Page 4

174 7 0
                                    

🌹Namijin Bahaushiya 🌹
 
By NucyAdam
  

Wannan litattafin mallakatane kuma hakkinane ban yarda wani ko wata ya canjamun maanar littafina ba.,,,

Episode4

Iyayen mukhtar sunje gidansu zahra antsaida maganar aurensu bayan bincike da duk wani abu na al'ada malam bahaushe da addinin, antsaida ranar aure wata 4 daidai zahra ta zana final exam dinta, tabangaren safiyya kuwa tana ta zabgowa mukhtar kira a waya da sakonnin messages ba adadi sam baibi takanta kamar yadda bai karanta sakonninta. Mukarram kuwa yana hannun hajiyarsa..
  
     Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya yau take ranar daurin auren mukhtar muhammad bawa da amaryar sa zahra Adam, daurin aure yatara jamaa manya da kanana kowwa ya shaida wannan aure mutane suna ta saka albarka karfe 7pm daidai yan uwa da abokan arziki suka kai zahra gidan ta dake anguwar sarki, sosai iyayen ta sukayi kokari ankawata ko ina, dan tun bayan da mukhtar yasaki safiyya ya saka mota aka kwashe mata kayanta tas ya aika mata su gidansu, dan haka kayan zahra sun samu guri sun bararraje sunyi kyau matuka sun kawata dakin zuwa 8 kowwa ya watse anbar zahra amarya da kawayenta zainab dakuma aina'u , karfe 8:30 ango mukhtar yashigo tare abokinsa kamal sosai angon yayi kyau kaikace aurensane na farko sai kyallin goshi yakeyi  , bayan angama siyan baki aka bama kawayen amarya kyautarsu kamal ya kwashesu a motarsq yamaida kowacce zuwa gidan iyayenta.. Bayan kawayen amarya sun wuce mukhtar yadawo daga rakiyarsu dayayi kofar gida nan ya kulle ko ina yakarasa dakin amarsa sosai gaban zahra ke lugude dan kawayenta sun tsoratata kwarai akan daren farko, Bayan sunyi alawala sun gabatar da sallolinsu mukhtar ya janyo musu kaxa tadanci kaxar dayake wunin ranar batasaka komai abakinta ba, takora da madara mai sanyi. Bayan sun gama suka kuskure baki nan yaga zahra nakokarin kwanciya da kayan dasuke jikinta duk da kawayenta kamun su tafi saida suka fito mata da sleeping wears din daxata saka amma fargaba bata barta ta saka. Haba my luv amma bada kayan nan xaki kwanta ba ko nandai ya lallabata tasaka kayan baccinta yakashe musu wuta yajawota jikinsa daganan ban kara ganin meye faruwa dayake duhu ya lullube ko ina 🥺
    

                 ........................
Yau monday kwana 8 kenan da bukin zahra da mukhtar amarya da ango anata dirzar soyayya, tun bayan asbah da zahra tatashi tahada masa breakfast fried yam ta soya sai egg spice da tayi masa tahada masa tea mai kauri tashirya masa a dinning bayan yafito sun karya tarataya jakan laptop dinsa tarakashi bakin mota ya wuce tadawo cikin gidan bayan ta gyara ko ina tsaftsaf ta kuma yin wanka sannan tasamu ta koma bacci. Karfe uku zahra nagani tanata kaikawo acikin kitchen dan yau tuwo takeso ta mullukawa gogan nata.. karfe 8 yashigo gidan yasamu zahra tayi kwalliyarta daidai gwargwado cikin riga da sket na ciganvy tayi kyau masha Allah taataso ta amshi jakar hannunsa tanata kasa kunne taji yayabi zazzafar kwalliyar tata tadaiji shuru ta kai jakar tashi daki tadawo ta kawo masa ruwa..

Namijin Bahaushiya Where stories live. Discover now