JUNAIYD ALIE 5

48 9 0
                                    

*JUNAIYD ALIE*

If you feel like you are loosing everything, remember that tree's loses their leaves every year, and still stand tall and waits for a better days to come..... So komai lokacine a Rayuwa, duk rintsi duk wuya karki yanke ƙauna da samun komai a rayuwarki, ki ƙaddara a ranki cewa komai lokacine🥰

         
          EPISODE: 05

Lokaci bayan lokaci Sukan ɗan taɓa hira a tsakanin Sumaiyyah da uncle Zaid, yayinda Suwat tai shiru a bayan mota tana sauraron hirar tasu sama-sama, tana jin kanta tamkar a takure, a haka suka isa gurin dinner ɗin ya samu wuri yay parking.

Sumaiyya ce ta fara fitowa sannan Suwat ma ta buɗe murfin bayan motar ta fito, hannunta Sumaiyya ta kama tana ƴar dariya ganin yadda suwat ɗin take ta faman zare idanu kaman tayiwa Lamiɗon Adamawa ƙarya😁.

Ɗan sunkuyawa Sumaiyya tayi still da murmushi sosai on her face tace " thank you so much uncle Zaid, na tabbata badan kai ba da anyi dinner ɗin nan babu mu ." ɗan wara manyan idanunsa yayi kamin ya buɗe murfin motan ya fito yana murmushi yace,"Your always walcome Sumy danger. Ko kuma ince Ƴar gaban goshin Hajja Lumbi..." yay maganar cikin zolaya

Folding hannayenta Sumaiyya tai on her chest tareda ɗan turo bakinta gaba irin na sangartattun yaran nan ta ce," haba Uncle Zaid da fa da yanzu ba ɗaya bane ba. wllh ni yanzu ba ruwana da rigima da ka ganni, magana ma ba sosai nakeyi ba, amma shine zaka ce min Danger a gaban ƙawata salon ta rainani..."

Dariya sosai magananta ya bashi, don haka walking slowly ya iso gabanta, ɗan ranƙwafawa yayi yanda tsayinsu zeyi dedai dana juna, sannan yasa hannu yaja hancinta har seda tayi ɗan ƙara kaɗan yace,"har Abada bazaki taɓa canzawa daga sunanki danger ba, kaf Familyn Moddibo babu wanda bai san rikicin ki ba, duk bama wannan ba a ina kika samo ƴar mutanan maiduguri haka? Naji tunda kuka shiga motana nakejin ƙamshi mai daɗi"

Dariya sosai maganan shi ya bama Suwat bata san lokacin da wani kyakkyawan murmushi yay escaping lips ɗinta ba, don ta lura mutumin badai son wasa da dariya ba. Kallon mamaki kawai Sumaiyya kebin Suwat dashi, misamman da taga tana mirmushi don tunda take tareda ita bata taɓa ganin tayi irin wannan murmushin ba.

Cikin maɗaukakin mamaki Sumaiyyah ta kalli Uncle Zaid ta ce," lallai Uncle ka ciri tutan da kaf cikin yola town da keyewayen babu wanda ya cira irin wannan tutan se kai, dubi yanda ka sanya Suwat murmushi har seda haƙorinta ya fito, gaskiya Uncle you're so lucky.."

Kallonsa ya mayar ga Suwat sannan ya faɗaɗa Murmushi sa yace,"Ai dole ƴar Maiduguri tamin murmushi tunda ita ɗin baiwa ta ce."

Da sauri Suwat ta kalleshi haka itama Sumaiyyah.

Dariya yay me Sauti sannan yace,"Ai duk inda Barebari Suke to bayin Fulani ne." da sauri Suwat tace,"No Fulani sune bayin Barebari...."

Gabaɗayansu da kallo suka bita cikin tsananin mamakin yanda tayi maganar da confidence, ganin yanda suke kallonta yasa tai saurin ɗora hannunta a saman lips ɗinta, don wllh ita kanta bata san sanda maganar ta subuto daga bakinta ba.

Ganin yanda tai saurin dafe bakinta yasa Uncle Zaid yay murmushi yace,"Suuwat who told you so?"

Ƙasa tai da Kanta tana wasa da yatsun hannunta cikin cool voice ɗinta tace,"Ya gambo ce ta gaya min she always told me that Fulani sune bayin barebari, ba wai Barebari ne bayin Fulani ba...."

Hararan wasa uncle Zaid ya galla mata sannan ya ce" Wace ya Gambo ɗin nan da take zama tana kwashema iyayen gidanta maki?, lallai inaga daga nan Yola zansa aje a kamo min ita, tunda naga ta raina Fulani da yawa tunda take gaya miki abinda ba haka yake ba." ya ƙare maganar yana murguɗama Suuwat baki

JUNAIYD ALIE Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin