Chapter 7-8

29 1 0
                                    

*💥GUNTUN GORO..!💥*

_Zainab habib(Mom Islam_

Free page 7-8

Yamutsa fuska yayi kamar bai san da zancen ba,
Na kawar da maganar tare da cewa "Hajiya dan Allah inason zuwa gurin Abbana"
"Bari driver yazo ya kaiki "
"To "
Nace ina ɗan faɗaɗa fuska da murmishi nabar gurin dama na gaji da harara.
Hijab ɗina na ɗauko kana na fito ina shirin fita naji Hajiya tace "bari drivern yazo mana "
Na tsaya cak tare da rungume hannuwana a cikin hijab,
Ina nan a tsaye suna magana da Mubin, amma bansan me suke cewa ba sbda ƙasa-ƙasa suke maganar,
"Aslamu alaikum hajiya barka da safiya gani "
"Gurin Babanta zaka kaita "
Driver yace "to angama Hajiya ",
Hajiyar ta miƙa masa kuɗi tace ya tsaya ya siya fruits,
Daga nan muka fice zuwa parking space, motar danaga drivern ya shiga ita na shiga muka lula zuwa asibitin Murtala.
A bakin titi muka tsaya, driver ya fita ya siyo fruits ya dawo muka ƙarasa ciki,
A gurin da aka tanadar dan ajiye motoci driver yayi parkin, ya miƙamin ledojin kafin na fito na nufi ɗakin da Abbana yake,
Ina shiga na sameshi shida malam Ahmad suna hira, da sallama na shiga na nemi kujera na zauna ina gaishesu, bayan sun amsa, nace Abba ya jikin ?"
Ya amsa da "alhmdulilh ƴar Abba ya gidan aikin naki ?"
Na ce" lafiya lau "ban sanar dashi abinda ke wakana a gidan ba,
Fitar da malam Ahmad yayi ne ta bani damar ƙarewa ƙafar Abba kallo na ɗago kaina ina ɗora idanuwana akan fuskarsa kafin nace "Abba amma kaji sauƙi koh? naji kace za'a sallameka yau kuma na ganka a kwance "Abba yayi murmishi kafin yace "eh da yau za'a sallameni, to anyi gyaran wallahi har yanzu ƙafar taci gaba da zubar ruwa ana tunanin fitar dani ƙasar waje ne, dan jiya wani yaron Alhjin mai suna Mubin ne yazo yake sanarmin zai nemi transfer zuwa asibitin India,
Wasu zafafan hawaye ne suka wanke min fuska nace "Abba wai ciwo sosai ƙafar take maka ?"
Naga Abba yayi murmishin yaƙe sai kuma yace "da sauƙi karki damu ai yaron yanada kirki jiya ma ya kawomin abinci,
"Dama wannan Mubin ɗin nada mutunci ko kuma dai yanada wani nufinne akan Abbana, amma zan zuba ido ",
"Ilham! Ilham!..."
Muryar Abba ta dawo dani daga dogon tunanin dana tafi,
"Na'am "
Nace tare da kawar da idona ga kallon Abba,
"Ilham ki kwantar da hankalinki babu abinda yake damuna face ciwon ƙafar nan, itama ɗin ina kyautata zaton  zatayi sauƙi insha Allah tunda ba kamar daba "
"Hmm "
Nace ina mamakin inda Abba yake ƙoƙarin  ɓoyemin damuwarsa,
"Abba kenan  kace ka sami sauƙi to nidai maganar fita ƙasar wajan nan ne ke damuna"
"Ilham banason musa musu ne ki kwantar da hankalinki"
Da mamaki na baro asibitin muka dawo gida,
Tun a mota nake tunanin anya babu abinda Abba ya ɓoyemin kuwa ?, ina tunanin akwai lauje a cikin naɗi ",
Dan rabona da ganin ya taka tun a gida,
1:40pm Nayi alwalah na kabbara sallah, ina idarwa na fito parlo na fara gyara dinning sbda jere abincin rana, Allah ya taimakeni Hajiya ta gama abincin kasancewarta mace mai kirki, da Mubin ne yayi halinta daya more wallahi.
Bayan na gama kawo komai ina shirin ajiye juyawa zuwa ɗakina naji sallamar su Ibrahim,
Da fara'arsa ya ƙaraso shi kum Mubin ɗin naga yayi room ɗin momy,
"Sister Ilham ya aiki..?"
Cikin jin nauyi nace "alhmdulilh"
"Masha Allah dan Allah inaso muyi magana mai amfani dake, pls karki ce a'a "
Rurin da wayarsa tayi ne ya sashi, cirota naga ya kara a kunnensa,
Cikin rashin tsammani naji Ibrahim ɗin yace "gata a kusa "
"To waye?"
Yana miƙomin wayar na karɓa kana nace "Aslamu alaikum "
Muryar Abbana naji yana cemin "Ilham kina jina....?"
Cikin sauri nace "eh...eh..a..Abba ina jinka"
Sai kuma na juya na kalli Ibrahim da shima yana tsaye niɗin yake kallo,
"Ki shirya gobe insha Allah zakuje wani taro, zakije a matsayin matar yaron gidan da kike aiki,  dan Allah karki bani kunya "
Mummunar faɗuwar gaba ne ya dirar min lokaci ɗaya, na sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da sharce gumin daya keto min tashi ɗaya, nace "Abba matarsa fa akace kenan gudun mawa zan bayar akan ƙarya? "Ash shaaa "
Abba yace tare da miƙewa zaune daga kan gadon asibitin da yake, ya daɗa kara wayarsa a kunne yace "kiyi haƙuri kinga suna taimaka mana ne, kuma watannin kamar wasa sai kiga sunzo, kuma idan ƙafar tawa ta warke kafin lokacin tafiyarmu kinga gida zan koma ",
Shiru ne ya biyo baya na tsawon wasu mintuna, na kalli Ibrahim a karo na biyu kana nace "Abba zanyi shawara "
Dariya ma naso bawa Abba, naji yana cewa "Ilham shawara kuma dawa zakiyi ?abinda gobe ne, amman idan kinga akwai damuwa ki faɗi ra'ayinki "
Daga yanayin da Abba yayi maganar nasan baiji daɗi ba, cikin sauri da gudun karya kashe wayar nace "Abba zanyi abinda kakeso na...na...amin..ce "
Na kashe wayar tare da rugawa ɗakin da nake kwana da gudu.
Ibrahim ya kalli wayar dana ajiye akan kujera yana dariya yace "wow nagode wa Allah daya bani ikon yin wannan hikimar saura gogan "
Cikin farinciki ya danna number momy,
Ring ɗaya zuwa biyu ta ɗaga tare da cewa "kun shigo ne? tun ɗazu nake tsumayin ku "
Ibrahim ya waro ido kana yace "eh amma na ɗauka Mubin yana gurinki ne?"
"A'a kodai ya wuce part ɗinshi "
"Eh to ki fito momy akwai kyakkyawan albishir "
Momy ta fito da sauri tana cewa "Khalil ina sauraronka "
Ibrahim na washe baki yace "momy mutuniyar fa ta amince, amma da izinin babanta "
Fuskar momy kamar wacce akayi mata bushara da gidan aljanna tace "bani labari ya akayi ?"
Ibrahim yayi dariya kana yace "Hospital naje gaisheda mahaifinta, nake jaddada masa inhar ƙafar yana ganin da matsala Mubin yace mu nemi transfer zuwa India tunda dama already sun riga sunyi maganar,
Yacemin yarinyarsa batason nesa dashi sbda mahaifiyarta ta rasu,
Anan na sami damar shigar da manufata, nace masa akwai wani taimako da mukeso yayi mana shida ƴar tasa,
Ibrahim yaci gaba da cewa "akwai wani taro da zamuyi, masana'antarmu na bukatar kulawa ta hanyar taron da muka shirya yi "
Na bashi labarin komai da komai akan shirye-shiyen da mukeyi, tare da jaddada masa zuwa gobe zamu tafi ".
Momy tace "toya ake ciki ta fanninta dai babu matsala koh?"
Ibrahim yace "ina tunanin hakan amma inason muyiwa Boss Surprise "
Momy tace "ina jinka "
Ibrahim yace "momy yanzu me kike ganin za'a fara ?"
"Yanzu dai abu na farko wankin kai da gyara gashi zakuje, daganan a gyara mata farce, idan kun dawo sai mu shiga kasuw ".
Momy ta faɗa cikin farinciki,
"Momy ina tsoron karfa Mubin ya gano ya hargitsa plan ɗin, zaifi ku tafi tare "
"Tom kawai momy tace "kana tayi masa godiya sosai, bai wuce gurin Mubin ɗinba ya fice.
4:12pm Tun da na shige ɗaki nake kuka, a halin yanzu hawaye sunyi ƙaura daga idona, banma san ankira sallah ba, "Innalilahi wa inna ilaihir raji'un "na ambata kafin na miƙe na shiga toilet nayi alwalah na fito na shimfiɗa sallahya na kabbara sallah, ina idarwa nayi adu'oina kamar kullum, sai dai yau harda na waɗannan mutanen da sam yanzu na kasa gane nufinsu a kanmu, gashin sun yiwa Abbana daɗin baki na shiga uku,
Ninke sallahayar nayi na fito zuwa parlo na wuce kichen, kasancewar door ɗin kitchen da ƙofar da zata sadaka da part ɗin Mubin tana nan parlon, acan ta waje ma akwai wata ƙofar,
Ina shiga na samu, babu aikin komai  na dawo ɗakina, sbda yanzu kam har momyn ma haushinta nakeji, musamman idan na tuno da farincikinsu tafi so, koda yake dama ni wacece da za'a dinga ban bance nawa ɓacin ran da farinciki?, na tambayi kaina ina dafe hannuna a kumatu.
"Aslamu alaikum"
Momy tayi sallama na amsa mata da "walkissalam "ba tare dana ɗago na kalleta ba kaina a sunkuye,
Kujerar roba ta janyo ta zauna kafin naji tace "Ilham "
"Na'am" nace ina saurarar abinda zatace,
"Nasan Ibrahim yayi miki ba dai-dai ba, akan haɗaki da mahaifinki da yayi, inason ki taimakemu dan Allah ki amsa abinda mukazo miki dashi, idan kuɗi kike buƙata akwaisu "na ɗago tare da cewa "ni bana buƙatar kuɗi, kawai zanyi biyayya wa mahaifina ne.."
Cikin farinciki momy tace "amma idan ba damuwa kukan me kike ?"
Nace "ina tuno halin da Abbana yake ciki ne "
"Ayya ana bashi kulawa koda yaushe kuma yana samun lafiya "
"Uhm "kawai nace,
"Yauwa ki shirya zamu fita yanzu idan kin gama ki sameni a parlo "
Na amsa da "To"
Momy na ficewa na zura hijab ɗina kana na fito,
Ban sameta anan ɗinba kamar inda tace, na zauna zaman jiranta har na tsawon wasu mintuna, sai gata ta fito tana cemin "tashi muje toh "
Nabi bayan momy muka wuce parking space driver na ganinmu ya taho da gudu yana kuma gaishe da momy, bayan ta buɗe motar muka shiga back side driver ya tada mota zuwa kantin kwari,
Da isarmu driver yayi parking muka fito, dama momy ta riga da ta sanar masa da inda zamu,
Munbar driver a mota, mu kuma muka shiga kasuwa, shagon wankin kai muka shiga, bayan mun gaisa da mutanen ciki da matar aka kawo mana kujeru biyu muka zauna,
Momy tace "Iya wankin kai za'ayimi, sai gyaran farce akuma gyaramin gashi na wato ayimin style ta nuna wani photo dake jikin bango na waɗanda aka gyara ta zaɓi ɗaya daga ciki, nidai nawa ido sai inda akayi dani,
Inada son gyara sosai kasancewar bamu da hali yasa koda nasa mai bana ɗorawa kaina damuwar inje a wankemin,
Mutane biyu ne a kaina, da mai wankemin kai da mai gyaramin farce, cikin wasu lokuta nayi kyau kamar ba niba, dan koni danaga gyaran gashin da akayimin a mudubi daɗi ya kamani, ana gama min momy ta biyasu driver ya wuce damu cikin kasuwa lokacin yamma ta farayi,
Bayan momy ta nuna masa inda zaiyi parking muka fito, wani katafaren shago muka shiga, wanda ke ɗauke da abayoyi iri-iri da daga waje kuma akwai kayan makeup, in taƙaice muku zance zan iya cewa "babu abinda babu "momy tace "zuwa za'ayi gobe ayimin kwalliya, sai data siyamin kaya wajen kala biyar masu tsadar gaske, da leshi mai ruwan coffee yanada adon flowers milk da baƙin stone, sai abaya baƙa mai adon duwatsu farare, sai atamfa mai manyan flawoyi bule da da baƙi, kayan dai sai wanda ya gani, ta siyamin bra da pants ko wanne guda uku uku, da takalmi heels masu tsada da mayafai kalar takalmin, da sarƙa mai haɗe da ɗankunne warowaro da agogo da zobuna, kai abin har mamaki yake bani, sai kuma na fara tunanin to idan an gama taron zata karɓe kayayyakin kenan ?"
Ina tsaye driver yazo yana loda kayan a both momy ta taɓoni kafin tace "me kuma kikeso anan?"
"Babu komai "nace ina murmishi,
Daga nan muka dawo gida a gajiye.
A ranar banyi girki ba, sai tea da bread da muka sha, bayan kowa yayi sallah nikam na kwanta, sbda bansan ko Mubin ɗin ya shigo ba, naja tsaki,
Washe gari da asbha inayin sallah na shiga wanka, bayan na fito daga wanka ina ɗaure da towel naji an murɗa handle ɗin ƙofa,
"Aslamu alaikum "
"Walkslm"
Momy tace "ƴata da wuri fa zamu shirya, iya mai zaki shafa munyi wayar da maiyin makeup "
Na amsa da "toh "
Momy ta fice bayan mun gaisa.
Kamar inda tace kar in yi kwalliya banyi ba na shiga kitchen dan haɗa mana break da wuri, tunda ance da wuri zamu fita.
Bayan na kammala na jere a dinning, lokacin ƙarfe bakwai(7:00) dai-dai,
7:30 Momy ta fito tana waya,
Ina zaune a parlo ina kallon tashar MBC action nace barka da fitowa Hajiya "
Momy tace " yawwa Ilham meyin makeup tana hanya insha Allah "
Kafin inyi magana, naga Mubin ya fito yana sanye da jallabiya fara mai hula, ya durƙusa har ƙasa yace "momy barka da safiya "momy ta amsa da barka  my son ya shirye-shirye?" Mubin ya amsa da alhmdulilh momy ƙarfe 9:00 zamu fita fa "
Yana faɗa ya fice.
"Ilham National I'D card ɗinki fa?"
"Yana ɗaki a cikin ƴar ƙaramar jakata "
Naba momy amsa,
Ƙarfe (8:3)meyin kwalliya ta iso, aka fara yimin,
Sai wajen ƙarfe takwas da minti arba'in muka gama,
Aka zaɓarmin kalar kayan da zansa, leshi ne milk color flawarsa mai ruwan  sai stone wanda ya ƙara ƙawata adon leshin, kasancewata fara ba'sosai ba, yasa leshin yayi min kyau, kasancewar shine duk a cikin kayan ɗinkake sai dogayen riguna,
Wuyana yasha sarƙar gold da ɗan kunne hannuwa na kuwa sunsha zobuna a warwaro da agogo fari mai kyau, ƙafata tasha heels mai tsini,
Ni kaina nasan nayi kyau ko ba'a faɗamin ba,
Momy data barmu a parlo tun ɗazu, ta dawo tana cewa "wow yarinyata ta fito "nima murmishi nayi wanda ya ƙara fitoda ainihin kyawuna, dama niɗin kyakkyawa ce,
Ana gama min aka fesheni da wani zafafan turaruka masu sanyin ƙamshi, momy ta sallameta.
Shigar momy ɗaki keda wuya, naga ta fito hannunta riƙe da glass burberry wanda ya rufemin fuska amma ba sosai ba,
Sallamar Ibrahim ce tasa momy washe baki tace "harka fito kenan ?"
Ibrahim ya durƙusa ya gaida momy kafin ya miƙa mata waya....
*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
      _Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
      _Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
      _Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
    _Mrs Bukhari_

5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*
     _Miss Hajo_

Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda  huɗu N700
Guda biyar 1k

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎....

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar  1000f
Guda huɗu  700f
Guda uku  600f
Guda biyu  500f
Guda ɗaya  300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇Kina turawa zamu saki a grp
08141799224

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*

GUNTUN GOROWhere stories live. Discover now