Cike da zallar ɓacin rai yake taka ƙafafuwansa a nan Parlo ya samu Abbu da Ummi da Mami harda Didi wacce bacci ya ɗauke ta a saman carpet bakinta ɗauke da ƙashi tana tsotsa.
Kai tsaye upstairs yay yana wani irin fitinannan taku kamar wani ɗawisu,  kai tsaye bathroom yay tare da  zame jallabiyar jikinsa akan wannan Village girl ɗin yay late a wajan aiki.
Wanka yay ya fito ɗaure da towel kafin yay ɗauki handrayer ya fara gyara sumar kansa, lotion mai ƙamshi ya shafa a saman fatarsa kana ya ɗauki body spray ya fesa, nan da nan sumar kansa ta kwanta luff har wuya jan laɓɓan nan suka ƙara yin yirrrrr dasu.
Wajan closet ɗinsa ya nufa ya ɗauki Sunset Suit Nevy blue ya sanya kana ya ɗura jacket a sama kafin ya sanya white necktie.
Wani half cover shoe ya sanya black kafin ya ɗauki briefcase ɗin sa, wayoyinsa ya ɗauka ya sanya a aljihu gently ya fita daga part ɗin yana tafe yana duba Rolex ɗinsa na Companyn Patek philippe.
Lokacin daya fita bai samu kowa ba sai Didi wacce take bacci kai tsaye fita waje yay dai-dai lokacin da P.a ya shigo bai tsaya amsa gaisuwar P.a yau da kansa ya buɗe ƙofa ya shiga back seat ganin hakan yasa P.a yiwa motar key ya fita da gudu.
Kai tsaye Audi baƙo way suka nufa inda *AKEEM BETTER FARMING INSTITUTE A.B.F.I* Babban waje ne babba  babu mai iya ganin girmansa domin makaranta ce guda ta kuyar da aikin noma, da kuma taimakon mutane, kai tsaye sashin ma'aikata yay tun daga reception aka fara gyarawa ga Hero nan, ga Hero nan hannu kawai yake ɗaga masu har ya isa Elevator yana tsaye kafin ta buɗe ya shiga lift ɗin ya danna 8floor a dai-dai 8floor ɗin ta tsaya ya fito ta office ɗin Md Adnan ya fara shigewa yana wani irin runtse idanunsa sosai.
Kafin ya nufi office ɗinsa wanda aka rubuta Ceo haɗaɗɗan office ne mai kyau da tsari domin hadda ƙaramar cineme da deep frizer ga wasu a.c masu kyau.
Kujera yaja ya zauna a hankali ya buɗe System ya fara aiki.
Ya jima yana dannawa kafin ya ɗauki telephone line ya danna wasu Numbers ɗagawa akai cikin girmamawa akace.
"Mun ɗaga kira daga sashin karɓar ƙorafi Tayaya zamu iya taimakawa maka Dr Abdul-hakeem Bukar Bello Ceo? Lumshe idanunsa yay yana sauke numfashi kamar bazai magana ba sai kuma yace "Uhm Something new?" Cikin nutsuwa matar tace "Yes sir! Mun ƙara samun takardar ƙorafi daga Ƙauyen Wudil  akan matsalar ƙwace masu gona, zuwa yanzu Mutanan sun fara yi masu ta ƙarfi"
Tsayawa yay daga danna keyboard ɗin ɗin tare da sauke hannunsa a fuska yana shafa gemunsa cikin ƙasa da Murya yace.
"Uhm! Su waye ne?" "Binciken da mukai ya tabbatar da cewa wasu Manyan shugabannin ƙasa ne suke sun yin kwacan Wannan gonakin domin su kafa wani company kuma an tabbatar da cewa Wannan company na magani za suyi kuma irin haramtattun Drugs ɗin nan masu kashe mutane, suna son yi a Wudil saboda ruwan dake wajan zai hana aji wari da kuma shaƙar hayaƙin maganin"
Miƙewa yay tsaye ba tare da yace komai ba ya kashe wayar baki ɗaya.
Daga 8floor ya sakko zuwa reception a nan ya samu p.a fita yay daga cikin sashin gaba ɗaya ya nufi ɓangaren koyar da ilimin noman.
Tafiya yay mai ɗan nisa kafin yazo ƙarshen wajan wani ƙaton fili ne a ƙalla za'a iya gida sama da ashirin ga wasu ƙanan kurayen ganye sun fara fitowa alamar shukar ta fara huda.
ga yara a wajan da manya hadda ƴan primary school, cikin nutsuwa ya zare takalman ƙafarsa tare da naɗe hannun rigarsa cikin gonar ya shiga tare da ɗaukan Adda ya fara yanke ciyawar da tai tsayi ganin hakan yasa gaba ɗaya yaran suka fara yin aikin da yake.

  *_littafi na paid book ne, 500 for vip 300 for nrml grp idan zaki siya dan ki fitar na yafe😂🤷🏾‍♀️_*

Http://wa.me/+2348119237616

A can gida kuwa Didi ce ta fito daga cikin gidan zuwan compound da sauri Bala driver ya ƙarasu tana ganinsa tace "Bala maza buɗe min mota" buɗe bayan motar yayta shiga kafin ya tayar da motar gatekeeper ya buɗe masu da sauri suka fita suna fita motar Abbu na shigowa.
A hankali Driven sa yay parking ajjiye jaridar daily trust ɗin hannunsa yay ya fito yana gyara zaman babbar rigarsa kai tsaye cikin babban parlo ya shiga da sauri Amani dake zaune ta riga da wando tana shan chocolate da ice cream ta miƙe tana faɗin "Oyoyo Grandfa"
Ɗaukan ta yay yana faɗin "eyee matar mai kama da Hero" Murmushi tai masa kafin yace "how was your school?" Tana sauka jikinsa tace "Allahamdulillah Grandfa" ganin babu kowa a Parlo ya san kuma su Aleema basu dawo ba kai tsaye ya nufi part ɗin yaran nasa yana sakin wani irin Murmushi domin ya azabtu da rashin ganin Akeela sosai.

Didi na cikin motar Bala driver yace "Hajiya Didi ina zan kaiki?" Kyaɓe fuska tayi tace "ofishin hisba" jinjina kai yay babu jimawa suka ƙarasa da sauri har tana ƙoƙarin faɗuwa ta shiga ciki tana shiga wajan mutane uku suka miƙe da sauri tace "A'a yaya..nace yaya haka kamar dai ana yaƙi bana son gantali babu ruwana wajan ogan ku nazo" ɗaya daga cikin su yace "Hajiya gani" wani kallo tai masa tace "Malam ogan ku nace yaya zakai min tsaye kamar sandar rake" wani ne yace "shine ogan" haɓa ta riƙe tace "Muhammadur Rasulullah S.a.w a'a babu ruwana akace hisbar malamai ne anya Wannan ya iya fataha ma, Tuf astagafirullah ai karatu kuma dai azuci yake Malam ƙara na kawo" Kallonta yay sosai kafin yace "ok Hajiya tame" fashewa tayi da kuka tace "Ubangiji dai ya haɗani da gantalallan jika abin yay masa yawa ga sata ga maita"
Cikin nutsuwa Abbu ya tura ƙofar ɗakin tun daga door way ya fara jiyo sautin shassheƙar kukan ta, da sauri ya rufe ƙofar tare da shiga ciki.
Tana zaune tayi wanka sanye take da Black Silk short robe sai wata Halter top data ɗura a sama, ta rufke gashin kan nan nata da ribbon ya sauka har baya sai ƙamshi take, wani irin harbawa zuciyar Abbu tayi kamar wanda ake ja da mayan ƙarfe haka ya nufi inda take ba tare da zato ba Akeela ta jita akan....

Me Abbu yake nufi ne😂😂 na kusa gama free pages tabbas daɗi na neman yi maku yawa.

*TSINTACCIYA*
NRML GRP ₦300
VIP: 500 SAFE YAMMA POSTING
0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616

*NOTE*
NRML GRP POSTING BA KULLUM BA🤷🏾‍♀️ IDAN ZAKI SAI BOOK ƊINA DOMIN KI FITAR NA YAFE NA FAƊA MAKU ZALLAR SOYAYYA NE A WANNAN BOOK ƊIN MAI TSAYAWA A ZUCIYA.

*FITATTU HUƊU🔥*

BAƘAR FATA
AutaR ManyA

DATTIJON ARZIƘI
Real ladingo

SULTAAN
Mss flower

gaba ɗaya ₦800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 zaku tura Evedance of payment a nan 08142105218

  *SARAUTAR MARUBUTA*

TSINTACCIYAWhere stories live. Discover now