PAGE 7&8

60 4 0
                                    

🌺🌺 *WAYE SANADI..!?* 🪦🪦
                *PART TWO*

                      *Story & Written*
                                  *By*
                        *Oum Sumayya*
                           #Babybintuu

BINTU KITCHEN AND INCENSE*

*Ina kuke ma'abota son k'awata girke girke da sinadaran girki masu k'amshi da sa dad'in girki uwar gida kai harda amarya kuna ina ku masto kusa ku mallaki Bintu curry powder ingantaccen sinadarin girki mai sa girki k'amshi da dad'i curry powder mu yasamu had'i na musamman daga ingantattun kayan k'amshi masu sanya girki d'and'ano har lau Bintu curry powder basu tsaya anan ba sun kawo muku had'add'en yaji dayaji kayan k'amshi mai k'ara lafiya ajiki dakuma had'in daddawa mai sanya miya k'amshi da sa oga santi muna da kitchen ingredients kamar haka*

Curry powder
Garin citta kanin fari dan lipton
Hadd'd'en yaji mai kayan k'amshi
Had'add'en yaji mai tafarnuwa
Had'add'iyar daddawa mai kayan k'amshi
Duka akan farashi mai sau'ki muna turawa ko ina afad'in arewacin nigeria kayan ki su iso cikin salama uwargida amarya maza ku hanzarta siyan *Bintu kitchen ingredients* sai angwada akan san na kwarai! Zaku iya tuntu'bar mu akan wannannumber 07017296839

*abun bai k'are haka ba akwai ingantattun turarukan mu masu sanyin k'amshi da dad'i munada turaruruka kamar haka*

Farar humra
Ba'kar humra
Ja humra
Kulacca
Humra ta fuska
Turaren wuta na kaya
Turaren wuta na jiki
Turaren wuta na tsugunno mai matse mace taciki da waje

*Kuna ina amarya uwar gida kai harda y'an mata ma don k'amshi shine mace muna saida d'aya d'aya muna bada sari akan farashi mai sau'ki uwargida amarya karku bari abaku labari zaku iya tuntu'ban mu akan wannan number 07017296839 koda kud'in ka saida rabon ka*

*SAVEN AND EIGHT*

Lokaci d'aya duk suka mik'e zuciyoyin su na wani irin lugude dak'yar Mama tafurta "tom muji alkair..." Bata k'arisa ba saiga Ammi ahargitse tashigo parlourn fuskan nan tayi jawur kamar jini zai fito tazube agaban Mama cikin kuka majina tana futa daga hancin ta take fad'in "Hausi burin ku yacika sai ku zuba ruwa ak'asa kusha duk halaccin da mutanen nan sukai muku amma ace irin sakayyar dazaku nuna musu kenan tabbas kun cika butulu kuma wannan ita ake kira da muguwar sakayya amma babu komai akwai Allah domin baya barci kuma baya zalunci zaibi mana hakk'in mu" tak'arisa maganar tana fashewa dawani sabon kuka mai cin rai,
Duk dacewa hankalin Mama yatashi amma hakan bai hanata kinin kinin da fuska ba tace "Hajiya nace kidaina zuwa gidan nan koso kike nakai k'arar ki wajen hukuma sumana iyaka ne koda yaushe dakin d'ebo mugayen alkaba'en ki saiki zo min gida wannan yazama na k'arshe idan ba haka ba dukkanin abunda yabiyo baya ke kika jama kanki tashi kifutar min agida" tak'arisa maganar tana nuna  mata hanyar futa daga d'akin jikin ta har kyarma yake,
Mik'ewa Ammi tayi tana fyace majina da gefen gyalenta takalli parlourn kamun tamaida duban ta zuwaga Mama dake tsaye idanun ta k'yam akanta hannu tasa tashaare hawayen dake zarya bisa kuncin ta kamun tace
"Koba kice intafi ba zan tafi Hausi amma kisani kunci amaanar yarda kusani Allah bazai barku ba daga ke har Haulatun hakk'in rai biyunnan tun aduniya sai kun ga sakayya" tana kaiwa nan tawuce fuu kamar zata tashi sama,
Dawani irin kallo suka bita jikin Mama na tsananta kyarma tace 'hakk'in rai biyu!!" Saikuma tai baya zata fad'i y'ar aikinta tatarota tazaunar da ita tana mata sannu hannu tad'aga mata kawai yayin da Salma takawo mata ruwa dasauri ita kanta jikinta tsuma yake don kukan dataga Ammi nayi ba abanza ba dawata ak'asa,
Dak'yar Mama ta had'iye ruwan datake jin shi kamar mad'aci kafun tasallmi y'ar aiki tamaida akalan kallon ta ga Salma dake zaune dab'ar saman rug tazuba uban tagumi tana kallon Maman, murya asanyaye Mama tace "kiramin Hamza Salma"
Jiki ba laka tajanyo wayarta tadanna ma Hamza kira amma harta jera mai kira goma ba'a d'aga ba hakan yasa takira Momma nan ma no answer har five miss call,
Aje wayar tayi gefe tana sauke ajiyar zuciya idanun ta akan Mama batare datace mata komai ba domin duk kiran datake hansfree take sawa duk sunyi zugum zugum ba me iya cewa komai kamar daga sama sukaji ring d'in wayar dasauri tajanyota ganin number Hamza ne yasa tayi picking dasauri amma sai taji muryan wani daban yana fad'in "My name's captain Mk naga miss call naki ne nabiyo"
Cikin in ina tace "dama dama ina son magana da Yaya Hamza ne shin yana kusa?"
"Madam..." Saikuma yayi shiru ganin sunan d Hamza yayi saving number ta my sister yad'an saki ajiyar zuciya kamun yace "General bashi da lafiya yana hospital"
Amugun rud'e Salma tamik'e hakama Mama murya aharhard'e tace "what me....me...menene yasame shi yana ina yanzu ina son magana dashi ne please is an urgent kataimaka min dan Allah"
Tsayuwa captain yagyara yana kallon cikin hospital d'in kamun yace
"Am so sorry to say general yasha guba acikin coffee shida mahaifiyar shi kimanin kwanaki biyar kenan yanxu haka yana soldier hospital dake cikin sobi barrack"
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ma...ma..matar shi fa?"
Cike da k'osawa captain yace "so sorry madam ita ake zargin tabasu guban" yana fad'in haka ya yanke wayar.
Wani irin dum kanta yamata tasaki wayar ak'asa tana maimaita "Haulat taba Momma da Hamza guba kuma wannann wani irin mummunan kaddara ne hasbunallahu wani'imal wak....." Tana kaiwa nan tai baya idanun ta na rufewa,
Sulaiman da Fatima dasuka shigo yanzu amma sun ji abunda tafad'i da mugun azama sukai kanta Sulaiman yatare ta yana fad'in "Fatima kawo ruwa dasauri"
Gaba d'aya tama manta inda ruwan yake tai hanyar bedroom saikuma tadawo tabud'e fridge tad'auko cool na gora
Mama ma kanta tayo tana fashewa dawani irin kuka tanajan innalillahi wa'inna ilaihirraji'un afili tafurta "wannan wani irin abune yake faruwa dani d ahalina Allah ka kawo mana d'auki" saikuma tafashe dakuka,
Duk yanda yajik'ata da ruwan bata farfad'o ba saima jini dayaga yana gangarowa ta k'asanta hakan yasa yad'auke ta da mugun sauri yayi waje da ita, arud'e su Mama da Fatima suka mara mai baya harsun shiga mota Sulaiman yace Fatima takoma tad'auko jariri dagudu takoma tad'auko shi tana kuka haka suka nufi asbitin nasarawa cikin azama aka amshe ta emergency sukuma suka tsaya reception sai sharar kuka suke Sulaiman ne yayi k'arfin halin ba Mama baki akan zancen dayaji inda yake ta k'ok'arin kwantar mata da hankali duk da shima yana buk'atar me kwantar mai da hankalin amma shi namiji ne kuma da jarumta akaasan maza.

Duk inda tashin hankali yake to Aunty Saudat da Dija sun ganshi akwanaki biyar da faruwan abun ne wasu samudawan sojoji sukazo har cikin d'akin dasuke aka tasa k'eyar Dija bayan ansa mata handcuff k'afa da hannu wani irin kuka mara sauti takeyi  (🤣aradu wargi ma da wajen yin sa) nadama da dana sani yana k'ara shiganta (niko nace marasa amfani) tana kallon Mom d'in ta kallon k'arshe dan tasan bazata sake ganin ta kashe ta za'ai wannan shine sakayya na abubuwan data aikata ma Haulat, 
Ita kanta Aunty Saudat d'in kuka take tana kallo aka tasa k'eyar Dija dagudu tamik'e tabiyosu tana k'ok'arin rok'on sojojin amma kallon d'aya wani yamata tashiga taitayinta dole tazube awajen tana  gunjin kuka mai cike da nadama itama🤔,
Suna fitowa aka samata wani bak'in k'yalle afuskarta aka jefe ta cikin wata mota awulak'ance kafun sauran sojojin suka shiga akaja motan da mugun space.
Hannun shine yafara motsi kafun k'afarshi saikuma yafara k'ok'arin yabud'e idanun shi duk kuwa da hasken daya cika mai idanu ahaka yabud'e idanun yana wani irin kallon pop room d'in kusan mintuna goma kamin yaji motsi dasauri ya waiga da kanshi dayake jin kamar ba ajikin shi yake ba murya asanyaye yace "Dr Jabir"
Da murmushi Dr yak'arisa gareshi yana fad'in "Waw masha Allah sannu general"
Yamutsa fuska yayi yana kallon ruwan da d'an kad'an yarage yagama shiga jikin shi yace "what happen to me Dr menake anan?" Yayi maganar yana k'ok'arin tashi zaune,
Dasauri Dr yataimaka mai yajingina shi da gadon yana fad'in "is a long story kabari kasamu lafiya don't street yourself idan kasamu lafiya zakaji komai kaji"
Idanu yalumshe yana cije busashshen lips d'in shi jin yanda gefen cikin shi ke mai zafi ajiyar zuciya yasauke yakwantar da kanshi ajikin katifar kamun yaacee "ina Mata t..." Saikuma yayi shiru yana bud'e idanun akan Dr tuna abunda yafaru dashi yawani zabura yana fad'in.........✍🏼


Don't forged to
Vote,  comments &
Shaare it fisabilillah
Follow me on wattpad
#Babybintuu
On arewabooks
#Babybintuu

WAYE SANADI!? BOOK TWOWhere stories live. Discover now