WATA QADDARAR part 2

157 14 0
                                    

♦️♦️♦️
*WATA QADDARAR*
              ♦️♦️♦️

True life story

*Writing by: Chubaɗo✍️*

_Page: 3 - 4_

📖____ Baiyana irin yanayin da Ameerah ta tsinci kanta a wannan yanayin abune mawuyaci a gareta balle kuma ni me rubutawa,  babban abinda ya ƙara ɗaure mata kai shine abinda taga Ahmad yana gudanarwa a gareta a wannan Rana, shine babban jigo koma ta kirashi mukullin boɗe ƙofar tashin hankali a gareta.

A nitse ya zate lips ɗinsa daga nata tareda zubawa fuskarta lumsassun idanunsa yana binta da wani irin kallo wanda yake ɗauke da wani sirri me wahalar fassarawa ga kowa,  zarazaran gashin idanunta dake lumshe yake kallo waƴanda suka ƙarawa fuskarta kyawu, sosai yaji yarinyar ta ƙara burgeshi musamman yanda ta kasa buɗe idanunta ta kalleshi, wani miskilin murmushi ya saki sannan ya tashi motar sukabar gefan titin zuwa gida.

Lokaci-lokaci yakan juya ya kalleta amma sam taƙi yarda ta buɗe idanunta ballema ta kalleshi, gaba ɗaya ƙirjinta bugawa yakeyi  sabida wani irin  tsoro datakeji a tareda ita, har lokacin  ji take kamar lips ɗin Ahmad yana manne danata, rintse idanunta tayi da ƙarfi tare da son ta kori tunanin abin a Ranta amma kuma ta kasa yin hakan, a haka suka ƙaraso ƙofar babban gidansu dake _JAN BULO SECOND GET_  horn ɗin daya zabga ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin datakeyi, lokaci guda kuma Gabanta ya faɗi data tinada Aunty Jameelah!

Wangale musu ƙofar Get ɗin Malam Garba yayi, sannan Ahmad danna hancin motar zuwa cikin gidan, harabar da aka tanada dan ajiye motoci ya nufa ya perker motar sannan ya juya yana kallonta, murmushi yayi me sauti sannan yace "ke wllh idan baki buɗe idonki kin fitamin a mota ba yanzun nan zan ƙara tsotse wannan bakin naki na rashin kunya.

Da sauri ta buɗe idon batareda ta bari sun haɗa ido ba ta kwashi takardunta dake kan qafarta ta fita a motar sekace wadda za'a kama a yanka sabida tsoro,    tabe baki Ahmad yayi sannna shima ya fito daga motar yana wani ɗaure fuska tambar bashine ya gama tsotsewa ƴar mutane baki ba.

A daidai ƙofar dazata sadaka da asalin cikin gidan sukaci karoda Baba Rakiya wadda take ƙanwa ce ga mahaifiyar Ahmad,  wani ɗan iskan kallo take bin Ameerah dashi wanda yasa har seda Ameerahn taji ta muzanta da irin kallon datake mata  sannan tace "ina yini Umma?

Dayake sunna da suke kiranta dashi kenan.

A wulaƙance ta amsa  wanda hakan yayi daidai da isowar Ahmad ɗin gurin, da wannan damar Ameerah tayi amfani tabar gurin da sauri ta nufi part ɗinsu  harda ɗan gudunta, sabida har ga Allah batason zuwan matar nan gidansu sabida ba alkhairi bane yake kawota,

Gabanta ne ya shiga bugun tara-tara a lokacin da take ƙoƙarin tura ƙofar perlourn, addu'ah kawai takeyi Allah yasa karsu haɗu da Aunty Jameelah , tasani muddin suka haɗu Aunty seta gane abinda ya faru tsakaninta da Ahmad, wanda tasan cewar muddin Auntyn tasan da batun tofa ta gama kaɗewa har ganyenta a hannunta.

Tafi minti 5 a gurin sannan ta murɗa ƙofar bakinta dauke da sallama ta shiga. Takoyi sa'a Babu kowa a perlourn se sadeeq da mujaheed dake wasa, da gudu yaran suka nufota suna mata oyoyo, 

Yaƙe kawai Ameerah takeyiwa yaran a ranta kuma Allah-Allah take tabar paarlourn tun kafin Aunty ta fito Asirinta ya gama tonuwa, da sauri tabi gefan Sadeeek da sauri ta nufi ƙofar ɗakinta,  da hanzari ta fara ƙoƙarin murɗa handile ɗin ƙofar tana ƙoƙarin shiga..

"Kekuma me kika tsayayi har biyar da rabi a makaranta?

Ameerah ta tsinkayi muryar Anty ta daki dodon kunnenta,  A daburce tace Clinic naje Aunty dama kaina ne yaketa min ciwo tunda naje makaranta, kuma ki tambayi ya Ahmad kiji, ta faɗa tana hawaye.

Kallon tsaf Aunty tayi mata tareda son gano wani abu a tareda ita amma kuma bata samu nasaran gano komai ba,  ajiyar zuciya Aunty Jameelah ta saki sannan tace "to Allah ya sawaƙe Ameerah, seki hanzarta kiyi wanka sannan kizo kici abinci kisha magani.

Bata amsa mata ba ta faɗa ɗakin tareda murza keyn dake jikin ƙofar ta faɗa kan mamadaidai cin gadonta tana sauke ajiyar zuciya, tsaki ta ɗanja kaɗan sannan tace "to meye ma'anar abinda ya Ahmad ya aikata a gareni?

Ganin kawai tana ɓatawa kanta lokacin kawai babu me amsa mata tambayar ne yasa ta miƙe ta fara rage kayan dake jikinta sannan ta faɗa toilet don ta watsa ruwa kota ji daɗin jikinta.

*ASALINSU*
A tsakanin Ahmad da Ameerah a kwai danganta me ƙarfin  gaske wadda take alaƙa ce ta jini a tsakanin mahaifansu maza,  mahaifin Ahmad Alhaji SUFYAN shine babba, Sannan Alhaji ABDURRAHMAN mahaifin Ameerah,  Asalinsu ƴan jihar katsina ne a cikin ƙaramar hukumar JIƘAMSHI,

Mahaifin Ameerah ya rasu tun tana ƴar shekara ɗaya a duniya, bayan rasuwarsa da shekara uku itama mahaifiyarta Allah ya karɓi abinsa a sanadiyar doguwar jinya datayi fama da ita, iyayensu su hudu suka haifesu, babbansu shine Abubakar se mabiyinsa me suna   Abdullahi, sannan Asma'u se kuma Ameerah wadda ta kasance itace Autan su. Tun bayan rasuwar iyayensu Ruƙon Ameerah ya koma hannun Yaya Abubakar tareda matarsa Aunty jameelah.

Aunty jameelah tanada kirki sosai da kuma tausayi, shiyasa Ameerah take matiƙar jin daɗin zama da ita, sedai tanada faɗa sosai idan aka taɓo ta, sannan kuma bata da kawaici akan dukkan abinda ze kawo mata cikas a tarbiyar yaranta.

A kwai shaƙuwa sosai a tsakanin mahaifin Ameerah da kuma na Ahmad, shiyasa ma suka gina rayuwarsu a muhali guda wato gida ɗaya, dukda cewar ana samun tseko sosai a tsakanin matansu wato iyayensu mata.

Alhaji sufyan yanada mata biyu, yara 8, babbar matar tasa itace hajiya Saude wadda take uwa ga mayan ƴaƴansa, Muhammad Aminullah da kuma   bilkisu, Hashim da kuma Noorudden

hajiya salma matarsa ta biyu kuna tanada yara 3 Sulaiman da sumaiya se kuma Fatima duna kiranta da (momy) sannan Ahmad shine ya kasance auta a garesu, duk a ciki hajiya salmah ce batason zaman lfy sabida rashin haƙurinta shiyasa kullum a faɗa take kamar ta ari baki, wannan shine mafarin jigon gidan,

Yaya muhammad babban yayansu Ahmad matarsa ɗayace Ana kiranta da Aunty hindu, sunada yara 3, khaleed da umar se kuma Aliyu dukansu a gidan suke zaune da iyalansu,

se kuma yaya sulaiman wanda suke ɗaki ɗaya dasu Ahmad shima yanada mata guda ɗaya da kuma yara biyu, Malik da mulaikha. Inda sauran matan kuma duk suke aure a cikin garin na kano.

mafararin ɗaurin dake tsakanin Ahmad da kuma Ameerah shine,  tun Ameerah tana ƴar shekara bakwai ta shaƙu da Ahmad, sabida irin ƙaunar dayake nuna mata, duk inda Ahmad zashi muddin ba nisa zeyi ba yana maƙale da Ameerah,  yasai mata wannan ya sai mata wancan, wannan shine mafarin ƙaunar da Ameerah keyiwa Ahmad ɗin,

Komai nata ya Ahmad Har abin ya fara damun Aunty jameelah, wata Rana Aunty jameelah tanayi mata wanka tace " oh Ameerah na Allah yasa inga aurenki, da sauri Ameerah tace "aini yaya Ahmad ne mijina kuma abokina.

mirmushi Aunty jameelah kawai tayi tana mamakin shirme irinna Ameeran,

bayan wani lokaci, Ameerah ne tsaye a jikin ƙofar ɗakin Ahmad se faman sosa ido takeyi, murɗa ƙofar tayi ta shiga tareda sallama, a zaune ta sameshi saman katifanshi yana nazarin wasu littattafansa na makaranta,

Tana shigowa ya dakata da abinda yakeyi ya zuba mata ido yana tambayarta damuwarta,

Turo baki tayi cikeda ƙuruciya tace "to ai inaso na gayama wani abune,  murmushi yayi me kyau sannan yace "ok to zo ki faɗa min ƙanwa ta, matsawa tayi gareshi sannan yace " ya Ahmad nikam ina sonka wllh, kuma na faɗama Aunty da Abban sadeek kai kaɗai zan Aura ni kaɗai.   Ta qare maganar tana washe ƙananun haƙoranta tana dariya  cikeda wauta gamida ƙuruciya me tarin yawa.

sandarewa Ahmad yayi yana kallonta cikeda mamakin kalamanta.



Comment
Nd
Share




Sushmah💋

WATA QADDARARWhere stories live. Discover now