f p 3♥️

51 6 0
                                    

*fatymasardauna*

*by meeerarh*

🖤*free page 3*🖤

A lokacin da Fatou tacika shekaru sha biyar, soyayyar ta da Amjad babu Wanda bai sani ba.

Saboda irin kula da affection da ke tsakanin su, aduk inda dayansu ya zauna tabbas sai anyi maganar dayan.

Sosai maman Fatou tayi farin ciki da wannan abun , saboda tasan yanda Amjad yake da tsananin kyawun hali, a lokacin taso fa'da wa Abey.

Amma ganin cewa Fatou yarinyace , sai ta bari akan sai ta gama secondary school, a lokacin da take shirin fa'da mishi kuma sai ta ji wannan maganar, ita kuwa ba abun da za tace sai dai godiya ga Allah.

CIGABA.

Sosai Fatou ta koma wani iri sanin da tayi cewa Amjad yabar kasar ya saka ta kara shiga wani hali, saboda gani ta keyi ba zata sake ganin saba har abadan.

Yau kwanaki biyar Kenan da Abey yayi mata wannan maganar, amma har lokacin basu taba yin ko da gaisuwa da Habban ba.

Abunda ya 'daure wa Hamdan da Musty kai Kenan, ganin cewar ha'da su a kayi amma ace ba zaya iya kiranta ba.

Tun da akayi maganar ma bai 'kara zuwa gidan ba, kodai baya sonta ne.

Duk da cewar basu ji da'din ha'din ba , amma haka suka 'karfafa mata guiwa cewar lallai ba zatayi dana sani ba.

Haka rayuwar ta cigaba, ana saura kwana biyu a 'daura aure kasancewar babu wani abu da akayi a bikin, 'yan uwa ma tsirara kawai suka zo kasancewar familyn nasu ba suda wani yawa.

Amjad ya dawo ana gobe 'daurin aure, ko da ya shiga gida gurin Abey yafara zuwa ya gaishe shi sannan ya wuce part din su shida Musty.

Yayi freshen up ya kwanta, karfe 6:30pm ya tashi, ganin cewar har anyi sallan magrib ya sakashi kiran sunan Allah , thinking of abun da ya sameshi har yakai yanzu yana barci shida tun 11 am ya dawo.

Tashi yayi yayi sallolin da suka wuce shi sannan yayi wanka bayan yayi isha'i kuma ya nufi cikin gidan.

Koda ya shiga cikin harabar part din mama, Fatou na kofar palon zaune hannun ta riqe da picture dinsu ita da shi lokacin dayayi proposing dinta.

Dafe daidai sautin zuciyar sa yayi saboda yanda take duka da matsanancin karfi.

Kafin ya dawo ya zaci zai iya jure rashin ta, amma ganin da yayi Mata yasa duk wani karfin guiwa daya ke dashi ya rugurguje.

Itakuwa Fatou jin idon mutum akan ta ya saka ta 'dagowa, yana ganin ta yayi saurin fita daga part din.

Da sauri Fatou ta bishi tana kiran sunanshi,"Habiby , Habibyy please ka tsaya ka saurare ni, koda wannanne zai zama magananmu na karshe , please", ta'karasa inda yake tare da zubewa a gurin.

Shima ganin ta zauna akasa ya sakashi zama yanda zasu fuskanci juna.

Hannuwan sa guda biyu ta riqe a cikin hannayen ta , wani irin yanayi mai matu'kar wuyar fassara wa suka shiga .

Wani irin yawu mai 'daci Amjad ya ha'diye yana jin kaman yadauke ta su gudu.

Amma idan yayi hakan bai yiwa Abey adalci ba, mutumin daya raine shi kaman 'dan cikin sa.

Hannayen sa ya cire tare da miqewa tsaye, har ya juya zai bar gurin ya sake juyo wa tare da fa'din.

"Kitashi ki dauko mayafinki mufita yawon karshe", wani murmushi ne ya kufcewa dukansu a sanda suka tuno irin rayuwar da suka yi.

Da sauri tami'ke tare da fa'din "ka jira ni anan please kar ka kuma tafiya kabar ni", juya wa tayi takoma part din.

Bayan wasu mintuna ta fito sanye da sweatpants da longsleeve tshirt kanta kuwa p cap ne, gaba'daya komai fari tasaka har sneakers 'dinta, tayi kyau sosai duk da ramar datayi .

ℱ𝒶𝓉𝓎𝓂𝒶𝓈𝒶𝓇𝒹𝒶𝓊𝓃𝒶 Where stories live. Discover now