Kofar ta bud'e a hankali sannan ta gaishe shi fuskarta dauke da murmushi. "Are you alright? Har yanzu baki yi bacci ba? Jannah fa?". Ba tare da ta sake kallon shi ba tace "Jannah is asleep. Ni kuma assignment nake yi".

Gyad'a kai yayi yace "can I come in? Ina so in ga Jannah" bashi wuri tayi sannan tabi bayan shi. Ganin tayi ya durkusa bakin gadon ya shafa fuskar Jannah. Ji yayi idanun shi na ciccikowa ganin yanda duk suka rame.

Allah sarki duniya! Ace wai babu Al'amin babu Sumayya? Da kyar ya iya shanye kukan shi. A hankali ya sumbaci goshin Jannah. Da yake ita ba me nauyin bacci bane nan ta bud'e idanunta.

" Uncle?" Murmushin karfin halinyayi yace " bumblebee". Hannu ta sakala a wuyarshi tace " where have you been? Tun dazu baka dawo ba". Shafa kanta yayi yace " I'm sorry, princess". Kwantar da ita yayi sannan yayi mata sai da safe. Nan ya wuce Rahama sannan ya fice.

Sai dai yana zuwa bakin dakin yaji wani irin bacin rai a zuciyar shi. Ji yake tamkar akan qaya yake zaune. Vacuum cleaner ya dauko da su tsintsiya. Nan ya fara karkade karkade ya share ko wani lungu da sako na dakin yayi mopping hatta ceiling din sai da ya goge.

Sannan ya chanza bedsheets din da labulayen dakin ya fitar ya kai laundry room. Nan ya dauko incense burner ya saka habbatus sauda ya bad'e dakin dashi. Dan shi duk ya da yaki halin Ya Umar da Aunty Hafsa, bai tana tsanar gidan ba, ballentana kuma ace wai har dakin shi yake ki. Hakan yasa yayi tunanin ko Jinnu ke mishi wasa da hankali.

Ruqiyyah ya kunna a mp3 player din shi. Sannan yayi addu'a yabi lafiyar gado. Sai a sannan ya samu yai bacci. Garin Allah na wayewa bayan ya dawo daga masallaci ya kira Ummah. Sosai tayi mamakin ganin kiran shi da asuba ganin ko wayewa gari bai gama yi ba. Kuma a iya sanninta Abdul baya dawowa daga masallaci har sai rana ya fito.

"In ce dai lafiya, Abdul". Er karamar murmushin yayi sannan yace da ita "Eh. Umma" bayan sun gaisa ne yake sanar da ita sabon al'amarin da ya fuskanta jiya. Nan ta yi ta mishi nasiha tace da ya tsanan ta addu'a kuma ya sa ido sosai a al'amuran gidan, musamman akan su Jannah da Rahma.

"Kuma kada ka sake barin kofar dakin ka a bud'e". " Toh Umma, naji. In sha Allah zan kiyaye, nagode." Da haka ya dauko azkar na shi ya karanto su. Nan yayi shirin office, kitchen ya nufa yana had'a ginger tea dinsa. Nan Hafsa ta same shi. " Je kayi breakfast bari zan had'a maka".

Nan yace da ita "a'a ". Shi abin daure mishi kai yake, wai yaushe suka fara shirin da Hafsa ne har wani take cewa zata had'a mishi tea. Ganin ta nace yasa ya daga mata gira "ki je ki yi abin gaba ki nace  ba na so, ko dai kin da wata manufa ne?"

Cikin sauri da tsoro tace "kaji ka fa Abdul wannan wani irin zance kake yi?" Nan ta fice ta kyale shi zuciyarta na tafasa, dan ko kad'an bata yi tunanin zai dawo gida ba. Ko dai maganin bai yi tasiri bane?

Nan ta doka salati data tuna abin da bokar yace, ta tabbata magungunar da ta barbada, ba'a share su ba har sai sun yi 24 hours. Da wuri ta nufi hanyar dakin shi nan ta tarar da Mairo na mopping corridor din gaba dakin shin.

Nan zufa ya keto mata tana share goshinta ta doka mata tsawa "ke kin share dakin Abdul?". Wani irin kallo Mairo tayi mata tace "a'a yace in bari zai share abun shi idan ya dawo daga office". Hamdalah ta saki ganin cewa ba'a share ba. A tunanin ta har tsubbun zai keta 24 hours ma kafin ya dawo daga office.

Sai dai kash! Aikin gama ya gama, Uncle Abdul ya riga da ya share maganinta tun tsakar dare!. A dining ta tarar da su Rahama suna breakfast. Sulaimi da Asiya ma na zaune a tare da su.

ILLAR MARAICIKde žijí příběhy. Začni objevovat