Part7

232 13 0
                                    

🌹Namijin Bahaushiya 🌹
  
      By NucyAdam
   

Episode 7
Haka rayuwa tayita turawa yau da dadi gobe babu dadi, mukhtar irin mazan nan ne wadanda baayi musu gwaninta sam, gashi da tsurfa da son gwale mutum idan yaga abun wasu yayita kodawa, amma idan akayi masa a gdn sa sam baxai bude baki ya yaba.

    Bayan zahra ta haihu yarinyar ta mace  khadija sunan hajiyan mukhtar ne suna ce mata ( Ashna).. haka xahra tadunga hakuri da mukhtar,, irin Dan shawarar nan ya mata da miji sam mukhtar baiyi da ita bawai dan baya sonta bane aa shi sam soyayya da kulawa da kuma tarairayar mace shine bai iyaba.. ( abunda ya lalata matarsa ta farko kenan safiyya dan itama da tana amarya sosai take kulawa da shi da ma kanta rashin yabawar mukhtar ne yasaka ta watsar da komai. Hakan yana faruwa sosai a auratayyar malam bahaushi,, mace tana iya kokarinta wajan ganin tafarantawa miji shikuma yana ganin komai takeba, abunda yaxamar mata dole ne kawao take yi, eh kwarai abunda yaxamar mataa dolene amma kowacce mace a rayuwa tanason a yaba mata a nuna mata kauna da tausayi da kuma kulawa, idan tayi girki a yaba idan tayi kwalliya a koda ta)
    

                    ...................
Itakam zahra tadauki aniyar baxata watsar ba xatayi kokari ta nunawa mukhtar yadda akeyiwa mace kuma tadauki damarar yin hakan, sannan tna ganin canji sosai daga mukhtar din. Tana kuma fatan hakan ya dore tsakaninsu...
     

    Toh kalubale garemu mata,, dan mijinki baya yaba miki ba ya nufin ki canja ki koma kazama marar kula bane aa damarar gyara miijinki xaki daura, shi namiji kamar karamin yaro ne duk abunda kika koya masa shi xaiyi as long as yana sonki.. mu cigaba da tsaftace muhallinmu,  jikkunanmu da kuma kula da mazajenmu, mutuna kosu basu yaba mana ba muna dumbin lada a wajan Allah.....
    
     Inafatan wannan dan takaitaccen labarin Nawa xai fadakar Yakuma nishadantar daku,.. littafin Namijin namijin bahaushiy kyauta ne ba na kudi ba..
   

       Sadaukar wa ga yan uwana mata 🥰
Taku NucyAdam
09139097669

Namijin Bahaushiya Where stories live. Discover now