9-10

14 1 0
                                    

*SAUYIN ZUCIYA.*
*Littafin kuɗi ne!*

*Ƴar mutan zazzau Naanah M Sha'aban✍🏽*

*SHAFIN ƘARSHE NA KYAUTA🥰💋HANZARTA KI MALLAKI NAKI DAN KADA KI BARI A BAKI LABARI! YAU BAN YI EDITING BA KUMA SABODA ABUBUWA SUN MIN YAWA, AYI MIN AFUWA🙏🏽*

_LAST FREE PAGE_
*EPISODE 9 -10*

*Whatsapp number https://wa.me/+2348122188717*

*Glad, Sad & Fancy life*

Tana shiga turakarta ta tarar da Falmata a tsaye tana jiran shigowarta, dan akan idonta komai ya faru, a wani ɓangaren taji daɗi da Bassim yay wa gimbiya Afsheen haka, wani ɓangaren kuma hankalinta a tashe yake dan ta san dole Gimbiya Afsheen ko mai martaba su kashe Bassim, amman ita ba za ta so hakan ya faru dashi ba, ga rashin ƴar uwarsa da yay ga kuma kasheshi, shiyasa ta ɗauki niyyar zata kubutar da Bassim ta kowace hanya, Gimbiya Afsheen bedroom ɗinta ta shiga ko mintina ɗaya batayi ba ta fito hannunta riƙe da zabgegiyar wuƙa, da sauri Falmata ta tari gabanta tace "Allah ya huci zuciyar Gimbiya, bai kamata kiyi haka ba, Bassim ya chanchanci hukunci, amman bata wannan ɓangaren ba, na san kin yarda da ni sosai, to a yau ma ina so ki yarda da ni domin mu shirya yadda zamuyi maganin Bassim na rantse miki sai yazo da kanshi ya sunkuya a gabanki yana neman gafararki a gaban bayin masarautar nan, a wannan lokacin kema zaki takashi yadda kike so" Cikin fushi Gimbiya Afsheen tace "kina nufi na dakata daga kasheshi bayan ya gama wulaƙantani a gaban kowa, yau mutumin nan ya saka girman izzata raguwa a gaban bayina, kuma duk saboda shi ne Mamy yau ta saka hannu ta mareni, Sultana Maimuna take gaya min maganganun da ta ga dama, to Falmata bari ki ji idan kin ga ban kasheshi ba to tabbas kafin na ƙarasa gurinshi na mutu" Falmata tace "kenan duk kin manta ƙudurinki akansa, Gimbiya koda kin kashe Bassim zuciyarki ba za ta taɓa yi miki dai-dai ba, zata cigaba da yi miki zafi kuma duk sanda kika tuno maganganun da yay miki a gaban dubban jama'ar gidan nan, to fa za ki ji wani sabon baƙin ciki, dan haka babu zancen kisa dole sai mun shirya masa abin da sai ya yayi nadamar faɗa miki baƙaƙen maganganun da yay miki yau, ita kuma Sultana Maimuna karki bi ye mata ki ce zaki hukuntata, ki barta dan idan kikayi yunƙurin hukuntata to fa zaku iya samun matsala da Sarauniya" Gimbiya Afsheen ta saki wuƙar hannunta ta faɗi ƙasa, ita kuma ta zube akan kujera tana kuka mai cike da baƙin ciki, yau anyi mata abin da har duniya ta naɗe ba za ta taɓa mantawa dashi ba, zuciyarta sai zafi take yi mata, Falmata ta durƙusa a kusa da ita tare da cewa " kuka bai kamace ki ba Gimbiyata, ya kamata ki sakawa zuciyarki dakiya da kuma rashin karayar zuci, domin ki zama jajirtatciya, ba'a komai ake yin kuka ba Gimbiyata, Allah ya huci zuciyar Gimbiya ƴar sarki jikar sarki" Gimbiya Afsheen ta ɗago bayan ta share hawayen fuskarta "Falmata na yarda da ke sosai, shiyasa ba zan hukunta wannan ƙasƙantatcen mutumin ba tare da Sultana Maimuna, amman dole ki samar min hanyar da zan wulaƙantashi ita kuma na koya mata hankali yadda gobe komai ta ga nayi zata ji tsoron yi min magana" Falmata ta saki murmushin jin daɗi tace "idan wannan ne karki samu matsala uwar gijiyata, kuma"..............harbin da suka ji anyi sau biyu a masarauntar ne yasa Falmata yin shuru, jikinta sai rawa yake dan ta san idan aka yi irin wannan harbin tabbas wani za'a kashe ta hanyar cire masa kai, Gimbiya Afsheen ta miƙe tsaya cike da mamaki tace "wannan harbin da akayi yana nufin ana ƙoƙarin yankewa wani hukuncin kisa, amman meyasa ba'a sanar min zaka kashe wani ba" Falmata cikin sauri tace "Uwar gijiyata ya kamata mu je don mu ga meke shirin faruwa" Gimbiya Afsheen ta jinjina kai tare da fita daga turakarta cikin takunta na isa da ƙasaita, Falmata ta bi bayanta da sauri tana addu'ar Allah yasa dai ba abin da take tunani ba ne zai faru, a tsakiyar masarautar suka tarar da mai martaba zaune akan kujera ga kuma fadawa sun tsaya kusa dashi sun rufeshi, gefe guda ga Mamy,Sultana Maimuna da kuma Gimbiya Abeela suna tsaye suna ta kuka, gaba ɗaya al'ummar cikin masarautar aka tattara a gurin, idon Gimbiya Afsheen ne ya sauka a kan mutumin da aka rufe masa fuska da wani baƙin kyale, bata gane wanene ba saboda fuskarsa a rufe take, kuma an ɗaure ƙafafuwansa da hannayensa, ga wani ƙaton bakin mutum ya tsaya a gabansa ya ɗaga zabgegiyar takobinsa yana shirin fille masa kai, "Dakata!" Gimbiya Afsheen ta dakatar dashi cikin tsawa, mutumin ya sauke takobinsa cikin girmamawa, ƙarasowa Gimbiya Afsheen tayi tana kallon mutumin da fuskarsa tana rufe tace "me nake shirin gani?? Mai martaba yanzu har akwai wanda zaka kashe amman ba za'a zo a sanar dani ba, sai dai na ji ƙarar harbi" Ɗaya daga cikin fadawan ne yace "Allah ya ƙarawa gimbiya Afsheen lafiya da kuma ƙara ƙarfi izza wannan mutumin shine Bassim wanda ya faɗa miki maganganu da basu dace ba a gaban kowa dan haka mai martaba yace a kasheshi a gaban kowa na masarautar" zuciyar Gimbiya Afsheen tayi matuƙar ɓaci lokaci ɗaya yanayin fuskarta ta chanza "buɗe masa fuska" Tayi maganar cikin zafin zuciya, wannan ƙaton mutumin ya buɗe masa fuska, idanuwansu suka haɗu Bassim ya watsa mata wani irin wulaƙantatcen kallo, maganar Falmata ce ta faɗo mata a rai "Falmata kin yi gaskiya ba zan kasheshi cikin sauƙi ba, sai na tabbatar na wulaƙantashi fiye da tunanin kowa, sai ya ɗurƙusa a gabana a gaban kowa tabbas sai nayi haka" Tayi maganar a zuciyarta, a fili tace "ku rabu dashi" Mai martaba ya miƙe cike da mamaki yace "gimbiya Afsheen me kike yi haka ne" Gimbiya Afsheen tayi murmushi wanda ita kaɗai ta barwa kanta sanin na menene tace "Mai martaba karka manta fa gobe za'a baka takaddar kwangilar da zakuyi a Abuja, dan haka ni ina farin ciki ka manta da abin da wannan maƙasƙancin yay yanzu lokacin farin ciki ne, kasanshi matsiyaci koda yana cikin arxiƙi ya jiƙashi sai ya nunawa mutane shi ɗin matsiyaci ne" Mai martaba ya jinjina kai yana murmushi yace "that's my daughter, Allah yay miki albarka" Sai kuma ya kalli wannan ƙaton mutumin yace "Ɗauwarama ka kunce sa" yana gama maganar ya nufi turakarsa fadawa na biye dashi a baya, Gimbiya Afsheen ta koma turakarta Falmata ta bi bayanta zuciyarta cike da farin cikin ba'a kashe Bassim ba, dan bata san meyasa ba tana jinsa sosai tamkar ɗan uwanta, bata son ta ga wani abu ya sameshi, dan haka dole ta dinga nunawa Gimbiya Afsheen bata son Bassim dan ta hakane kawai xata dinga samun damar da zata dinga taimaka masa, bayin gidan kuwa mamakin Gimbiya sukayi tayi ba ma su kaɗai ba, Bassim, Mamy da kuma Sultana Maimuna mamaki kashesu yay, sai a lokacin Mamy ta duba gefenta amman sai ta ga bata ga Gimbiya Abeela ba, "ina Gimbiya Abeela?" Mamy tayi maganar cike da tashin hankali, Sultana Maimuna tace "tun lokacin da za'a buɗewa Bassim fuska ta tafi turakarta da gudu" Mamy tace "to muje turakartata" Mamy ta huce gaba Sultana Maimuna da Jakadiya suna biye da ita a baya, Bassim ya miƙe ya nufi ɗakinsa, zuciyarsa cike da tsanar Gimbiya Afsheen, Falmata da kuma Gimbiya Abeela, a ɓangaren Mamy kuwa suna isa turakar Gimbiya Abeela suka tarar da ita tana zaune tana kuka, da sauri suka ƙarasa suna tambayarta meyafaru da ita, taɓe baki tayi zuciyarta cike da baƙin ciki tace "ina ƙawata ta tafi?? ni ina so naje na ganta, ki kai ni gurinta dan Allah" Sultana Maimuna tace "tashi muje ki ganta" Mamy tace "baki da hankali ne! kin san fa Ifteehal ta mutu ko" Gimbiya Abeela tace "menene mutu?" Tayi maganar tana kallon Mamy "wata dubiya ce idan mutum yaje baya dawowa a chan yake zama" Mamy ta bata amsar tana kallonta tana sakar mata murmushi, "Laaaa! da gaske dan Allah ku kaini ina so sai mu zauna a chan ni da ƙawata" Sultana Maimuna tace "zo nan Gimbiya Abeela zan kai ki gurin ƙawarki" Gimbiya Abeela ta miƙe tare da kama hannun Sultana Maimuna tace "muje to" Sultana Maimuna kalli Mamy tace "Mamy ki kwantar da hankalinki, babu abin da zai faru kuma Gimbiya Abeela ba za ta taɓa fahimtar komai ba, zan kai ta ta ganta mu dawo tare" Mamy tace "ba zan bari ku tafi ku kaɗai ba, mu je tare zan fi samun nutsuwa" Miƙewa Mamy tayi suka nufi asibitin masarautar, koda su ka je aka ce Bassim ya ɗauki Ifteehal ya fita da ita, fitowa sukayi daga asibitin zuciyoyinsu cike da mamakin ina Bassim ya kai Ifteehal,kai tsaye ɗakin Bassim suka nufa, a bakin Sultana Maimuna da Gimbiya Abeela sun riga su Mamy isa ƙofar ɗakin "Assalamu alaikum" Sultana Maimuna tayi sallama har kusan sau uku ba'a amsa mata ba, dan haka ta shiga ɗakin, su Mamy ma suna ƙarasowa suka shiga ɗakin da sallama, farin ciki, murna tare da jin daɗi mara misaltuwa ne ya kamasu ganin Ifteehal da sukayi a zaune tana kuka, babu kowa a ɗakin ita kaɗai ce, da gudu Sultana Maimuna da Gimbiya Abeela suka ƙarasa kusa da ita, an cire bandejin fuskarta an saka wani abu kamar lalle a saka a duka fuskar har ya bushe "ƙawata har kin dawo daga duniyar.....hhmm ya ma" Sai kuma tayi shuru alamar tana tunani, sai ta kalli Ifteehal tare da taɓe fuska tace "na manta, wannan ce tace min kin tafi duniya kuma ni na manta sunanta" Tayi maganar tana nuna Mamy, Ifteehal cike da ƙarfin hali tayi murmushi tace "ƙawata ai ni ba ni na saka kika faɗi ba ko?" Gimbiya Abeela ta gyaɗa mata kai alamar eh, Ifteehal ta cigaba da cewa "amman meyasa baki faɗa mata ba, ni ban faɗar da ke ba??" Gimbiya Abeela tace "nima ban sani ba, muguwa ce ba za mu yi wasan ɓuya da ita ba" Ifteehal tace "eh ba za mu yi da ita ba, ita muguwa ce bata da kirki" Sultana Maimuna tace "amman ni zakuyi da ni ko?? dan nima ina son nayi wasan ɓuya" Ifteehal tace "eh zamuyi dake, ai ke ba muguwa bace" duk maganar da Ifteehal take yi daƙyar take yi kana ganin yadda take kasan ƙarfin hali ne kawai yasa take yi, Mamy ta zauna kusa da Ifteehal tare da riƙo hannunta tace "masoyiyata, na ji daɗi sosai da kika farfaɗo baki mutu ba" Ifteehal tayi murmishin jin daɗi tare da cewa "ke ta daban ce, ba muguwa bace ina sonki sosai sarauniya" Mamy tace "kul! ba sarauniya zaki ce ba, Mamy zaki dinga cewa zan ji daɗi sosai, zaki dinga ce min Mamy??" Ifteehal ta gyaɗa kai da sauri, Gimbiya Abeela tace "nima zan ce miki Mamy" Mamy ta saki murmushin jin daɗi tace "oya ku faɗa a tare naji" Sultana Maimuna, Gimbiya Abeela da kuma Ifteehal suka haɗa baki tare da cewa "Mamy!" Dariya Mamy ta saki sosai, zuciyarta ta cika da farin ciki yau kam ta yarda rana ce ta daban, da farko ta shiga baƙin ciki tare da zafin zuciya amman daga ƙarshe yanxu ta shiga cikin matsanancin farin ciki mara misaltuwa, sun kai kusan mintina talatin suna hira cike da nishaɗi idan ka gansu zakayi tunanin sun daɗe sosai da sanin juna, sun burge Jakadiya sosai, daga ƙarshe suka tashi suka fita kowaccensu ta koma turakarta zuciyarsu fas, a ɓangaren Bassim kuwa yana dawowa daga gurin mai maganin da yaje ƙarbo wasu tsumin da zai sakawa Ifteehal a fuska ko Allah zai sa ta tashi, yana shiga ɗakin ya ga Ifteehal tana kwance tana wasa da hannunta "Ifteena!" ya kira sunanta da ƙarfi cike da murna, Ifteehal tana ganinsa ta tashi da gudu ta ƙarasa kusa dashi tare da rumgumesa "Alhamdulillahi! Allah kai ne abin godiya, Ifteehal ɗita kece ma sha Allah!" Ifteehal ta fashe da kuka tare da cewa "Yaya ba za ka ƙara bari ayi min mugunta ba ko?" Bassim cikin fushi yace "wallahi ba zai bari ba, kowane yazo don ya ɗaukeki to tabbas ni zan yi ajalinsa" Ifteehal tayi murmushi "ai Yayana na san kana da ƙarfi sosai" Dariyar jin daɗi Bassim yay sannan ya kama Ifteehal suka zauna a bakin katifa yana yi mata hira tare da tatsuniyoyi masu ban dariya da nishaɗi.
*INDIAN.*
         _{MUMBAI}_
Wani kyakkyawan saurayi ne, a kwace akan gadon ɗakinsa, kyakkyawa ne sosai na ajin ƙarshe, gaba ɗaya jikinsa anyi masa tatu daga shi sai gajeran wando yake, gashin kansa yayi mugun taruwa kamar na mace yay parking ɗinsa a tsakiyar kansa, sai sheƙi yake kana kallonsa kasan yana shan mugun gyara, wata siriyar sarƙar wuya ce ta gwal a wuyarsa, kunnansa ma ɗankunne ne na gwal a jiki irin ɗan ƙaramin nan, hannunsa riƙe da shisha yana sha a hankali yana busharwa, wata baturiyar yarinya akansa babu komai a jikinta, sai manne masa take yi shi kuma yana sakar mata wani lallausan murmushi wanda kana ganinsa kasan na shu'umanci ne, cikin harshen indian take magana "Sweetheart ka tashi ka ƙara yi min ni ban gaji ba, idan zamu kwana mu wuni ana kaina ba zan taɓa gajiya ba, dan kai ɗin na daban ne, kasan yadda ake tafiyar da mace yadda ya dace" Shima cikin harshen indian yace "ba yanzu ba, ina hutawa ki bari sai zuwa anjima" taɓe fuska tayi alamar maganar da ya faɗa batayi mata daɗi ba, chan kuma sai ta saki wani irin murmushi, tare da fara shafa ko ina na jikinsa a hankali zuciyarta cike da muradin son ya ƙara kusantarta a karo na biyu, tana shafashi yana lumshe ido yana kuma zuƙar shishan, a haka har ta zo kan mararsa da ta zo nan sai ta chanza salon yadda take shafashin, anan take ya rikice tare da yarda shishan ta faɗi ƙasa, gajeran wandon ta shiga zame masa har sai da ta cire masa ya rage shima babu komai a cikinsa, janyota yay tare da fara tsotsar lips ɗinsa kamar ya samu wata alewa, ita kuma tana cigaba da shafashi, haka dai sukayi ta zuba love kunsan fa idan zaki ya kama dila abin ba'a cewa komai, sai da suka kwashe kusan awa ɗaya da rabi suna yin abi guda sannan suka haƙura, Amba ta shirya cikin kayanta na india zata tafi, zama tayi akan cinyarsa tare da kiran sunansa "Ɗalhat!" zuba mata kyawawan idanuwansa yay ba tare da ya amsa ba, Amba ta cigaba da magana cikin harshen india "zan yi kewarka sosai, ka iya soyayya sosai, gaba ɗaya jikinka tamkar zuma yake, indai mutum ya tsotsa dole ya ji zaƙi mai gigita kwakwalwa" ta ƙarasa maganar tare da sumbatar bakinsa sannan ta tashi ta fita daga ɗakin, shi kuwa Ɗalhat bin ta yay da kallo tare da ƙurawa surorin jikinta kallo ganin yadda take kaɗa ko ina yana rawa, har sai da ta fita sannan ya ɗauke idanuwansa daga kanta tare da cizon yatsa, bai so ta tafi ba, dan Amba ta kware sosai wajen nuna soyayya, yana jin daɗinta sosai dan idan yana kusantarta, yana ji kamar yana cikin tekun zuma ce mai tsanani  daɗi bala'i✍🏽.

*ALHAMDULLILAH! A YAU NA KAWO ƘARSHEN FREE PAGES ƊINMU DUK MESON CIGABAN LABARIN ZAI IYA ZAƁAR A CIKIN MATAKAI UKUN NAN WANENE YAFI MIKI SAUƘI DA ZAKI IYA SIYANSA, NORMAL GRP #300, VIP GRP #600 SAI KUMA SPEACIAL GRP 1K*

*KO KAƊAN BAMU YI MA FARKON LABARIN BA BARE MA HAR ACE MUN SHIGA CIKIN LABARIN! GASHI HAR NA GAMA FREE PAGES💃🏽KU HANZARTA BIYAN KUƊINKU, DOMIN KU YI KARATUNKU CIKIN KWANCIYAR HANKALI, KARKI CE BA ZA KI BIYA BA SAI AN FITO DASHI! YA KAMATA KI YI ƘOƘARIN MALLAKAR NAKI HALALINKI ƳAR UWA*

INSHA ALLAHU ZAN DIN GA ƘOƘARIN YI MUKU POSTING  DA WURI DAN INDAI KU KA GA BAN YI BA TO BAN DA CHAJI NE, NA SHIRYA TSAF DOMIN NA NISHAƊANTAR, FAƊAKAR, ILIMANTAR DA KU DA WANNAN ƘAYATATCEN LITTAFIN🥰💕

SAI KU NUNA MIN SOYAYYARKU TA HANYAR SIYAN LITTAFIN, KUMA DAN ALLAH DUK WAƊANDA SUKA SIYI LITTAFIN KARSU FITAR MIN DASHI KU SANI AMANA CE NA BAKU KUMA NI NA YARDA DA KU SOSAI DAN HAKA KARKU SA NA FARA JIN SHAUKU A ZUCIYATA GAME DA YARDAR DA NAYI MUKU, INA GODIYA SOSAI MASOYANA ONE LOVE💕❤️KUMA DAN ALLAH AYI SHARE ƊIN FREE PAGES ƊIN NAN, ZUWA WASU GROUPS ƊIN.

KU TURO KUƊINKU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0017770369 UNITY BANK, AISHA YUSUF MUHAMMAD, SAI KU TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 08122188717

        SHARE IT FISABILILLAHI💕

SAUYIN ZUCIYA.Where stories live. Discover now