don haka daga goɓe dokar ta ɓaci zata fara aiki akansu, don haka duk wanda kuka kama a waje ko babba ko yaro ko mace ko namiji muddin ya saɓa wannan dokar ta hana zirga-zirga ku hukuntashi idan ta kamama ku kulleshi har tsahon kwana guda Tareda horo me tsanani.

Cikeda girmamawa suka amsa da yess sir tareda sara masa, sannan suka fara tafiya cikin wani irin salo gwanin birgewa gamida ɗaukar hankalin duk wani me kishin ƙasarmu ta haihuwa wato Nigeria.

*_BAYERO UNIVERSITY KANO (B.U.K)_* A nitse take takawa cikin salon tafiyarta me cike da nutsuwa gamida ɗaukar hankali, kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci a matiƙar gajiye take, sanye take cikin wata doguwar jallabiya baƙa ta naɗe kanta da mayafin rigar (Roling) wanda ya sauka sosai ya rufe Mata ƙirjinta, A nitse ta samu guri ta zauna a ƙasan wata bishiya bisa Kan wata kujera wadda aka sarrafa da farin dutse don zaman duk wani ɗalubin dake makarantar, wanda yake opposite ɗin Department ɗin Education, A nitse ta zube takardun dake hannunta da wayoyinta a gefe tana yarfe hannu alamar gajiya, se'a lokacin nasamu nasarar ƙare mata kallo, doguwace meɗan matsakaicin tsayi, tanada doguwar fuska gamida dogon hanci tareda siraran laɓɓa, idanunta a zagaye suke waƴanda sukai daidai da halittar tsarin Fuskarta, sam bata kasance a cikin jerin mata masu hasken fata ba, sedai tanada gogewar fata, ma'ana dai irin matannan ne waƴanda akewa laƙabi da black beauty, *_AMEERAH ABDURRAHMAN JIƘAMSHI_* kenan, Yarinya mayshiya mejida gayu gamida ƙwalisa, tunda ta zauna take ta faman aikin kallon wayarta tana turo baki gamida yatsine fuska, da alama a kwai kiran datake tsammanin shigowar sa amma shiru babu alamar Shigowar kiran,

hakanne yasa ta Ƙara cika tai fam kamar zata fashe sabida takaici, Wata baƙar motace ƙirar Benz ta sulalo harabar Faculty of Education ɗin baƙa wuluk da ita taji Uban tinted.

wani farin matashi ne ya fito daga motar Fari sol dashi wanke hannu ka taɓa, daga Kallon yanayin zubin Halittar Fuskarsa yafi kamada larabawan yankin Qasar misrah, Kokuma A kirashi da ruwa biyu. A takaice dai sak mijin novel 😂

fuskarsa sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda gizna skey blue ta alfarma, wadda ta ƙara baiyana kwarjininsa da kuma haibarsa, ƙafarsa a saƙale take cikin wani Black ɗin takalmi ƙirar Companyn Batozy se faman baza ƙamshi yakeyi, Direct inda take zaune ya nufa fuskarsa babu yabo ba fallasa harya isa inda take, tun kafin ya iso ƙamshin turarensa na (mukhallat ) ya ziyarci hancinta, A hanzarce ta kwashi books ɗinta da phone ɗinta ta nufeshi kamar zatayi kuka a haka ta cimmasa, dariyace taso ta kamashi amma kuma seya gimtse sabida gudin Raini ya wani haɗe rai.

narai-narai tayi da ido zatamai kuka ya wani galla mata uwar harara yace "wazakima kuka a nan eh?

Haɗiye kukan tayi tareda nufar motar ta buɗe ta shiga se faman zumɓura baki take kamar zata fashe, sabuda takaicin ɓata mata lokacin dayayi, a haka ya shiga motar ya murza mata key suka bar harabar gurin, a nitse yake tuka motar cikeda ƙwarewa da bajinta bakajin sautin komai sena mutuniyarsa silindion a cikin waƙarta me taken (i love you).

satar kallon fuskarta yayi tareda sakin wani irin tattausan murmushi yace" dama kin saki ranki dayafi miki Alkhairi, U know that I'm not your Driver dazan bar uzirina nazo wani ɗaukan ki a school, so I have the right dazan shanyaki yanda naga dama tunda motana ne bana wani ba, harda wani tara ƙwallan gulma da kinibibu duk kinbi kinsa an matsamin Sena dinga zuwa ɗaukanki ai seki shiryama abinda yafi hakan don wllh kaɗan ma kika fara gani Yarinya. ya faɗa yana wani irin cixon lips ɗinsa na ƙasa.

Kwallan datake dannewa ne yasamu nasaran zubo mata sabida takaicin kalamansa, wani irin bugu ƙirjinta yakeyi tamkar zuciyarta zata faso ƙirjinta ta fito, cikeda tsiwa ta kalleshi tace "stop this car ya Ahmad! Nace ka tsayar da motar na fita na barma motan ka! Wai shin meye laifina dazan dinga fuskanta irin wannan cin kashin daga gareka?

"don kawai ribatar ƙuruciya yasa na furta maka kalmarso shikenan se in zama wawuya kuma mara galihu a idanunka? To indai wannna ce taƙamarka kasa Ranka cewar na dade da dena sonka Yaya Ahmad!!!!!! Ameerah ta faɗa cikin wani irin karaji kamar zta shiɗe sabida kukan dayaci ƙarfinta.

Wani miskilin murmushi Ahmad ya saki wanda iyaka cinsa lips ɗinsa, sannan ya paker motar A gefan titi tareda zuba mata Tsimammun idanunsa batareda ya iya firta koda kalma ɗaya daga bakinsa ba sabida takaicin kalamanta, haka kuma bakajin sautin komai sena shashsheƙar kukan ta, A ranta kuma tana mamakin jidakai irinna *_AHMAD SUFYAN JIƘAMSHI,_* se'a yanzu takejin haushin kanta tareda ganin tsantsar wautar Akan abinda ta aikata a Shekarun ƙuruciyarta, shin meyasa ma ta firtawa Ahmad kalmar so ne?

"yanzu ai gashi nan yanayi miki cin kashi irin nasu na maza masu jinda kansu, tareda Jin alfaharin Cewar kince kina sonshi, wani ɓangare na zuciyarta ya gaya mata hakan, to am...... "Ke ni kike gayama wannan maganar don na gaya miki gaskiya?

A tsiwace ta kalleshi idanunta duk sun caɓe da hawaye tace " Aeɗin na faɗa ɗin, idan har taƙamar ka kenan a kan *_AMEERAH ABDURRAHMAN JIƘAMSHI_* to ka tabka babban kuskure Ya Ahmad! Domin kuwa salon ya daɗe da canzawa tun a lokacin da na kammala karatun Secondary school ɗina na dena son.......... Da wani irin mugun zafin nama Ahmad ya fizgota ta faɗo jikinsa, lokaci guda kuma ya haɗe bakinsa da nata guri ɗaya batareda tunanin komaiba ya fara kissing ɗinta gently cikin wani irin salo me baiyana Tsantsar shauƙinsa a gareta.

sandarewa Ameerah tayi lokaci guda Numfashinta ya tsaya cak, wani irin bugawa Ƙijinta keyi da wani irin ƙarfi tamkar zuciyarta zata tsaga ƙirjinta ta fito sabida tsanannin tsoro da fargabar irin halin data tsinci kanta a ciki A wannan rana, wasu siraran hawayene suka Shiha bin kuncinta wanda ita kanta batasan na menene ba.

Wai shin menene ma'anar hakan?

Domin jin irin sarqaqiyar dake cikin wannan littafi me taken WATA QADDARAR!! seku biyoni donjin yanda akalar labarin zata cigaba da ja😁



Wannan kenan✍️

*Kaɗan daga cikin LIttafin Wata Qaddarar*

DON'T FORGET TO VOTE
AND COMMENTS

Chubaɗo

WATA QADDARARWhere stories live. Discover now