ta ɗaura jibgegiyar rigar sanyi data kai mata har gwiwa kasancewar lokacinsa ne, duk da veil data naɗo a kanta kamar yanda larabawa keyi hakan bai hanata jan hular rigar da bakinta keda gashi mai laushi har saman kanta ba. side bag dake hanunta ta saƙala cikin wuyanta sai faman tura baki take. Duk da Mamie na zaune a falon tana yanka tufa ko kallonta batai ba....
      “Mamie na shirya kuɗin to”.
Batare da Mamien ta tanka mata ba ta tura mata card ɗinta na ciran kuɗi. “Na gode ALLAH ya ƙara buɗi mai albarka”. Ta faɗa tana kama hanun Mamie ta sumbata tare da ɗagowa ta sumbaci kumatunta kamar yanda dai larabawa sukanyi. Mamie bata kulata ba, hakan yasa taƙi tafiya idanunta har sun cika da kwalla, dan tunda taga Mamien bata maida mata murtanin sunbar datai mata ba tasan har yanzun tana fushi da ita.
       Haka kawai murmushi ya suɓucema Mamie, ta girgiza kanta da kamo hanun tilon ƴar tata da a kullum cikin jimamin ranar da aure zai rabasu take, dan ta tabbatar hakan na gab da faruwa. A ido zaka ɗauka Anam bata da wani shekaru saboda ƙaramin jiki da ALLAH ya bata. Sai dai kuma a zahiri shekarunta ashirin da uku kenan a duniya. Itama sumbatarta tai da ɗanjan kumatunta, hakan yasa Anam yin ƴar dariyar jin daɗi ta rungume Mamien. Mamie tai murmushi.
        “To sarkin taɓara tashi kije ko ƙya dawo da wuri”.
     “Okay Mamie bye”.

BABU SO...Where stories live. Discover now