Chapter 1-2

173 12 3
                                    

*💥GUNTUN GORO💥*

_Zainab Habib(Mom Islam_

🆓🅿1-2

_Gargaɗi!! Gargaɗi!! Gargaɗi!! ban amince a sauyamin littafi ,ko a ɗoraminshi a wata ƙafa ba tare da izinina ba! wannan littafin mallakar Zainab Habib ne, yin hakan zai iya sawa ince nabar mutum da Allah! ina roƙon Allah yasa kamar inda muka fara littafinnan lafiya Allah kasa mu kammalashi cikin ƙoshin lafiya amin_

Asabar shida ga watan bakwai ,shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu, 11:1am
Zaune nake gaban Abbana hannuna bisa kumatuna, idona kuwa nakan ciwon ƙafarsa wacce munyi magani har mun gaji.
"Ilham" Abba ya kira sunana cikin sanyayayyar muryarsa wacce duk sanda naji ya kirani da ita jikina ke kyarma sbda nasan babu lafiya.
"Na'am" nace kaina a ƙasa ina jiran inji abinda Abbana zai cemin "Ilham kinga wannan ciwon ƙafar tawa daɗa ta'azzara yake, gashi duk wata dukiya da muka mallaka a halin yanzu mun tashi babu ko sisi, ciki harda gonakin mahaifiyarki duk kince in siyar na siyar Allah baisa an dace ba", kallon Abbana nayi idanuna na zubar da ƙwallah nace "Abba to yanzu ya zamuyi gashi ƙafar daɗa rarikewa take?"
yamutsa fuska Abbana yayi lokacin da yake ɗago ƙafar alamun zafi takeyi masa,
"Da zaki amince Ilham da na nema miki aikatau a gidan Alhaji Abdullahi Zakin Naira "a gigice na ɗago kaina dana sunkuyar ina kallon Abba kafin nace" aikatau kuma Abba ?ko ka mance kai da kake cemin baka shiri da iyayen da suke tura ƴa'ƴansu aiki amma kai da bakinka kake kiramin inje inyi aiki" na faɗa gabana na dukan uku-uku, tabbas inda abinda na tsana bai wuce ace gani a gaban wasu sai nayi musu wanke-wanke da shara sannan zasu bani abinda zanci ba,cikin mamaki da tsoro nace ",Abba mezan gani haka ?kuka kakeyi ?, cikin muryar kuka Abba yace "Ilham bawai ina nufin ki dauwama kina aikin bane, nidai burina a bada kuɗin aikin naki in sun yarda mu fara zuwa asibiti tunda ,har yanzu bamu taɓa tunanin zuwa ba ko za'a dace" yanayin da naga Abbana ya shiga ya jefani cikin wani hali, nace "Abba ka nemo wata shawarar amma wannan batayiba" na miƙe rai a ɓace, a dole ina ganin Abba yanason ya sa a wulaƙantani, yo inba wulaƙantawa ba, yace inje wani gida aikatau bacin nasan zubar da mutunci ne, duk da nasan bashi da cikakkiyar lafiya .
Kai tsaye ɗakina na nufa, na kwanta saman katifata wacce taji zanin gado milk color ,kasancewar a ƙasa take duk da hakan bai hana zanin gadon ɗame ƙatifarba .
Kaina na kifa a kan pilo tare da tuno maganar Abbana ta gurin aikatau "ya illahi" na ambata idona na zubar da hawaye ,daga nan bacci yayi awon gaba dani.
Ganin na shiga ɗaki baba ya ɗogara ƙafarsa cikin ƙarfin hali ya wuce ɗakinsa, zuciyarsa fal baƙincikin ƙin amincewata da buƙatarsa.
Bani na tashi ba sai waje ƙarfe biyu dai-dai ,ina mutsike idona na fito tsakar gida ina cewa "gaskiya nayi bacci mai nisa taɓɓ yaushe rabona dayin wannan barcin ?",
Bayi nashiga na ɗauki buta na kama ruwa kana na fito nayi alwalah, na nufi ɗaki dan gabatar da sallah, ina idarwa na shafa adu'oi na ,na miƙe na ninke sallahya na cire hijab kana na fito tsakar gida tambayar Abba mai zamu dafa zuwa dare .
Da sallama na shiga ɗakin nasa ,bayan ya amsa na tsuguna kafin nace ",Abba me za'a dafa ɗazu da safe ma raguwar gari nasha da suga" rai a ɓace Abbana yake kallona ,wanda yasa na fara tsorata dan tunda mahaifiyata ta rasu lallashina yake, amma yau shine dayimin irin wannan kallon?, na tambayi kaina cikin tsoro.
"Tashi ki bani guri bana son ƙara jin maganarki" Abba ya faɗa yana nunani da hannunsa, Innalilahi wa inna ilaihirraji raji'un na ambata a fili kafin nace,"Abba ko nayi maka laifi ne?" abinda Abbana baya yimin naga ya kuma yimin wato harara, shidako mugun kallo baya min haka kuma ko me nakeso shi za'a dafa, kasancewar ana yawan kawo mana sadakar abinci .
Jiki a sanyaye na tashi nabar gurin idona tabb da ƙwallah, ina shiga ɗaki suka zubo,
Har aka kira sallahar la'asar Abba bai cemin komai ba, har akayi magrib ko kulani ma bayayi, balle yaji nayi masa magana.
Tunowa nayi, ashe akan ƙin amincewa da buƙatarsa da naƙi yine yasa shi yin fushi dani,
Kiran sallahar Azhar da akayi ne ya sani fitowa daga ɗakina, saboda inason idan nayi alwalah nayi sallah inje gidansu Muhibba ƙawata wace muka gama secondary tare, in aro nera ɗari, ina tsaye ina shirin shiga bayi naji Abbana na sauke numfarfashi kamar wanda yayi uban gudu, da sauri nayi ɗakin cikin mamaki na gansa a zaune yana kuka ga ƙafar na zubar ruwa, "mun shiga uku" na ambata sai kuma na fashe da matsanancin kuka, bansan lokacin da nace "Abba na amince ,na yarda zanyi aikatau domin samun lafiyar ƙafarka",
Albarka Abba ya dinga samin har cemin ga ɗari biyar in siyo taliya a dafa ko mai da yaji ne, tunda bama rabo da kayan abinci amma yau kam bamu da taliya ta ƙare.
Ganin fara'a a fuskar Abbana yasa nima naji farinciki sosai,
Na miƙe na haɗa wuta na ɗora sanwa, ruwan na tafasa na zuba taliyar, na tsiyayo manja na yanko albasa, bayan taliyar ta dahu na sauke na juye a kwando,na ɗora manja nasa albasa, ina gama haɗa komai na zubawa Abba nasa, nima na zuba nawa.
Ɗakinsa naje munacin abincin muna hira har muka gama, Abba ya miƙe ya kuskure baki, dan gabatar da sallaha ni kuma na dawo ɗakina nayi tawa sallahar, tare da kwararo adu'oi akan samun lafiyar Abbana.
Washe gari,bayan anyi sallah Abba yayi tasa a gida sbda ƙafarsa, ina idarwa naje na gaishesa ya amsa cikin sakin fuska, na fito na haɗa wuta,wutar na kamawa na ɗora ruwan wanka haɗe da ruwan kunu, yanayin zafi na ɗiba naje na sirka kana na nufi bayi kasancewar soso da sabulun yana can, cikin sauri nayi wanka na fito,lokacin ruwan yanata tafasa na dama kunun zuwa anjima nasa gasara na sanya suga,na ɗauko kofin baba na sanya masa na shiga ɗakinsa da sallama, amsawa Abba yayi fuska a sake ,na durƙusa nace "Abba ga kokon naka "Abba ya karɓa yana sanyamin Albarka na fice .
Cire hijab ɗin dana fito daga wanka nayi,na janyo ledar kayan kwalliyata, cikin ƙwarewa irin tawa a fannin ado da kwalliya na tsara kwalliya mai ɗaukar hankali, bayan mayukan dana shafe jikina dasu masu ƙamshi mai daɗi, miƙewa nayi na buɗe akwatin kayana na ciro doguwar rigar milk color anyi mata flawoyi da pink ɗin zane wanda yai matuƙar fito da kyan rigar, bayan na feshe jikina da turare na kawo rigar nasa,nayi rolling ɗin mayafin rigar a kaina tare da kallon kaina a mudubi" murmishi nayi kana nace Alhmdulilh, na ɗauki glass ɗina no respect nasa, wanda ya rufe ilahirin fuskata, duk wanda ya ganni zai ɗauka ƴar wata alhajin ce sbda irin shigar da nayi koni jin kaina nake a sama lol, farin takalmi da farin mayafi na ɗauko kana da sarƙa da warwaro da ɗankunne duk na maƙalasu, tunowa nayi ban sanya agogon hannuna wanda nake gayu dashi sbda a zahiri baya aiki kawai dai ina sawa ne.
Kunsan in mutum yayi wanka,musamman ma yaci tsaleliyar kwalliya baya son ya dinga tafiya cikin rashin tsari, to nima a nawa ɓangaren haka ne, tafiya nake kamar ƴar wani mai muƙami, kofin danasha kunu na fito dashi, Allah yasa nayi wanke-wanke, ina daga bakin ƙofar ɗakina ina kallon fuskata a mudubi na ɗaga murya nace "Abba yanzu ƙarfe nawa?"Abba ya kalli agogon wayarsa kana yace "ƙarfe goma saura minti uku (9:57am) "To" nace, dan ba haka naso ba, naso ace ƙarfe sha ɗaya ne yanzu, na zauna har ƙarfe goma sha ɗaya (11:00) dai dai na fito haɗe da janyo ƙofar ɗakina,naje ɗakin Abba nace Abba zanje gidansu Muhibba "Abba yake kinsan dai banason ki fita ki kai yamma koh ?"Abba insha Allah ba jimawa zanyi ba",
Abba yace "a dawo lafiya" nafice.
Kai tsaye na fita,
Bakin titi na nufa ina jiran napep,
Wata dalleliyar mota fara sol mai masifar kyau ta biyo ta gabana,saura kaɗan ta bigeni "cike da masifa haɗi da huci na jin haushin abinda mai motar ya yimin, naja tsaki mtsw, sai kuma naga motar ta dawo da baya tayi parking a gabana, rage tsayin baƙin gilashin motarsa yayi, na kusa dashi yace "ƴam mata dan Allah kiyi haƙuri" cikin yamutsa fuska na nuna wanda yake mazaunin driver da hannu kafin na fara zazzaga musu ruwan masifa ina cewa "banda tsabar wulaƙanci da rainin wayo shi drivern makaho ne ?"ko baya gani ne?, inda abinda yafi bani haushi bai wuce, ƙin kulani da drivern yayi ba, sai wani shan ƙamshi yake "Ibrahim sai da nace maka bazan dawo ba bana son raini amma kaga abinda ka janyo mana ko ?"wanda saurayin ya kira da Ibrahim yace "afuwan Mubin, kamar inda ake yabon ahalin gidanku gurin tarbiya da sanin mutuncin juna bai kamata ka sauya naka halin ba" Ibrahim ya ƙarshe zancen yana dafa kafaɗar Mubin.
Niko raina ya gama ɓaci sosai gashi ban sami adai-daita sahu ba, gashi sun wani taremin gaba nikuma nakasa matsawa tsabar inajin ruwan masifa.
Ibrahim ya leƙo da kansa, cikin sanyaya murya yace "ƴan mata kiyi haƙuri dan Allah",
Shiko Mubin ɗin tsaki yaja tare da cewa "aikin banza aikin wofi ni kaga ba tsayawa jiranka zanyi ba "jibeki mitsw"
Mubin yaja mota kamar wanda zai kuma bi ta gabana.
Iya jin haushi naji haushi ji nake kamar zanyi kuka tsabar baƙinciki, gashi inajin kamar inkoma gida.
Kallon jikina nayi naga ai yama watsamin kwatami, na dafe kaina cikin zafin rai nace "anyi shege ɗan kutumar uba Allah sai ya saka min, inhar kere na yawo zabo na yawo watarana zasu gamu, ina tsaka da tunani naji mai napep na cewa "hajiya tafiya ne?"
Idanuwana nayimin zafi nace eh zakaje ɗorayi ?" mai napep yace "naira ɗari" batare da na taya ba nace tom muje ,
Muna tafiya ina tuno wulaƙancin Mubin da bani haƙuri da abokinsa Ibrahim yayi, nuna masa ƙofar gidansu Muhibba, bayan yayi parking nace dan Allah yayi haƙuri in shiga in amso kuɗi "mai napep ɗin yacemin babu komai".
Cikin sauri na shiga, tare da yin sallama nayi sa'a Muhibba na zaune tana latse-latse a wayarta, gefe kuma mahaifiyarta ce take bawa ƙaninta nono, ina ƙaƙalo murmishi nace "Muhibba bani nera ɗari "mahaifiyarta na washe baki tace "ah Ilham kece a gidan ?"ta miƙomin ɗari biyu, na amsa na kaiwa mai napep ya bani chanji,
Dawowa nayi ina murmishi nace "Ummi ga chanjin "Ummi tace "kibarshi kawai Ilham muje ciki" Muhibba tana dariya ta fara tsokanata tana cewa "wannan wankan fa ?"nayi dariya kafin nace ",na zuwa gidanku ne" muka shiga ɗakin Ummi dukkanmu,
Bayan mun gaisa da Ummi ta tambayeni ya jikin Abbana, nace mata yaji sauƙi, daga nan ta fice muka sha firarmu nida Muhibba "ya na ganki wani iri kamar kinyi ciwo gashi idonki kamar kinyi kuka ?"Muhibba ta tambayeni,
"mtsw Muhibba na haɗu da wani shege wanda kansa ke rawa walhi da tuni kunji labari yasha ban ban an kaɗeni "Muhibba ta dafe ƙirji tana cewa" na shiga uku garin yaya "cikin ƙosawa da bada labarin, sbda bana son in dinga tuno abinda yayimin yasani cewa "iskanci kawai ",
Bani nabar gidansu ba sai da muka yiwa Ummi gyaran ɗaki da wanke-wanke, muka sake gyara ɗakin Muhibban, kasancewar gidan babba ne, yasha siminti ɗakuna biyar ne a gidan, ɗay na Ummi ɗaya na Muhibba ɗaya kuma na baban Muhibba ɗaya na baƙi ɗayan kuma yana mazaunin kitchen ne.
Bayan mun sanya turaren wuta a gidan lokacin munyi sallahr Azhar muka shiga kitchen muka fere dankali na hausa muka soya, kasancewar sunada miya.
Idan naje gidansu Muhibba sai ka rantse gidanmu ne,
Ƙarfe 6:pm na ɗauko mayafina ina cewa "Abbana yace kar in daɗe lallai yau zansha faɗa sosai" Muhibba tasa dariya tana cewa "Ilham akwai tsoro gaskiya, to gashi bakici abincin ba ai saiki tsaya dan bazaki tafi bakici ba" Ummi na jinmu tana dariya, har nayi hanyar waje Ummi ta ƙwalamin kira na amsa kana nazo, baƙar leda naga ta miƙamin tace "aiko gashi na ƙulle miki a leda" murmishi nayi ina tattaba dankalin kana na rufe baki ina cewa "Ummi harda miya?,
Ummi tace" eh to ki gaida baban bak kice ina gaishe shi ",
Muka fito tare da Muhibba muna tafe muna hira, sannu a hankali muka iso bakin titi na tari napep zuwa anguwarmu Rijiyar lemo, Mukayi sallama da Muhibba.
Ina komawa gida na rangaɗa sallama, duk da nasan zansha faɗa,
Shiru naji babu alamun motsin Abba a gidan, cikin ƙanƙanin lokaci na tsorata dan ko sallahar magrib ba'a kira ba ana harama, a iya sanina tunda Abba ya haɗu da ciwon ƙafarnan ya dena yawan fita amma yau ina yaje ?, na tambayi kaina batare da tunanin ai babu wanda zai ani amsa ba.
Ban kawo komai a raina ba sbda banji wani yanayin damuwa a jikina ba, dan haka na wuce ɗakina na buɗe kana na ajiye dankalin cikin roba, fitowa nayi tsakar gida ina mai cire no respect ɗin idona nahau tunani,
Kiran sallahar magriba da akayi ne ya sanyani miƙewa naje na ɗauro alwlah na dawo na shimfiɗa sallahya na kabbara sallah, ina idarwa na fito tsakar gida na ɗauki kujera ƴar tsugunno na zauna tare da rafka tagumi, abinda ya fara yimin ciwo shine rashin waya da bani da ita, har akayi sallahar isha'i aka idar har ƙarfe tara Abba shiru, babu shi babu alamunsa..!

GUNTUN GOROWhere stories live. Discover now