Part title

225 4 1
                                    

🌹Namijin bahaushiya 🌹

         By NucyAdam

   Episode 2
  Karfe 8pm daidai mukhtar yashigo gdn sa matsakaicin gidane mai dauke da babban falo dauke da 3 bedroom kowanne bedroom akwai toilet, akwai yalwatacciyar barander daxata sadaka da kofar falon, matsakaicin parking space da xai dauki at least motoci guda uku gefe kuma akwai karamun daki wanda aka tanaadeshi dan maigadi duk da dai babu mai gadi a gdn. Parking motarsq yayi sannan yafito yaje ya rufe get din, kofar mai zaman banxa na motar tasa ya bude yadauki jakarsa ta office yanufi hanyar da xata sadashi zuwa cikin falon nasu. Da sallama yashiga falon mukarram kadai yasamu a falon yana kallon cartoon da gudu irin na yara yataso yana abbu oyoyo yanayi yana leka dayan hannun baban nashi abbu mekasiyomun? Yaron ya tambaya da maganarsa irin tayara marasa wayo hannunsa mukhatr ya kama suka xauna kan  kujera, bansiyo maka komaiba mukarram bana hanaka wanann dabiar ba?  to abu nadaina mukarram din yafada yana kallon baban nashi yauwa yaron kirki.. bai tambayi safiyya ba haka kuma bai nemetaba dan yasan babu mamaki tana toilet sai yanxu take wanka tabe baki yayi yabi falon da kallo ba laifi andan share saidai kana gani kasan baayi mopping ba danganan dankon tea nan daga gani tun nasafe ne da aka sha yabare kuma baa samu damar gogewaba.  Ajiyar zuciya ya sauke gami da tashi yanufi bedroom dinshi, shima babu laifi angyara gadon da ya kwanta saidai daga gani dakin baisamu shara ba danganan goran ruwan da yasha da safe kamun yafita tana nan inda yabartq, kayan jikinshi yarage dan yanaso ya watsa ruwa ya kwanta dan agajiye yake toilet ya shiga nan ne ranshi ya baci dan shima toilet din yana nan yanda yafita yabarshi daga gani ko tabashi baayiba ballantana a gyra tsaki yaja yashiga toilet din a darare haka yayi wanka yafito danshima bagwanin aikin gida bane ballantana ya gyara kwafa yayi yace to ma dama Aibaa wuyanaa nauyin gyaran yake ba a wuyan matar gidan yake nafita nema tun safe ai kamata yayi nadawo naji ko ina yaka kamshi. Bayan yafito yanaa shiryawa cikin kayan baccinshi safiyya tashigo  sannu da dawowa tayi mishi ya amsa a dakile dan kwata kwata tafita a ranshi. Abban mukarram ga abincin kafa akawo mkaa nan ne ko xaka ci a falo tafada tana dan sosa tsakanin cinyoyinta aa nakoshi yafada yana hawa kangadon alama kwanciya bacci zaiyi haba to shknn tace gamida ficewa daga dakin.. bayan tafita ya janyo wayarsa yashiga kiran number zahra wadda yayi mata saving da my angel saida tayi ringing almost 3 times sannan tadaga lumshe ido yayi lokacin da zazzakar muryarta ta daki dodon kunnensa amincin Allah ya tabbata agareki ya abar kaunata kaima ina maka fatan haka tafada cike da so da kauna hira sukayi Ta 30minutes kafun su kashe, Haka bacci yadauki mukhtar zuciyarsa cike da begen zahrar sa dayake ganin 3 month ma yamai yawa bai kawota gidansa ba..
                 ...............
       Karfe shida da rabi xahra tafarka daga baccin data koma tun bayan sallah asbah, toilet tafada domin tayi wanka dan yau tanada lectures na 8, bakwai da rabi daidai tafito daga dakinta sanye da doguwar riga ta material maroon color  wanda akayiwa dinkin A shape sosai rigar ta amshi chocolate skin dinta, dankwalin rigar ta daura akanta sannan ta yi rolling da vail dinta white colour takalmi marar tudu ne akafarta na kamfanin vinci sai side bag dinta data rataya hannunta dauke da logbook nata.  Cikin sauri tashiga bedroom din mamanta a zaune tasameta gefen gado tana karanta 40 rabbana, kusa da ita ta xauna ina kwana mama, maman ta amsa kinshirya kenan eh mama nama kusa makara, baxaki tsaya ki karya ba?aa mama  idan naje schl nakarya nakusa nayi latti toh shknn maman ta dauka 1k tabata toh adawo lpy agurguje ta amsa tafito ta karata bakin titi keke napep tahau yakara sa da ita schl din tabiyashi tafito tashige cikin schl.

Namijin Bahaushiya Where stories live. Discover now